Connect with us

Labarai Hausa

An Cafke Dan Shekara 25 Da Ake Zargi Da Taimaka Wa ’Yan Fashi Da Maguna

Published

on

Jami’an rundunar ‘yan sandan Najeriya na jihar Katsina sun sanar da cafke wasu da ake zargin jami’an kiwon lafiya ne na bogi wadanda suka kware wajen kula taimaka wa ‘yan fashi da maguna a cikin dajin Katsina.

Wanda ake zargin mai suna Musa Shamsudin, dan asalin jihar Kogi ne amma yana zaune a karamar hukumar Kankara ta jihar Katsina.

Naija News ta ruwaito da cewa an gabatar da shi ne tare da sauran wadanda ake zargi da aikata laifuka a hedikwatar rundunar a ranar Talata, 25 ga Mayu.

A cewar kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, SP Gambo Isah, ana zargin jami’an likitocin na bogi da ke shiga daji don kula da ‘yan fashin da ke a cikin dajin jihar marasa lafiya da wadanda suka samu raunukan harbin bindiga.

Abubuwan da aka samo a wurinsa sun haɗa da nau’ikan magunguna kamar yadda suke a cikin hoton da ke a kasa:

SP Isah ya ce: “Wani kwararren likita ne, Musa Shamsudin, (dan shekara 25), dan asalin jihar Kogi amma mazaunin Kankara ana zarginsa da shiga daji a koyaushe don kula da marasa lafiya da masu rauni.

”A yayin gudanar da bincike, an gano wasu kwayoyi da yawa a hannunsa. Ana zargin ya ɓace daga Kankara a ranar da wasu bandan fashi suka sace yaran makarantar Kankara sannan daga baya suka sake bayyana. Ana ci gaba da bincike,” inji Isah.