Connect with us

Labarai Hausa

An Kama Wasu Matasa Hudu Da Ake Zargi Da Satar Awaki A Kano

Published

on

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kano ta cafke wasu matasa hudu da ake zargi da satar awaki a unguwar Sani Mainagge da ke jihar.

Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ne ya bayyana zance ga manema labarai a cikin wata sanarwa a ranar Talata, 25 ga watan Mayu.

A cewarsa, ‘yan matasan da ake zargin sun kware a harkar satar dabbobi a yankin.

Rahoton ‘yan sanda kan lamarin na kamar haka: “A ranar 08/05 / 2021 da misalin karfe 1600hrs, an samu labari daga wani Basamariye mai kirki cewa, an ga wasu samarai a cikin Keke NAPEP tare da wasu akuyoyi da ake zargin sata ne.

“Da samun rahoton, nan take tawagar Operation Puff Adder suka garzaya zuwa inda aka sami labarin. Da zarar hangen ‘yan sandan zuwa sai wadanda ake zargin suka tsere,”

“An kama mutum hudu (4) daga cikin wadanda ake zargi, daya Aminu Musa, dan shekara 18, Sani Abdullahi, shekara 18, Huzaifa Jafar, shekara 18 da Rabiu Lukman, shekara 17, duk maza ne, mazaunan Sani Mainagge a jihar Kano.

“Jami’ai sun sami ribato mota mai kafa uku da ke dauke da akuyoyi biyu (2), an riga an yanka akuya daya (1).”

“Ana kan kokarin kamo sauran wadanda suka gudu kamar yadda ake ci gaba da bincike. Wadanda ake zargin za a caji su kotu kan kammala bincike,” sanarwan ‘yan sandan ya bayyana haka.