Connect with us

Labarai Hausa

Dokar Harbi-Daga-Hange Makircin Share Kabilar Ndigbo Ne – Inji ‘Yan Kudu Maso Gabas

Published

on

Shugaban kungiyar na yankin kudu maso gabashin tarayyar (ASETU), Cif Emeka Diwe, ya bayyana rashin amincewa da umarnin ‘harbi-daga-hange’ da Sufeto Janar na ‘yan sanda ya ba da kwanan nan a matsayin wani shiri na shafe ‘yan kabilar Igbos daga doron kasar.

Diwe ya ce umarnin, tun lokacin da aka fitar da shi, ya fara aiki ne kawai a yankin Kudu maso Gabas inda aka kashe daruruwa a cikin mako guda.

Naija News ta fahimci cewa Diwe ya yi wannan magana ne a Owerri, babban birnin jihar Imo, yayin zantawa da manema labarai.

A cewarsa, “wannan umarnin sanarwa ce ta kisan sharar da ‘yan kabilar Igbo. Idan ka kalli abin da ke faruwa a Kudu maso Gabas da kuma yadda makiyaya ke yanka manomanmu a kullum, to za ka san abin da nake fada.

“Shirye-shiryen su shi ne su ci gaba da kashe matasan mu ta yadda ba za a sake samun wanda zai sake fuskantar su ba. Saboda sun yi imani kasar ita ce gadonsu.”

Dan gwagwarmayar nan dan asalin jihar Imo ya la’anci shugabannin kudu maso gabas da yin shiru game da abubuwan da ke faruwa a kasar.

Ya bayyana kudurin da shugabannin kudu maso gabas da kudu maso kudu suka dauka a kwanan nan, na kiran a hade yankin a cikin harkokin siyasa, a matsayin matakin da ya jinkirta.

Ya ci gaba da danganta karuwar rashin tsaro a yankin na Kudu maso Gabas da mayar da yankin saniyar ware, yana mai yin kira har ga tabbacin daidaita albarkatun kasa da shugabanci a tarayyar Najeriya.