Connect with us

Labarai Hausa

Duk Abin Da Ya Faru A Libya Ya Shafi Najeriya – Inji Buhari

Published

on

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari, ya ayyana da cewa duk abubuwan da ke faruwa a Libya na da tasiri ga Najeriya da sauran kasashen da ke yankin Tafkin Chadi.

Kamfanin dilancin labarai ta Naija News ta ruwaito da cewa Buhari ya fadi hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin Mohammed Younis Menfi, Shugaban Majalisar Shugaban kasar Libya, a ranar Laraba.

Buhari ya lura cewa Jamhuriyyar Chadi da Nijar suna da kan iyaka da Libya. A cewar sa: “Duk abin da ya shafe su ya shafe mu. Kwanciyar hankali ko rashin kwanciyar hankali na Libya zai shafe mu kai tsaye,”

Buhari ya ce tsaron Najeriya shi ne babban abin da ya sa a gaba, yana mai cewa “sai dai idan wata kasa ko wata hukuma ta samu tsaro, babu yadda za a yi ka iya sarrafa ta yadda ya dace.”

Ya nuna godiya ga Menfi saboda halartar da yayi a babban Taron Kogin Chadi da aka gudanar a Abuja ranar Talata.

Menfi, a cikin jawabin nasa, ya bayyana cewa Libya tana ci gaba cikin sauri tare da gwamnati mai aiki.

Shugaban ya ce, “Muna korar sojojin haya, da kuma dunkulewar umarnin”.

Menfi ya bayyana cewa za a gudanar da zaben dimokiradiyya a lokacin da ya dace, kuma ya ba da tabbacin ci gaba da dangantaka tsakanin kasarsa da Najeriya.

Ya kara da cewa “Muna fatan hadin gwiwa, da kuma sake kulla yarjejeniyoyin da aka yi a baya.”