Connect with us

Labaran Siyasa

Kaduna: El-Rufai Ya Kori Ma’aikatan Siyasa 19 A Gwamnatinsa

Published

on

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, a ranar Laraba, ya kori ma’aikatan gwamnati goma da ke aiki karkashin shugabanshi sa.

Gwamnatin karkashin jagorancin El-Rufai ta bayyana cewa ci gaban shi ne kashin farko na korar wadanda aka nada wa mukaman siyasa.

Naija News ta ruwaito da cewa ‘yan Nijeriya da dama sun ƙararrawa Gwamnatin Kaduna da korar dubun dubatan ma’aikatan gwamnati a karkashinsa.

Gwamnatin jihar a yayin kare manufofinta, ta fada da cewa ba za ta ci gaba da biyan sama da kashi 80 na kudin da ake baiwa jihar daga asusun tarayya ba ga ma’aikatan gwamnati. Ta kara da cewa ma’aikatan siyasa har ila yau zasu ji jiki kwarai da hakan.

Daga cikin wadanda aka kora daga aiki sun hada da Mataimakin Shugaban Ma’aikata da mashawarta na musamman guda biyu.

Gwamna El-Rufai a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter ya jinjinawa jami’an da suka gudanar da ayuka a jihar tare da yi musu fatan alheri a ayyukan da suka sa gaba.

A cewar sanarwar, wadanda abin ya shafa har da Bala Yunusa Mohammed, Mataimakin Shugaban Ma’aikata (DCOSL); Halima Musa Nagogo, mataimakiya ta musamman ga DCOSL da Umar Abubakar, wani mataimaki na musamman ga DCOSL.

Sanarwar ta ci gaba da cewa Ben Kure, mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa; Mustapha Lynda Nyusha da Jamilu Gwarzala Dan Mutum, mataimaka na musamman ga mai ba da shawara na musamman kan harkokin siyasa su ma za su fice daga aikin, ciki har da Umar Haruna, wani Mataimaki na Musamman kan Harkokin Siyasa.

Jerin wadanda abin ya shafa har da mai ba da shawara na musamman kan harkokin cigaban al’umma Zainab Shehu; Mataimaki na musamman ga mai ba da shawara na musamman, Stephen Hezron da Mohammed Bello Shuaibu, babban mataimaki na musamman kan harkokin masu ruwa da tsaki, da kuma babban mataimaki na musamman kan matasa, Aliyu Haruna.

Har ila yau, a cikin jerin akwai Halima Idris, Mataimaki na Musamman kan Fasahar kere-kere; Engr Aliyu Alhaji Salihu, Darakta Janar na Hukumar Sayen Kayan Gwamnati, Mataimaki na Musamman kan Hulda da Jama’a Ashiru Zuntu da Saida Sa’ad, wani Babban Mataimaki na Musamman.

Mataimakan shirye-shirye na musamman, Elias Yahaya da mataimaki na musamman ga sakataren gwamnatin jihar Kaduna, Tasiu Suleiman Yakaii suna cikin jerin sunayen.

Mataimaki na musamman kan al’amuran tattalin arziki, Samuel Hadwayah da Ahmed Mohammed Gero, babban mataimaki na musamman kan muhalli suma an kore su.