Connect with us

Labaran Siyasa

Gwamna Emmanuel Yayi Bayani Kan Zancen Ficewarsa Daga PDP Zuwa APC

Published

on

Gwamnan jihar Akwa Ibom, Udom Emmanuel, ya karyata jita-jitan cewa yana shirin barin jam’iyyar dimokradiyya, watau Peoples Democratic Party zuwa All Progressives Congress, APC.

Naija News ta ruwaito da cewa Gwamna Emmanuel ya bayyana hakan ne yayin da yake maida martani game da rahoton cewa ya shirya sauya sheka daga PDP zuwa jam’iyyar da ke shugabancin kasar, watau APC.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Talata, a cikin wata sanarwa mai taken, ‘Gwamna Udom Emmanuel ya kawar da jita-jitar sauya sheka’.

Sanarwar ta ce, “Kun san dalilin da ya sa suke rubutu cewa zan shiga cikinsu?

“Suna neman mutanen kirki da zasu gyara jam’iyyar su. Suna neman wani ne mai kyakkyawan ayyuka da zasu yaudara tun da basu da ko daya.

“Ku gaya musu ba zan zo ba. Akwa Ibom PDP ce! PDP Akwa Ibom ce!

“Idan ka gansu, ka gaya musu cewa Akwa Ibom ba kamar kowace Jiha ba ce.

“Akwa Ibom PDP ce! Ina ganin kalma ya isa ga mai hankali.

“Ku sani, lokacin da suka zo suka ga kyawawan hanyoyi da Gwamna ya tsarafta, suna neman hanyar da za mu zo mu yi hakan a can.

“Ku gaya musu cewa ba daya bane. Irin shafawar da ake yi a PDP ba za a same ta a kowace Jam’iyya ba.”