Connect with us

Labarai Hausa

Hisbah Ta Kwace Kwalaben Giya 8,400 A Kano

Published

on

Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta kwace kwalaben giya 8,400 a kananan hukumomin Dawakin Kudu da Kura.

Naija News ta samu tabbacin hakan ne a wata sanarwa da babban kwamandan hukumar, Dokta Harun Ibn-Sina, ya baiwa manema labarai a ranar Talata, 25 ga watan Mayu.

Ibn-Sina ya gayawa manema labarai da cewa hukumar su ta ci karo da motar ne da ke dauke da kayan maye a kan hanyarta ta zuwa Kano daga Zariya.

“Motar tana zuwa daga Zariya ne zuwa Kano a lokacin da jami’an Hisbah suka kama direban. Hukumar Hisbah ta hana sayar da giya a jihar don guje wa buguwa,” in ji shi.

Dokta Harun Ibn-Sina ya kara da cewa da zarar an kammala bincike, za a gurfanar da wadanda ake zargin a kotu.

Kalli hotunan kwallaben giyar da wanda aka kama da su a kasa: