Connect with us

Labaran Nishadi

Kofin Europa: Chukwueze Na Cikin ‘Yan Wasan Villarreal Da Za Su Kara Da Man Utd

Published

on

Dan wasan kwallon kafa na Najeriya da ke buga wa Villarreal daga gefe, Samuel Chukwueze, yana daga cikin ‘yan wasan da za su kara da Manchester United ranar Laraba.

Naija News ta fahimci cewa Villarreal sun riga sun ƙusa kai zuwa Gdansk, gabanin wasan karshe na Kofin Europa da zasu buga da United a yau, 26 ga watan Mayu.

An bayyana da cewa dan wasan Super Eagles din ya dace da taka rawar gani a wasan.

Chukwueze ya yi jinya a wasansu na biyu na wasan dab da na kusa da karshe da Arsenal. Duk da hakan dai, kungiyar La Liga din ta samu ci gaba da jimillar ci 2-1 ba tare da dan Najeriyar ba.

Chukwueze bai buga wasannin kulob din sa da Celta Vigo da kuma Real Valladolid da Sevilla da kuma Real Madrid ba. Amma dai dan wasan ya zura kwallaye biyar sannan ya taimaka aka zura kwallaye shida a wasanni 39 a duk wasannin da aka yi a kakar 2020-21.

A wata sanarwa, Naija News ta ruwaito da cewa fitaccen dan wasan tsakiya na Real Madrid, Luka Modric ya sanya hannu kan tsawaita kwantiraginsa wanda zai ci gaba da zama a kulob din har zuwa karshen kakar wasa mai zuwa.

An sanar da zancen ne a ranar Talata, 25 ga Mayu.