Connect with us

Labaran Nishadi

Mourinho Na Shirin Yaudarar Hazard Zuwa Roma

Published

on

Ana danganta dan wasan gefe na Real Madrid, Eden Hazard da komawa AS Roma a kasuwar musayar ‘yan wasa mai zuwa.

A cewar wata majiya ta Italia, Leggo, Jose Mourinho yana zawarcin Hazard a yayin da yake shirin sayan ‘yan wasan sa na farko a Roma.

Majiyar ta nuna da cewa Mourinho na shirin sake haduwa da Hazard, bayan da ya kwashe shekaru biyu yana horar da shi a Stamford Bridge, watau a Chelsea.

Naija News ta yi la’akarin cewa shahararran kocin watakila ya samu isashen kudi don sayan ‘yan was a yayin da zai fara horar da kungiyar kwallon kafa ta Roma a kakar wasa mai zuwa.

Ba mamakin tayin £43million zai iya ya jarabtan Real Madrid ta yarda da yarjejeniyar sayar da Hazard.

Dan wasan na kasar Belgium din yana daya daga cikin ‘yan wasan da Real Madrid ta ware don siyar da su a wannan bazarar bayan wani kaka mai ban haushi a LaLiga.

Shugaban Real Madrid, Florentino Perez, a shirye yake ya ba da izinin barin dan wasan gefe na Hazard daga kulob din a yayin da Chelsea ke zawarcinsa.

Hazard da kansa Naija News ta gane yana son barin Real Madrid a wannan bazarar kuma rahotanni na cewa yana neman komawa Chelsea. Kwantiraginsa ta yanzu da Real Madrid za ta kare a 2024.