Connect with us

Labaran Siyasa

PDP Ta Amince Da Sauya Sakatariyar Ta A Edo

Published

on

Shugabannin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ke a mazabar Oredo 2, a karamar hukumar Oredo na jihar Edo sun amince da sauya sakatariyar jam’iyyar tasu, saboda nuna dacewar tafiyar da mulki.

Naija News ta fahimci cewa wannan ya biyo ne bayan nasaba da halin rashin tabbas da jam’iyyar ke ciki yanzu a jihar, inda shugabannin kananan hukumomi da dama suka mamaye hulba da zanga-zangar nuna adawa.

An bayyana hakan ne a sanarwar mai dauke da maki 3 da shugabannin jam’iyyar suka bayar a Ward 2, a cikin karamar hukumar kuma daya daga cikin shugabannin, Mista Victor Enoghama ya karanta a garin Benin, babban birnin jihar.

Sun sanar da cewa za a kafa wani kwamiti da zai binciki sakatariyar Ward 2 da ta dace a cikin makonni hudu bayan jawabin da shugabannin jam’iyyar suka yi a wajen taron wanda aka gudanar a tsohuwar sakatariyar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a gida mai lamba 59 da ke a hanyar filin jirgin sama a garin Benin.

Wani bangare na sanarwar ya karanta cewa: “Mu Shugabanni da mambobin PDP na Ward biyu a karamar hukumar Oredo muna nuna goyon baya ga matsayin Shugaban jam’iyyar, mai girma Godwin Obaseki kan dacewar hadewa da daidaita dukkan mambobin jam’iyyar a dukkan matakan gudanar da jam’iyya da tsarinta. Wannan zai inganta zaman lafiya da hadin kai a cikin jam’iyyar ”.

Shugabannin sun kuma kada kuri’ar amincewa ga gwamnan jihar Godwin Obaseki a matsayin shugaban jam’iyyar a jihar Edo tare da yaba masa kan kyawawan ayyukan sa, samar da kayayyakin more rayuwa da kuma bunkasa rayuwar mutane.