Connect with us

Labaran Nishadi

Seria A: Gennaro Gattuso Ya Samu Sabon Aiki Bayan Korar Sa Daga Napoli

Published

on

Bayan kwanaki biyu da korar sa daga Napoli, Fiorentina ta sanar da nadin Gennaro Gattuso a matsayin sabon kocinta.

Naija News ta ruwaito da cewa Napoli ta kori tsohon tauraron dan kwallon ne bayan wasansa na karshe a ranar Lahadi da ta gabata.

An sanar da tsohon gwarzon dan kwallon duniyar ne da zama sabon kocin Fiorentina a ranar Talata, 25 ga Mayu.

Naija News ta fahimci cewa an sallami Gattuso ne bayan da ya kasa kai kungiyar kwallon Napoli ga gasar cin kofin zakarun Turai a kakar wasa mai zuwa bayan buga wasa 1-1 da Verona.

Su kuma Fiorentina sun kasa sabunta kwantiragin manajan su Giuseppe Iachini.

Gattuso ya hada da kwararru ‘yan wasan Italiya wacce ta dauki Kofin Duniya ta 2006 kuma ya horar da Sion, Palermo, OFI Crete, Pisa da AC Milan.

A wata sanarwa, Naija News ta ruwaito da cewa shahararran dan wasan tsakiyar Liverpool, Georginio Wijnaldum, na shirin komawa Barcelona.

Zancen ya fito ne bayan da aka hangi wakilin dan wasan tsakiya na Netherlands din, Humphry Nijman, a gidan talabijin na Spain, El Chiringuito TV, yana barin ofisoshin Nou Camp a safiyar Talata.