Connect with us

Labarai Hausa

Tubabbun ‘Yan Garkuwa Sun Mikar Da Makamansu A Adamawa

Published

on

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Adamawa, Aliyu Alhaji, a ranar Talata, ya bayyana cewa wasu tubabbun ‘yan garkuwa biyu sun mikar da makamansu ga rundunar ‘yan sanda a jihar.

Alhaji a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Yola ya ce tubabbun masu garkuwar sun mika bututun G3 guda biyu mai lamba 58607 da mai lamba 52007 tare da harsasai biyar masu rai.

Ya kara da cewa rundunar tana ci gaba da bincike kan yadda ‘yan garkuwar suka samu bindigogi da suke amfani da su wajen kai hari, tare da ba mazauna jihar tabbacin tsaron rayuka da dukiyoyi.

Alhaji ya yi kira ga masu satar mutane su tuba kafin a kama su. Ya kara da cewa rundunar ta cafke mutum hamsin da biyu da ake zargi daga watan Maris zuwa 25 ga Mayu.

Ya kara da cewa kayayyakin da aka kwato sun hada da haramtattun bindigogi 20, da alburusai masu rai guda 1,000, harsashi guda biyar, da sauran kayayyaki na kimanin Naira miliyan uku.

“Daga watan Maris zuwa yau, rundunar ta fara kai samame maboyar masu aikata laifi wanda hakan ya kai ga gano da kilogram 50.70 na ciyawar da ake zargin tabar wiwi ce.”

“Sauran sune diazepam, tramadol, maganin roba, da sauran kwayoyi masu kauri wadanda duk sun kai kimanin naira miliyan uku,” in ji shi.