Connect with us

Labarai Hausa

‘Yan Bindiga Sun Kashe Jami’an‘ Yan Sanda Hudu A Enugu

Published

on

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kashe wasu jami’an‘ yan sanda hudu a jihar Enugu.

Naija News ta ruwaito da cewa wani jami’in dan sanda da ya tabbatar da faruwar a ranar Laraba ya lura cewa wannan shine sabon harin da aka kaiwa jami’an tsaro a yankin.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar, Daniel Ndukwe, yayin yada yawu kan batun, ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun mamaye ofishin ‘yan sanda da yammacin ranar Talata.

Ndukwe ya ci gaba da cewa, mutanen da ke dauke da makamai da suka bude wuta a ofishin ‘yan sanda sun kuma cinna wa wani bangare na ginin wuta.

Ya ce, “Hudu daga cikin jami’an, wadanda suka samu munanan raunuka daga harbin bindiga, daga baya an tabbatar da mutuwarsu a asibiti.”

Ndukwe ya kara da cewa wasu daga cikin maharan an harbe su amma sun tsere da raunuka. Ya yi kira ga mazauna yankin da su bai wa ‘yan sanda bayanan da za su kai ga kame mutanen.

Naija News ta kula da cewa wannan na zuwa ne yan sa’o’i kadan bayan wani jami’in dan sanda ya mutu bayan gurnetin da ke a jikinsa daure kan bel ta tarwatse a ranar Talata.

Kakakin rundunar ‘yan sanda na jihar Ebonyi, Loveth Odah, ta shaida wa kamfanin dillacin labarai na AFP cewa “Rundunar ‘yan sanda tana bakin ciki da mutuwar babban sufeton a wannan mummunan lamarin.”