Connect with us

Labarai Hausa

‘Yan Siyasan Najeriya Ke Baiwa ‘Yan Fashi Makamai’ – In ji Seun Kuti – [Kalli Bidiyo]

Published

on

Mawaƙi da kuma ƙarami ɗa ga yaran marigayi fitaccen ɗan wasan Afrobeat, Fela Anikulapo Kuti, Seun Kuti, ya zargi ‘yan siyasar Najeriya da ɗora wa ‘yan fashi baya da kuma samar masu da makamai.

Naija News ta ruwaito da cewa Kuti ya fadi hakan ne a cikin wani faifan bidiyo da ke ta yawo a kafafen sada zumunta.

Mawakin ya bayyana cewa idan ‘yan Najeriya na son kawo karshen ta’addancin, a bukaci duk ‘yan siyasan kasar da su rubuta jerin sunayen mutanen da suka baiwa bindigogi don a iya kwato makaman.

”Yan siyasa sune suke baiwa ‘yan fashi da bindiga makamai a Najeriya. Kada muyi kamar bamu sani ba. Idan muna son kawo karshen wannan ta’addancin, duk ‘yan siyasa ya kamata su rubuta jerin sunayen mutanen da suka baiwa bindiga saboda mu je mu karbo su. Wadannan ‘yan ta’addan siyasa ne.”

Kalli bidiyon a kasa kamar yada aka rabar a layin sada zumunta: