Connect with us

Labaran Nishadi

Jami’ar Kano Ta Damke Dalibai Maza 17 Kan Cin Zarafin Wata Da Ta Sanya Abaya – [Kalli Bidiyo]

Published

on

Shugabancin babban Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Kano (KUST) sun cafke dalibai 17 da suka ci zarafin wata daliba saboda sanya Abaya.

A cikin wata faifain bidiyon wanda tuni ya yadu a yanar gizo, an ga daliban suna jan mayafin dalibar, suna mata sheri da ikirarin ‘mai Abaya’.

Kalli bidiyon a kasa:

https://twitter.com/Suleey7/status/1397156940787113984

Shugaban jami’ar, Farfesa Shehu Alhaji, a cikin wata sanarwa da aka fitar ‘yan sa’o’i da suka gabata, ya ce biyo bayan rahotannin cin mutuncin da gungun daliban maza suka yi, shugabannin makarantar sun dauki matakin gano wasu daga cikinsu daliban.

Wata sanarwa ta ce jami’ar ta kafa wata kwamiti mai karfi karkashin jagorancin DVC ACAD don gano daliban marasa amana da gaskiya da abin ya shafa tare da bayar da shawarar daukar matakin ladabtarwa nan take da za a dauka a kansu ba tare da bata lokaci ba don zama abin koyaswa ga sauran daliban jami’ar.

“Kwamitin zasu gabatar da yammacin yau (Alhamis, 26 ga Mayu) da rahotonsu gadi da shawarwari ga shugabannin jami’ar don ci gaba da ladabtarwa,” in ji wata sanarwa da DSA ta sanya wa hannu ga kwamitin.

“Muna nuna godiya ta musanman ga goyon bayan da ɗaukacin ɗaliban KUST suke bayarwa wajen nuna da’a, nutsuwa da kuma kwarin gwiwa kan gudanarwa a bisa haƙƙin ɗalibar. Zan sanar da ku nan ba da jimawa ba a kan matakin da shugabancin jami’ar ta dauka akan daliban da ake zargi.”

Karata bayanin jami’ar a kasa kamar yada aka fitar a wata sanarwa: