Connect with us

Labarai Hausa

Kada Mu Yaudari Kanmu, Abubuwa Basu Tafiya Daidai A Kasar – Sarkin Musulmi

Published

on

Mai martaba Sarkin Musulmi, Muhammad Sa’ad Abubakar ya ce kada ‘yan Najeriya su yaudari kansu tunda abubuwa ba su tafiya daidai a kasar.

Naija News ta ruwaito da cewa mai martaban ya fadi haka ne yayin da yake jawabi a wajen taron koli na Tsaron Kasa a Abuja. Sultan din ya kuma bayyana cewa sama da shekaru 11 a matsayin mai rike da sarautar gargajiya, ya shiga tattaunawa da yawa kan tsaron kasa na Najeriya.

Ya kara da cewa yanzu lokaci ya yi da shugabannin za su aiwatar da ayyuka maimakon tattaunawa kawai.

Sarkin Musulmi ya ce; “Kada mu yaudari kanmu cewa abubuwa suna daidai, abubuwa ba daidai suke ba a kasar.

“Mun san da hakan kuma mun ga hakan. Ga wasun mu, mun gana da ababe sosai a rayuwar mu.

“Yanzu abubuwa sun lallace kwarai da gaske. Ba wanda bai san cewa Najeriya na cikin wani mummunan yanayi ba, kuma gaskiya ne.

“A cikin watanni daya da rabi da suka gabata, mun yi taruruka uku masu maiko kamar wannan tare da manyan jami’an tsaro da shugabancin kasar nan.

A yau, mun sake dawowa don tattaunawa kan batutuwan da suka shafi tsaron kasa. Ina ganin ya isa wannan tattaunawar, bari mu samar da ci gaba daga tattaunawar.

“Duk lokacin da muke zama a nan don tattaunawa, lokaci mafi yawa na wuce wa musanman ga daukar matakai na hakika saboda mun san matsalolin.”