Connect with us

Labaran Nishadi

Kannywood: Takaitaccen Tarihin Zainab Idris

Published

on

Zainab Idris ‘yar wasan hausa ce, ‘yar rawa da kuma furodusa ce wacce aka haifa a Jos, Jihar Filato.

Naija News ta gane da cewa an haifi shahararriyar ne a ranar 18 ga Maris, 1982 a Filato.

Zainab ita ce ta biyar a cikin iyalin yara goma, ‘yan mata shida hadi da maza hudu.

Bincike ya nuna da cewa Zainab ta yi makarantar firamaren ta ne a RCM Kabo da kuma Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Jos don karatun firamare da sakandare.

Ta kuma ci gaba da karatun ta har ta karbi satifiket a kwas da ta yi a kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kaduna.

Naija News ta ruwaito da cewa Zainab ta nuna sha’awar shiga wasan kwaikwayo a lokacin da take da karancin shekaru. A karshe ta hadu da darakta, Abbas Sadiq wanda ya gabatar da ita ga wasan kwaikwayo.

Zainab ta yi fitar ta na farko ne a wata shiri mai taken ‘Ikama’. Ta bi wannan tare da wani shiri mai birgewa a cikin fim din ‘Kallabi’ inda ta fito tare da Safiya Musa, Hafsat Shehu, Adam A. Zango da sauransu.

Zainab Idris ta kuma shirya finafinai da dama kamar; Albashi, Gwanaye, Gwamnati da sauransu.