Connect with us

Labarai Hausa

Ranar Yara: Ku Koya Wa Yaran Ku Tarbi’a Mai Kyau – Atiku Ya Gayawa Iyaye

Published

on

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar dimokradiyya a zaben 2019, Alhaji Atiku Abubakar, ya shawarci  iyaye da su koyawa ‘ya’yansu tarbi’a mai kyau.

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da aka fitar a yau Alhamis, 27 ga Mayu domin taya yara murnar bikin ranar yara ta bana.

Atiku a sakon da ya wallafa a shafinsa na Twitter ya bukaci shugabannin da su samar da kyakkyawan yanayin koyo ga yara da kuma samar da kayayyakin karatu.

Ya ce, “Na hada kai tare da sauran ‘yan kasa masu kyakkyawar manufa don taya daukacin yaran Najeriya murnar ranar yara. Ya zama wajibi a kanmu a matsayinmu na al’umma mu tabbatar yara sun sami cikakkiyar damar su a rayuwa.

“Ilimi shi ne ginshikin kowace al’umma. Cutar Korona wacce da ta shigo kasar ya farkar da masu gudanarwa da shugabanci a kowace sashe don tabbatar da kari da gudanar da kayayyakin ayuka na taimaka wa rayuwa da samar da kayayyakin dama a cibiyoyin koyo.

“Babban nauyi na a kan shugabanni ne don samar da kyakkyawan yanayi ga kananan yara, kuma dole ne iyaye su cusa kyawawan halaye ga yara tare da cusa musu kyawawan dabi’u.

“Har ilayau, ina taya daukacin yara murnar wannan rana ta tunawa da aka kebe don bikin su. Ina kira gare su da su zama jakadun iyayensu da na kasar su a duk inda suke. Ina kuma yi musu fatan nasara a ayyukan da suka zaba da kuma kokarin da za su yi nan gaba.”