Connect with us

Labaran Nishadi

Ka Canza Ni, Zan Kiyaye Ka’idodinka – Lukaku Jinjina Wa Tsohon Kocin Inter, Conte

Published

on

Dan wasan gaba na Inter Milan, Romelu Lukaku, ya jinjina da nuna ladabi ga Antonio Conte, bayan ficewar manajan daga Nerazzurri a ranar Laraba.

Naija News ta lura da cewa Conte ya kwashe tsawon shekaru biyu yana jan ragamar Inter Milan kuma ya jagoranci kungiyar da daukar Kofin Seria A na farko a cikin shekaru 11 a bana.

Dan shekaru 51 din, wanda ya kawo karshen nasarar da Juventus ta samu sau tara a jere, ya bar Inter Milan ne da yarjejeniya.

Da yake mayar da martani, Lukaku ya ce Conte ya canza shi tun lokacin da ya iso Milan bayan barin sa Manchester United, ya kara da cewa a koyaushe zai kiyaye ka’idojinsa.

Dan wasan na Belgium ya ci kwallaye 64 a wasanni 95 karkashin jagorancin Conte, Naija News ta san da hakan.

Lukaku ya wallafa a shafinsa na Twitter kamar haka: “A cikin shekarar 2014, mun yi magana a karon farko, kuma muna da wata alaka tun daga lokacin,”

“Muna da lokuta da yawa don aiki tare, amma Allah ne kawai ya san dalilin da ya sa hakan ba ta faru ba tun daga baya.”

“Ka zo a lokacin da ya dace kuma ka canza ni a matsayin dan wasa kuma ka kara min karfin gwiwa kuma mafi mahimmanci, mun yi nasara tare!”

“Lashe nasara shi ne kudurin ka a koyaushe kuma ina yi farin ciki da na same ka a matsayin koci na.

“Zan ci gaba da kiyaye ka’idojin ka har zuwa karshen rayuwata (kiyayewa na jiki, na tunani da kuma kokarin samun nasara…). Abin farin ciki ne da yin wasa a karkashin ka!

“Na gode da duk abin da ka yi. Ina bin ka bashi da yawa .. @antonioconte ”