Connect with us

Labaran Siyasa

2023: Najeriya Ba Zata Iya Aiwatar Da Demokradiyya Ta Gaske Ba – Inji Galadima

Published

on

Jigo a jam’iyyar Demokradiyya, watau Peoples Democratic Party (PDP), Buba Galadima, ya bayyana dalilin da yasa Najeriya ba zata iya gudanar da mulkin demokradiyya na gaskiya ba.

Naija News ta ruwaito da cewa a yayin da yake magana a ranar Laraba, a wata muhawara da Premium Times for Investigative Journalism (PTCIJ) ta shirya kan dimokuradiyyar jam’iyya da jam’iyya, Galadima ya ce dole ne a yi garambawul ga tsarin zabe kafin a samu dimokradiyya ta gaskiya a Najeriya.

Dan jam’iyyar PDP din ya yi kira da bukatar a nuna gaskiya a cikin harkokin zabe. Ya yi zargin cewa nade-naden da ake a cikin jam’iyyu wani lokaci ba a yin su da adalci kamar yadda wadanda ke da iko ke sanya ‘yan takara.

Ya lura cewa tasirin ‘jakunkunan kudi’ a zabe ba za a iya aje shi ba, ya kara da la’antar wadanda ke karban kudi a shirin zabe.

Ya ce: “Kamar yadda muka samu kanmu a yau, manyan jam’iyyun siyasa biyu ba su da dimokiradiyyar cikin gida a cikin tsarinsu. Ko dai kana da dangantaka da wani jigo na jam’iyyar ko kuma kuna da aljihu mai zurfi kafin ma ku sami takara.

“Don haka, ta ina za mu sami mafita kan wannan? Mafita ita ce dole ne mu magance matsalar sake fasalin zabe a kasar.

“Idan wadanan jam’iyyun suka gane da cewa ko da sun tilasta wani dan takara a kan mutane, da alama za su fadi a zaben saboda ba za su sami damar rubuta adadi na ‘yan takarar da suke so ba, dole ne za su yi taka-tsantsan da kokarin yin tarnaki a kan ‘yancin mutane su.

“Babu wani wuri a cikin kowane kundin tsarin mulkin jam’iyya da ya ce shugaban wata jam’iyya na iya samun dan takarar da ya fi so. Mutane ne kawai ke da ‘yancin zaɓar waɗanda za su wakilce su takwas daga jam’iyya, sannan mu je babban zaɓe.

“Amma a yanzu, INEC ba ta da aiki; bangaren shari’a ba su da kwari. Ana sanya su ne kawai shirin shiri hatta wadanda ke da iko suna dora dan takarar da suke so.

“Kuna iya ganin cewa abin da bangaren shari’a su ke nema ba gaskiya ba ne, amma za su nemi fasaha ne. Kuma a cikin bin wannan tunanin, ba za a sami dimokiradiyya a Najeriya ba. Sai dai idan mu mutanen Najeriya mun tashi don mu yi garambawul ga hidimar zaɓe, ba mu fara ba, kuma ba za mu iya samun ganin dimokiradiyya ba.”