Connect with us

Labarai Hausa

Rundunar Sojojin Mali Ta Saki Shugaban Kasa Da Firayim Ministan Kasar

Published

on

Rundunar sojojin Mali ta saki shugaban kasa da firaministan kasar.

Naija News ta ruwaito da cewa wani jami’in soja ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis.

An sakin shugabannan ne bayan kwana uku da aka tsare su da kuma kwace musu iko a wani abin da ya zama kamar juyin mulki na biyu a kasar cikin watanni tara.

“An saki shugaban rikon kwarya da firaminista a cikin dare da misalin 1:30 na safe (0130 GMT). Mun kasance masu gaskiya ga kalamarmu,” jami’in ya fada wa kamfanin dillacin labaran Faransa na AFP, wanda ke magana a kan sharadin sakaya sunansa.

Yan uwa sun tabbatar da cewa an saki Shugaba Bah Ndaw da Firayim Minista Moctar Ouane. Mutanen biyu sun koma gidajensu a Bamako babban birnin kasar, wadanda ke kusa da su sun bayyana hakan, duk da cewa yanayin sakin nasu bai fito fili ba.

Naija News ta gane da cewa sakin nasu ya kasance daya daga cikin bukatun kasashen duniya.

Jami’an soja wadanda suka nuna rashin jin dadin yadda gwamnatin kasar ke tafiya ne suka cafke shugabanan a ranar Litini da ta gabata, a wani yanayi da ya haifar da fushin diflomasiyya.

An kulle shugabanan ne biyu a sansanin soja na Kati kimanin kilomita 15 (mil tara) daga Bamako.

Ndaw da Ouane sun kasance suna jagorantar gwamnatin rikon kwarya wacce aka kafa a watan Satumba a karkashin barazanar takunkumin yankin, da nufin ayyana maido da cikakken mulkin farar hula cikin watanni 18.

Assimi Goita, wanda ya jagoranci wata gwamnatin mulkin soja da ta kwace mulki kasa da watanni 10 da suka gabata, ya fada jiya Talata cewa an kwace ikon mutanen biyu.

A ranar Laraba, shugabannin sun yi murabus a gaban masu shiga tsakani da suka ziyarci sansanin soja, Naija News ta ruwaito.