Connect with us

Labarai Hausa

Biafra: ‘Yan Sanda Sun Cafke Manyan Masu Tallafawa IPOB/ESN

Published

on

Wasu mutane da ake zargi suna daukar nauyin kungiyar ‘yan asalin Biafra (IPOB) da kungiyar tsaro ta Gabas (ESN) sun shiga hannun hukumar ‘yan sandan Najeriya.

Naija News ta ruwaito cewa mukaddashin Sufeto-Janar na ‘yan sanda, IGP Alkali Usman Baba ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis yayin da yake magana a taron tattaunawa na Shugaban kasa da Tawagar Shugabannin Sadarwa ta Shugaban kasa suka shirya a fadar shugaban kasa, Abuja.

Usman Baba ya ce ‘yan sanda na duba shigar da wadanda ake zargin masu daukar nauyin IPOB / ESN a hannunsu da kuma wadanda ke wajen kasar.

A cewar shugaban ‘yan sandan, za a gurfanar da wadanda ake zargin a gaban kotu bayan cikakken bincike.

Ya kuma ce ‘yan sanda sun samu nasarori a kan masu neman ballewa daga kasar da wadanda ake zargi da aikata laifi a kudu maso gabashin. Ya kara da cewa wandada ake zargin kotu ba za ta iya gurfanar da su ba a halin yanzu saboda yajin aikin da ma’aikatan shari’a ke yi.

Da yake ci gaba da magana, IGP Baba ya ce an sami sarari ne bayan rusa rundunonin musamman masu yaki da fashi da makami, (SARS). Ya kara da cewa karfin halin ‘yan sanda ya dusashe bayan zanga-zangar #EndSARS da ta girgiza al’ummar kasar.

Mukaddashin IGP din ya ce ‘yan sanda da mata da maza har ila yau ba su iya cike gurbin da rudanin SARS ba, ko da shike ana ci gaba da kokarin horar da su don sabon aikin, inji shi.