Connect with us

Labaran Nishadi

Zidane Ya Tsige Kansa Daga Matsayin Kocin Real Madrid

Published

on

Zinedine Zidane ya tsige kansa daga matsayin kocin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid.

Naija News ta ruwaito da cewa Zidane yayi hakan ne duk da cewa yana da sauran shekara daya a kwantiraginsa.

Ku tuna da cewa Madrid ta kare ne a lamba na biyu a kan teburin La Liga ta bana a yayin da abokan hamayyar su, Atletico Madrid ta lashe kofin gasar.

Majiyar AS ta ruwaito cewa Zidane ya nemi ‘yan kwanaki don yanke shawara kan makomarsa bayan wasan karshe na gasar kakar bana da Villarreal. Bafaranshen a ranar Laraba ya sanar da kulob din cewa hakika niyyarsa ce ta ficewa daga kulob din.

Tsohon dan wasan mai shekaru 48 da haifuwa ya kuma shaida wa ‘yan wasan nasa kudurin sa da yammacin Laraba.

Shugabannin Real Madrid a yanzu suna da isasshen lokaci don nemo wanda ya dace da maye gurbin Zidane kafin lokacin canja wurin bazara.

Massimiliano Allegri, Raul Gonzalez, Joachim Low da Antonio Conte suna cikin manyan shahararrun kocin da ake hange da maye gurbin Zidane a wannan lokaci.

“Yanzu ya kamata mu kwantar da hankula kuma nan da ‘yan kwanaki masu zuwa za mu yi magana a kai,” Zidane ya fada wa manema labarai bayan wasan karshe na Real Madrid na kakar bana.

“Jin kadan da nan, za mu ga abin da zai faru. Ba wai kawai tare da ni ba, amma da duk abin da kungiyar za ta yi a kakar wasa mai zuwa.”