2019: Farmaki ya tashi tsakanin APC da PDP a Runfar Zabe ta Jihar Kano

Farmaki ya tashi a runfar zabe mai lamba 001 da ke a Wad na Chiranci, karamar hukumar Gwale da ke a Jihar Kano a yayin da dan takaran kujerar Gwamna daga Jam’iyyar PDP a Jihar, Abba Yusuf ya hade da Ciyaman na Jam’iyyar APC na Jihar Kano, Abdullahi Abbas.

Naija News Hausa ta gane da cewa ‘yan siyasa biyun sun jefa kuri’ar su ne a runfa daya. Farmakin kuma ta fara ne sakamakon yabo da kirari da mabiya bayan dan takaran jam’iyyar PDP ke yi ga dan takaran su. Da mamba jam’iyyar APC suka gane da hakan, sai suka fara jefe-jefen dutse har farmaki ya tashi tsakanin.

A halin yanzu ba cikakken bayanin yadda abin ta kare. Amma ka kalli bidiyon yanayin a kasa kamar yadda gidan jaridar Daily Trust suka bayar.

 

PDP: ‘Yan ta’adda sun Konne Ofishin Jam’iyyar PDP a Jihar Kano

Mun samu rahoto a Naija News a yau Litinin da cewa wasu ‘yan ta’adda sun kone Ofishin dan takaran Gwamnar Jihar Kano na Jam’iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf.

Sun kone Ofishin ne da ke a lamba na 36, Chiranchi Quarters a karamar hukumar Gwale, a nan Jihar Kano.

‘Yan harin sun kuma lallace wata motar ‘Golf 3’ da ke da lambar NSR 237 AE.

An samu tabbacin konewar Ofishin ne daga bakin kakakin yada yawun dan takaran, Sanusi Bature Dawakin Tofa, kamar yadda ya bayar ga manema labaran Daily Trust.

Tofa ya bayyana da cewa ‘yan harin sun kai kimanin mutane 60 da suka hari Ofishin, a jagorancin Junaidu Abdulhamid, Mataimakin Ciyaman na Jam’iyyar APC na Jihar, Abdullahi Abbas, tare da Habibu Dandayis, magoya bayan ciyaman na Jam’iyyar APC a Jihar.

Dan takaran, Abba Kabir Yusuf ya bukaci hukumomin tsaro da su dauki mataki ta musanman cikin gaggawa don ganin cewa sun kame wadanda suka aikata irin wannan mugun abin.

Mun ruwaito a Naija News da cewa wasu Yan Ta’adda sun fada wa Ofishin dan takaran shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar, dake a garin Akure, ta Jihar Ondo.