Ambaliyar Ruwa ya Tsinke Gidaje Kimanin 2667 a Jihar Neja

Naija News ta samun tabbacin cewa akalla gidaje 2,667, gonaki, hanyoyi, gadoji ne ambaliyar ruwa ta tsinke da su a kananan hukumomi 17 da na jihar Neja.

Tabbacin hakan ya bayyana ne a yayin wata gabatarwa na tattaunawa da Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa na jihar Neja (NSEMA), Alhaji Ahmed Inga yayi a Minna, babban birnin jihar Neja a ranar Alhamis.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Gwamnatin Jihar Neja tayi Ikirarin cewa An yi Kusa da Karshe Gyaran Babban Hanyar Minna zuwa Suleja.

Jagoran hukumar NSEMA, Mista Inga ya bayyana da cewa da yawar gidaje, hanyoyi da gadoji ne ambaliyar ruwan ya lallace a kananan hukumomin Jihar.

“Haka kazalika ambaliyar ya shafi wuraren kiwon dabbobi, hanyar bin ruwar (kwalbati), makarantun firamare, asibitoci, tafkunan kifaye, da wuraren kiwon lafiya” inji Shi.

Naija News Hausa ta gane da cewa yawar ruwan sama a Jihar ne ya kawo sanadiyar ambaliyar.

Hukumar NEMA DG ta ce lamarin ya faru ne tsakanin watan Agusta da Satumba, kuma ta kara da cewa hukumar na ci gaba da karbar karin rahoto game da aukuwar ambaliya a jihar a halin da ake ciki.

Wadannan ne bangaren da ambaliyar ya shafa, bisa bayanin sa; Rafi, Gurara, Paikoro, Suleja, Agaie, Katcha, Kontagora, Gbako, da Shiroro. Sauran wuraren da abin ya shafa kuma sun hada da Bosso, Chanchaga, Mashegu, Edati, Lavun, Lapai da Mokwa.

Ko da shike dai Daraktan ya bayyana da cewa hukumar su ta riga ta samar da rahoton yanayin ga Ofishin Gwamnan Jihar, Abubakar Sani Bello (LoLo), don daukar mataki ta musanman kamin abin ya kara yawaita da mumunar barna a Jihar.

A kalla mutane 15 suka Mutu a Hatsarin Jirgin Ruwa da ya afku a Borgu, Jihar Neja

Naija News Hausa ta karbi rahoton mutuwar Mutane goma sha biyar a wani hatsarin jirgin ruwa da ya afku a kan kogin Malale da ke karamar Hukumar Borgu ta Jihar Neja.

Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja (SEMA) ta bada tabbacin al’amarin ga menama labaran gidan Talabijin na Channels a ranar Laraba da ta gabata.

Bisa bayanin Darakta Janar na hukumar, Mista Ibrahim Inga, ya bayyana da cewa abin ya faru ne a karshen mako da ta wuce, amma dai da cewa hukumar ta sami sanin hakan ne a ranar Talata da yamma saboda rashin sadarwa.

Ya kara a bayanin sa da cewa rahotannin da aka tattara sun bayyana da cewa kwale-kwalen akalla na dauke ne da yawar fasinjoji 50, ya kuwa  kife da su a tsakiyar kogin.

“Ko da shike, Shugaban SEMA ya fada da cewa a yayin da aka kubutar da wasu da suka tsira, wasu da dama kuma an rasa gane ko ina ne suke, amma ana kan kokarin ceto su.”

Wadanda abin ya rutsa da su sun bayyana da cewa hatsarin ya faru ne a yayin da suke dawowa daga kasuwar Warrah, wata karamar shiya a karamar hukumar Ngaski na zuwa Sabo Yumu a karamar hukumar Borgu lokacin da hatsarin ya faru.

Duk da cewa ba a iya bayyana sakamakon hadarin ba, amma ana diba da zargin cewa wata kila lodi ne yayi wa jirgin wata.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa Koramar Malale da wasu bakin ruwa da ke a Jihar na yaduwa da kashin mutane.

Mista Inga, ya bayar da cewa Gwamnatin jihar na a shirye don magance ire-iren hatsari kamar irin wannan.

Ya kuma kara da cewa Gwamnatin Jihar na kokari da ganin cewa an karfafa da kuma samar da kayan shiga Iho ga mazauna.

KARANTA WANNAN: Katsinawa ga taku! Kalli Rawan ‘Yan Katsina da baka san da shi ba

Anyiwa ‘yan wasan Kwallon Niger Tonadoes alkawarin naira dubu N500,000 a kowane Gwal da suka ci Kano Pillars

Hukumar kula da kwallon kafa ta jihar Neja ta sanar da alkawarin naira dubu N500,000 na kyauta akan kowane gwal da aka zira wa ragar ‘yan kwallon Kano Pillars a karshen gasar cin kofin Aiteo 2019.

An bayyana hakan ne a bakin Shugaban kungiyar, Hon. Adamu Aliyu, a lokacin da yake bayar da kudi na Naira Miliyan Daya da Dari Biyar (N1.5 Million) da aka baiwa ‘yan wasan kafin su kammala gasar Semi-final ga cin kofin Aiteo 2019, a hadewar su da ‘yan wasan kwallon Rivers United.

A wasar Semi-final din, Niger Tornadoes ta lashe ragar Rivers United da gwalagwalai 2-1 a filin kwallon Soccer Temple, Agege a Jihar Legas.

Bisa bayanin shugaban kungiyar kulob din, ya bayyana da cewa nasarar zai samar wa kulob din kimanin Naira Miliyan daya.

“A lokacin da kuke shirin buga wasar Semi-final, hukumar tayi maku alkawarin kudi naira miliyan daya, haka kazalika Shugaban Hukumar Tsaro kuma ya maku alkawarin naira dubu dari biyar (N500,000). Ina so in tabbatar maku da cewa kudin na a nan yanzun nan. Ga wasar karshe kuma, a kowane gwal da kuka iya saka a ragar su, za a bayar da kudi rabin miliyan daya, idan kun ci kwallaye hudu, tabbas akwai Naira miliyan biyu da karin Naira miliyan daya domin lashe wasan, ma’ana, akwai Naira miliyan 3 ajiye” in ji shugaban kulob din.

A karshe shugaban kulob din ya bayyana da cewa Gwamna Abubakar Sani Bello, gwamnan Jihar Neja zai kasance a kallon wasan, “kuma ba mamaki gwamnan shi ma ya bada nashi tallafi don murnan nasara” inji shi.

Aha! Kalli Hoton Gwamnan Jihar Neja da baka taba gani ba

Naija News Hausa ta ci karo da wani tsohon hotunan gwamnan Jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello.

Ka ga gwamna Bello ya chake da zanzaro cikin kakin bautan kasa (NYSC). Gidan labaran nan ta gane da cewa Gwamna Bello ya dauki wannan hoton ne a kamp lokacin bautan kasar a birnin Calabar. Ko da shike yayi bautan kasar ne a birnin Port Harcourt, babban birnin tarayyar Jihar Rivers.

Ka tuna Naija News Hausa ta ruwaito da  tsohin hotunan shugaba Muhammadu Buhari da matarsa Aisha Buhari.

Kalli Hoton Gwamna Alhaji Abubakar Sani Bello a kasa;

Shugaba Muhammadu Buhari na ganawar Kofa Kulle da Gwamnonin Jiha

Shugaba Muhammadu Buhari a yau Litini, 27 ga watan Mayu na ganawa da Gwamnonin Arewacin Jihohin kasar Najeriya a nan fadar shugaban kasa, birnin Abuja.

Ko da shike ba a bayyana ko menene dalilin taron gaggawar ba, amma manema labarai na hangen cewa ba zai wuce yanayin matsalar hare-hare da ake fuskanta ba a kasar, musanman Arewacin kasar.

Naija News Hausa na da sani da fahimtar cewa kashe-kashen rayuka na yaduwa a koyaushe a arewacin kasar Najeriya, musanman daga ‘yan ta’addan Boko Haram da kuma Makiyaya Fulani.

Ka tuna a hangen magance hakan ne hukumar Jami’an tsaron ‘Yan Sandan Najeriya suka kafa wata rukunin Tsaro da suka kira ‘Operation Puff Adder’, duk da hakan matsalar harwayau bai bai sauya ba a kasar.

Bisa rahotannai, a ranar jiya Lahadi, an rasa rayukan mutane da gidajen zama a shiyar Dutse Uku, Rikkos da kuma Gadar Cele ta garin Jos, Jihar Filato, a wata sabuwar harin da ‘yan ta’adda suka kai.

Taron shugaban kasar da Gwamnoni Arewacin kasar ya samu halartan Gwamnoni kamar su; Nasir el-Rufai, gwamnan Kaduna; Kashim Shetima, Gwamnan Jihar Borno; Yahaya Bello, Gwamnan Jihar Kogi; Simon Lalong, Gwamnan Jihar Filato; Aminu Tambuwal, Gwamnan Jihar Sokoto; Atiku Bagudu, Gwamnan Jihar Kebbi da kuma Abubakar Sani Bello, Gwamnan Jihar Neja.

Diyar A. A. Kure, Tsohon Gwamnan Neja ta Mutu

Mai rana ya dauki abinsa! Tsohon Gwamnan Jihar Neja, Abdulkadir Kure ya rasa diyar shi na farko.

Naija News Hausa ta karbi rahoto da safen nan da cewa Fatima Abubakar Kure, diyar Tsohon Gwamnan Jihar Neja ta Mutu a birnin Abuja, babban birnin Tarayyar kasar Najeriya.

Gidan labaran nan ta mu ta samu sanin cewa Fatima ta mutu ne da barin yaron ta daya da ta haifa.

Ko da shike ba a gabatar da cikakken bayani ba game da rasuwar ta, amma dai Alhaji Abubakar Sani Bello, Gwamnan da ke kan kujerar mulkin Jihar Neja, ya gabatar da gaisuwar ta’aziyya ta musanman ga Iyalan Tsohon Gwamnan.

Gwamna Bello ya yi mamaki da mutuwar Fatima, ya kuma yi addu’a da cewa Allah ya ba Fatima madawwamiyar hutawa, ya kuma sa ta ga Jannatul Firdausi.

“Allah ya sa Fatima ta huta lafiya, ya sa ta ga Jannatul Firdausi, ya kuma baiwa dukan Iyalin Kure karfin zuciya na daukan kaddarar mutuwar Fatima.” inji Gwamna Bello.

Bincike ya bayar da cewa an riga an bizine Fatima a birnin Abuja, Allah ya sa ta huta Lafiya.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Sanatan da ke Wakilcin Jihar Kogi a Gidan Majalisar Dattijai, Sanata Dino Melaye, ya rasa tsohuwar sa, Deaconess Comfort Melaye.

Jihar Neja ta gabatar da kashin Biliyan N3.2b don gyara Gidan Gwmnati

A wata sanarwa ta yau, Jumma’a, 22 ga watan Maris, an sanar da cewa Gwamnatin Jihar Neja ta kadamar da kashe kudi kimanin naira Biliyan N3.2b don sake tsarafa ginin gidan gwamnatin Jihar da ke a Minna, babban birnin Jihar Neja.

A bayanin Zakari Jikantoro, Kwamishanan Aikace-aikacen Jihar Neja, ya bayyana ga manema labarai a ranar Alhamis da ta gabata a garin Minna da cewa aikin gidan gwamnatin ya kasu biyu ne.

Jikantoro ya cigaba da cewa kashi na daya ya riga ya ci kudi naira biliyan N2.1 wanda aka riga aka gama da aikin; Kashi ta biyun kuma zai ci kimanin kudi naira biliyan N1.6, kuma an riga an bayar da aikin ga ma’aikata.

Ya kara da cewa kashi na biyun aikin ya kunshi gina gidan baki, wajen iyo ko ninkaya da sauransu.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Abubakar Sani Bello, Gwamnan Jihar Neja ya kafa wata kwamiti da za ta samar da mafita ga raguwa da kuma matsalar issashen karfin wutan lantarki da ake fuskanta a Jihar.

Gwamnan ya bayyana da cewa wutan tsawon awowi shidda (6Hrs) da hukumar Abuja Electricity Distribution Company (AEDC) ke bayar wa ga kananan hukumomin Jihar bai dace ba.

Karanta wannan kuma: Wata mugun tsawa ta kashe mutane 3 a karamar hukumar Ughelli ta Jihar Delta

Gwamnan Jihar Neja ya kafa kwamiti don karfafa karfin wutan lantarkin Jihar

Abubakar Sani Bello, Gwamnan Jihar Neja ya kafa wata kwamiti da za ta samar da mafita ga raguwa da kuma matsalar issashen karfin wutan lantarki da ake fuskanta a Jihar.

Gwamnan ya bayyana da cewa wutan tsawon awowi shidda (6Hrs) da hukumar Abuja Electricity Distribution Company (AEDC) ke bayar wa ga kananan hukumomin Jihar bai dace ba.

“Ban amince da wutan lantarki na awowi shidda da AEDC ke bayarwa ga Minna, babban birnin Jihar Neja da sauran kananan hukumomin Jihar ba” inji Gwamnan.

Kwamitin da Gwamnan ya kafa ya kunshi, Mataimakin sa ga kujerar Gwamna, Alhaji Ahmed Mohammed Ketso da Kwamishanan Kudi, Hon. Mallam Zakari Abubakar.

Gwamna Bello ya umurce su da ganawa da hukumar AEDC ta Abuja tsakanin nan da awowi 24 da kuma tabbatar da cewa an samu canji daga yadda ake bayar da wuta a garin Minna da sauran kananan hukumomi da ke kewaye da ita.

Ya kuma sanya Alhaji Ahmed Mohammed Ketso ga jagorancin kwamitin.

Naija News Hausa ta gane da cewa Jihar Neja na da Dam da kuma sanfarin dan dama da ke bayar da wutan lantarki ga kasar Najeriya, amma Jihar na kuma daya daga cikin Jihohin kasar da ke samun matsalar wuta.

Gwamna Abubakar ya lashe kujerar Gwamnan Jihar Neja – INEC

Hukumar gudanar da zaben kasa (INEC) ta gabatar da Abubakar Sani Bello, Gwamnan Neja a matsayin mai nasara ga lashe zaben kujerar gwamnan Jihar Neja a zaben ranar Asabar, 9 ga watan Maris da aka yi.

Naija News ta iya gane da cewa Gwamna Bello ya lashe kananan hukumomi 24 daga cikin hukumomi 25 da ke a jihar. Gwamna ya fiye babban dan adawan shi daga jam’iyyar PDP, Alhaji Umar Nasko da kuri’u.

Ga takaitaccen kuri’un wasu kananan hukumomin kamar haka;

Agaie

APC – 19,295

PDP – 16,903

Mashegu

APC – 18,102

PDP – 10,988

Mariga

APC – 17,890

PDP – 13,433

Magama

APC – 20,546

PDP – 17,633

Bargu

APC – 25,111

PDP – 7,206

Suleja

APC – 19,105

PDP – 14,975

Bida

APC – 21,493

PDP – 11,212

Agwara

APC – 11,236

PDP – 5,365

Lapai

APC – 24,724

PDP – 10,599

Shiroro

APC – 28,285

PDP – 16,438

Mokwa

APC – 26,679

PDP – 13,155

Kuri’ar Kontagora a lokacin nan bai bayyana ga kamfanin mu ba amma zamu gabatar da shi a baya inda hakan ya samu. da sauran kananan hukumomi.

Jam’iyyar PDP ta Jihar Neja sun gabatar da Azumi don nema sa’a ga Umar Nasko, dan takaran Gwamnan Jihar

Zaben gwamnonin Jihar kasa ta bana ya bayyana da zafi da gaske a yayin da Jam’iyyar PDP suka gabatar da azumin kwana biyu da mambobin ta don nema sa’a da nasara ga dan takaran su na kujerar gwamnan Jihar Neja.

Naija News Hausa ta gane da cewa Alhaji Umar Mohammmed Nasko, dan takaran kujerar gwamnan Jihar Neja daga jam’iyyar adawa ta PDP ne babban dan takara da ke jayayya da Alhaji Abubakar Sani Bello (LOLO), gwamna da ken kan mulkin Jihar a halin yanzu.

Jam’iyyar sun gabatar da hidimar azumi na kwana biyu ne don neman fuskar Allah ta wajen addu’a don samun nasara ga Jam’iyyar ga zaben tseren kujerar Gwamnan Jihar a shekara ta 2019.

Hidimar azumin zai dauki tsawon kwana biyu ne kawai, watau daga ranar Alhamis 7 ga watan Maris zuwa ranar Jumma’a 8 ga Watan Maris, 2019. Kamar yadda jam’iyyar suka gabatar.

Ga sanarwan kamar haka;

AZUMI! AZUMI!! AZUMI!!!

Sanarwa ga duk masoyan Umar Nasko, Ana bukatar mu duka da azumin kwanaki biyu, daga ranar Alhamis zuwa Jumma’a don neman fuskar Allah ga nasarar zaben gwamna.

Naija News Hausa ta kuma gane da cewa, Alhaji Tanko Beji, ciyaman na Jam’iyyar PDP a Jihar ya bukaci masoya, al’ummar duka da ke goyon bayan jam’iyyar PDP da su fito da yawar su ranar Asabar ta makonnan don jefa kuri’ar su ga dan takaran su.