Oshiomhole Ya Ki Karban kyaututtukan Kirsimeti Daga Obaseki

Shugaban jam’iyyar APC na kasa baki daya kuma tsohon gwamnan jihar Edo, Comrade Adams Oshiomhole, ya yi watsi da kyaututtukan Kirsimeti da gwamnatin jihar Edo ta aika masa.

Mista Crusoe Osage, mai ba bada shawarwari ga gwamnan jihar Edo kan harkokin yada labarai da sadarwa, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a Benin a ranar Laraba.

Naija News ta ruwaito a baya da cewa Adams Oshiomhole, ya dage kan ci gaba da wata zagayen Rali da suka shirya yi a jihar Edo.

Manyan membobin jam’iyyar APC daga Abuja sun shirya da halartar taron gangamin don marabtan tsohon dan takarar gwamna Fasto Osagie Ize-Iyamu da daruruwan magoya bayansa, daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a tasu jam’iyyar.

Kodashike, Mataimakin gwamnan jihar, Philip Shuaibu ya wallafa wata wasika ga Sufeto Janar na ‘yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, da neman ya dakatar da zanga-zangar saboda hakan na iya haifar da tashin hankali a yankin.

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 17 ga Watan Disamba, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 17 ga Watan Disamba, 2019

1. Rundunar Sojojin Najeriya Sun Sarwake Major Janar 20, Brigadier Janar 10

Rundunar Sojojin Najeriya sun sake girke Manjo-janar 20 da Birgediya-Janar 10 a cikin abin da ake gani a zaman babban koma-baya a rundunar.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa Sojojin Najeriya sun ba da sanarwar sake daukar manyan hafsoshin sojojin ne a cikin wata sanarwa da suka fitar a ranar Litinin, 16 ga Disamba ta hannun Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Kanal Sagir Musa.

2. Boko Haram: Leah Sharibu Ta Saura Da Rai – Bisa Bayanin Malamin Jami’a Da Aka Sace

Wani Malamin Jami’ar wata kwaleji da wasu mutane goma wadanda kwanan nan ‘yan ta’addan Boko Haram suka sace su, sun yi kira ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da su daukin matakin ceton su daga hannun ‘yan ta’addan.

Wannan na zuwa ne awanni 24 kacal bayan kisan wasu ma’aikatan agaji hudu da kungiyar Boko Haram ta yi. ‘Yan ta’addan sun sace ma’aikatan agajin ne da a baya aka kashe a kan babbar hanyar Damaturu zuwa Maiduguri.

3. Kotu ta Ba da hukuncin Karshe akan Gwamna Ganduje Kan Cin Hanci Da Rashawa

Kotun Tarayya da ke zaune a Kano ta yi watsi da wata kara da wani lauya a Kano, Bulama Bukarti ya shigar a gabanta na neman umarnin kotun da ta tilasta wa Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arziki Kasa Ta’annati (EFCC) don ta binciki gwamna Abdullahi Ganduje bisa zargin karbar cin hancin daga hannun wani dan kwangila.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ba da rahoton cewa babbar kotun tarayya da ke zamanta a Kano, arewacin Najeriya, ta yi watsi da karar a ranar Litinin da yamma, 16 ga Disamba saboda “rashin hujja”.

4. Dalilin da yasa DSS baza ta iya sakin Omoyele Sowore ba – Malami

Babban Lauyan Tarayya da kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya ce ba zai iya ba da umarni ga ma’aikatar ta DSS ba don su saki Omoyele Sowore.

Malami ya fadi hakan ne don mayar da martani ga kiran kalubalai da lauya da kuma mai ba da shawara ga Sowore, Femi Falana (SAN), ya bayar na neman shi da ya umarci ‘yan sanda asirin da su saki Sowore.

5. APC Ta Janye Dakatarwar Da Aka Yiwa Akeredolu, Okorocha da Sauransu

Shugabannin jam’iyyar APC ta kasa baki daya a ranar Litinin sun dage dakatarwar a kan Gwamna Rotimi Akeredolu, Sanata Ibikunle Amosun, Sanata Rochas Okorocha, Mista Osita Okechukwu, da Fasto Usani Uguru Usani.

Jam’iyya mai mulki ta sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ta sanya wa hannu, wace kuma ta aika wa kamfanin dilancin labarai ta Naija News ta hannun Sakataren yada labarai na kasa ga Jam’iyyar, Lanre Issa-Onilu.

6. Sarkin Bichi Na Jihar Kano Ya Tsige Hakimai 5

Alhaji Aminu Ado Bayero, Sarkin Bichi a jihar Kano, Arewacin Najeriya, ya kori Shugabannin Gundumomi guda biyar a yankin nasa.

Naija News ta samu labarin cewa an cire Shugabannin Gundumomi biyar ne saboda rashin biyayya ga Sarki Aminu Ado Bayero da masarauta bi da bi.

7. Wata Rukuni Na Zargi Fayemi da yin Makirci don maye gurbin Osinbajo da Tsige Oshiomhole

Bangaren yada labarai ta Jam’iyyar PDP a reshen jihar Ekiti, ta zargi gwamna Kayode Fayemi da shirya makarkashiyar maye gurbin Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osinbajo.

A wata sanarwa da kungiyar ta fitar ranar Litinin ta hannun Bola Agboola, kungiyar ta nemi tsohon Ministan da ya daina shirin tsige Shugaban Jam’iyyar na kasa baki daya, Adams Oshiomhole.

8. Ni Ba ‘Yar Kano Bace, Saboda Haka Ba Ku Da Iko A Kaina – Sadau Ta Gayawa Kannywood

Jaruma Rahama Sadau ta bayyana da cewa shugabancin kungiyar masu shirya fina-finan Hausa a Kano wace aka fi sani da Kannywood, cewa basu da ikon daukan matakan hukunci a kanta, don ita ba ‘yar Kano ba ce.

Wannan zancen ya fito ne a wata sanarwa da shugaban kungiyar masu shirya fina-finai ta Arewa reshen jihar Kano, Jamilu Ahmed Yakasai ya bayar a wajen bikin rantsar da sababbin shugabannin kungiyar reshen jihar Kano, wanda ya gudana a ranar Lahadi, 15 ga watan Disamba 2019.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya ta Yau a Naija News Hausa

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 16 ga Watan Disamba, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 16 ga Watan Disamba, 2019

1. Shugaba Buhari Ya Taya Ajimobi Murnan Cika Shekara 70

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya tsohon gwamnan jihar Oyo, Abiola Ajimobi murnar cika shekara 70 da haihuwa yau, 16 ga Disamba, 2019.

Buhari a cikin wata sanarwa da ya bayar ta hannun mashawarcinsa ta musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina, ya taya Abiola Ajimobi ga dimbin nasarorin da ya samu a bangarorin kamfanoni da na gwamnati.

2. Tsohon Shugaban Najeriya, IBB bai Mutu ba

Naija News Hausa ta fahimta da cewa Ibrahim Badamosi Babangida (IBB), tsohon Shugaban Najeriya bai mutu ba, kamar yadda ake yada wa.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa rahotanni sun bayyana a wasu sassan kafafen yada labarai na Najeriya a safiyar ranar Lahadi, inda suke nuni da cewa Tsohon Shugaban na Najeriya ya mutu amma mai magana da yawun sa ya fitar da sanarwa inda ya karyata rahoton.

Mai magana da yawun IBB, Kassim Afegbua a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadin, 15 ga Disamba, ya bayyana rahotannin mutuwar IBB da cewa “labarai ne na karya”.

3. Sharia: CAN Ta Yi Kukan Cewa A Tsige Babban Alkalin Najeriya CJN Tanko

Kungiyar Kiristocin Najeriya (CAN) ta yi Allah wadai da kiran da babban mai shari’a na Najeriya (CJN), Muhammad Tanko ya yi, na yi wa kundin tsarin mulkin kasar kwaskwarima don “karbar tallafawa wasu damuwar musulmai da kuma kafa dokar Shari’a.”

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa Tanko Muhammad ya gabatar da wannan kudurin ne yayin da yake ayyanar taron Taro na Shekaru 20 da aka bude a Jami’ar Ahmadu Bello (ABU), Zariya a ranar Laraba da ta wuce.

4. APC/PDP: Dan Takaran Shugaban Kasa Atiku Ya Hade Da Asiwaju Tinubu A Jihar Neja

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Atiku Abubakar a ranar Asabar da ta gabata ya gana da tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu.

Naija News ta fahimci cewa Tinubu ya hade da Atiku a Minna, babban birnin jihar Neja ne don karbar lambar girmamawa ta jami’ar Ibrahim Badamosi Babangida, Lapai.

Gwamnan jihar Neja, Sani Bello, ya karbi Tinubu da mukarraban sa a lokacin da suka isa wajen hidimar.

5. Mashahurin Sarkin Kudu Maso Yamma ya Saki Matarsa ‘Yar Jamaica

Oba Abdulrasheed Akanbi, Oluwo na Iwoland, ya rabu da matar sa ‘yar kasar Jamaica, Chanel Chin.

Hakan ya bayyana ne ta bakin Sakataren yada labarai na Oluwo, Ali Ibrahim a wata sanarwar da ya bayar a ranar Lahadi.

6. Rikicin APC: Obaseki Da Shuaibu Na Barazanar Murkushe Ni – Oshiomhole

Shugaban Hidimar Zabe ga jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Comrade Adams Oshiomhole, ya zargi gwamna Godwin Obaseki da mataimakin sa, Phillip Shuaibu da yin barazanar murkushe shi.

A wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi ta hannun Babban Sakataren yada labaran sa, Simon Egbuebulem, tsohon gwamnan jihar Edo ya ce gwamna Obaseki da mataimakinsa ba su da tasirin siyasa a yankinsu domin cin zabe.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya Ta Yau a Naija News Hausa

Oshiomhole Yayi Watsi Da Umarnin IGP, Ya Dage A Kan Cewa Dole Ne APC Tayi Rali A Edo

Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC) na tarayya, Adams Oshiomhole, ya dage kan ci gaba da zagayen Rali da suka shirya yi a jihar Edo.

Naija News ta tattaro cewa manyan membobin jam’iyyar APC daga Abuja sun shirya da halartar taron gangamin don marabtan tsohon dan takarar gwamna Fasto Osagie Ize-Iyamu da daruruwan magoya bayansa, daga jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a tasu jam’iyyar.

Kodashike, Mataimakin gwamnan jihar, Philip Shuaibu ya wallafa wata wasika ga Sufeto Janar na ‘yan sanda (IGP), Mohammed Adamu, da neman ya dakatar da zanga-zangar saboda hakan na iya haifar da tashin hankali a yankin.

A yayin mayar da martani ga sakon, IGP ya umarci Kwamishinan ‘yan sanda a jihar Edo don tabbatar da cewa an dakatar da zanga-zangar. Amma shi Oshiomhole ya bukaci magoya bayan sa da kada su karaya, ya kara da cewa zai nemo mataki na gaba kan zanga-zangar.

“Na san cewa kun damu da gaske game da abin da muke fuskanta a nan, amma ina so in rokeku da kada ku fusata. Duk wani shugaban jam’iyya mai hankali zai yi murna da marabtan mutane daga wata jam’iyyar zuwa jam’iyyarsa,” inji shi Oshiomhole.

“Musamman lokacin da ya zama cewa masu shigo jam’iyyar sun kasance ne mutanen da suka yi gwagwarmaya da gaba da jam’iyyar a babban zaben da ya gabata inda muka fiye su da yawar kuri’u kamar dubu 50,000. Don haka muke a Benin don marabtan su amma zaka ga yadda azzaluman su ke jefa mutane cikin rikici.”

“Amma ina so in shaida muku, APC gidan mu ne ba za mu lalata shi ba kuma ba za mu bar kowa ya rusa shi ba. Ba ma son a kashe kowa, don Allah kar ku yaƙi kowa. Wadanda suka san ni sun san ni ba matsoraci bane, bana tsoron fada. Amma ba zan yi hakan ba kuma ina roƙonku da ku natsu.”

“Muna samun rahoton da ruduwa a yanzu, IG na ‘yan sanda a da ya umarci Kwamishinan ‘yan sanda ya ba mu kariya daga taronmu. Amma a yanzu ana gaya mana cewa wannan kariyar an soke ta. Amma zan yi kira don gano menene matsalar idan ‘yan sanda suna cewa ba za su iya yi mana kariya ba ga zanga-zangar siyasa. Zan bincika kuma in sanar da ku. Amma ko da sun ce ba za mu iya bamu kariya ba, don Allah kar a yaƙi kowa. Zan haɗu da su, in nemo lokacin da za a ci gaba da zanga zangar. Amma dai zanga-zangar zata ci gaba dole wata rana… Babu wanda zai girgiza zuciyar mu. Zamu karbi ‘yan uwanmu a cikin jam’iyyar don karfafa jam’iyyar.”

APC: ‘Yan Zanga-Zanga Sun Mamaye Titi da Bukatar a Tsige Oshiomhole

Wasu masu zanga-zanga a ranar Juma’a (yau) sun bukaci a cire Adams Oshiomhole a matsayin sa na Shugaban Jam’iyyar APC na kasa.

A wasu hotuna da Naija News Hausa ta ci karo da su a wata labarai da aka bayar a Premium Times, an gano masu zanga-zangar dauke da rubuce-rubuce zuwa sakatariyar jam’iyyar APC na kasa.

Wasu daga cikin katunan suna da rubutu kamar haka, “Dole ne Oshiomhole Ya Tafi”, “Barawo” da dai sauransu.

Naija News ta kula da cewa masu zanga-zangar, akasarinsu matasa ne, amma a yayin da suke gudanar da zanga-zangar, wasu tarin ‘yan ta’adda matasa kuma sun fito daga wata hanya inda sakatariyar APC ta ke. Suka kuwa hari masu zanga zangar da jifan duwatsu da sanduna domin tarwatsa su.

Akalla mutum guda ya jikkata a tashin hankalin. Ko da shike ba wanda ya gane ko wanene ke tallafawa masu zanga-zangar, amma ana zargin cewa wasu shugabannin jam’iyyar ta APC ne tare da wasu gwamnonin jam’iyyar ke kokarin ficewar Mista Oshiomhole a shugabancin jam’iyyar.

KARANTA WANNAN KUMA; 2023: Tsohon Gwamnan Jihar Zamfara, Ahmad Sani Yarima Ya bayyana Shirin Fita Takarar Shugaban Kasa.

2023: Ga Takaitaccen Hirar Tarayyar APC da Shugaba Buhari ya jagoranta

Shugaban hidimar neman zaben Jam’iyyar APC na ƙasa, Comrade Adams Oshiomhole, Da yake jawabi bayan taron wanda ya ƙare da misalin ƙarfe 11:30 na yammacin ranar Alhamis, ya ce batutuwan da aka tattauna yayin taron daren jiya sun haɗa da aiwatarwa a zaɓen da suka gabata, batutuwan yau, kasafin kuɗi, shari’ar kotu, da kuma batun ladabtarwa.

Oshiomhole ya ce, “Kun san wannan ganawar ta tarayyar jam’iyyar ne. Ainihin, taron ya kasance ne kawai don nazarin ayyuka a zabukan da suka gabata, abubuwan da suka shafi yau, kasafin shekara mai zuwa, da batutuwan horo. Kun san rukunin APC din kamar majalisar dattawa ne don yin magana kan abubuwa da yawa waɗanda zamu tattauna a NEC a gobe (watau a yau).”

Shugaban Jam’iyyar APC na kasa wanda ya yi maganansa ta karon farko bayan furucin Darakta Janar na kungiyar ci gaban Gwamnonin (PGF) Salihu Mohammed Lukman kan yadda yake tafiyar da jam’iyyar, ya yi watsi da kalaman da Lukman ya yi.

“Babu matsin lamba. An shirya taron NEC kamar watanni biyu da suka gabata. Muna jiran kawai ranar ta zo ne. An sanar da shi ne watanni biyu da suka gabata. Kuma za a gudanar da shi ne a gobe (watau yau). Shin ba ku san da wannan ba?”

“Kana maganar abin da Mista Salihu Lukman ya fada, Wannan shine ra’ayinsa. Tun ma kafin ya fadi haka, an shirya wannan ganawar. Ba daidai bane a gudanar da taro,” in ji shi.

“Muna da taron NEC don duba bayanan asusunmu na shekarar da ta gabata, kasafin kudin shekara mai zuwa, matsalolin da suka taso lokacin zabuka da kuma bayan zabuka, da kuma sakamako daban-daban da suka shafi kotu; wanda muka ci nasara da wanda muka rasa; ci gaba; al’amurra a wasu jihohi inda muke da sabani da kuma yadda za mu warware rashin jituwa. Ina tsammanin haka ne. Kuma taron ya gudana yadda ya kamata. Kuma za ka iya ganin shugaban kasan a zaune har karshen taron.” Inji Oshiomhole.

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 21 ga Watan Nuwamba, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 21 ga Watan Nuwamba, 2019

1. 2023: Tinubu Ya Dace da Zaman Shugaban Kasa – Guru Maharaj Ji

Wanda ya kafa kungiyar ‘One Love Family’, mai suna Satguru Maharaj Ji, ya ce shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Bola Tinubu, ya cancanci zama shugaban kasa a 2023.

Ya bayyana hakan ne a ranar Laraba yayin da yake Magana a wani taron tattaunawa da aka gudanar a kauyen Maharaj Ji.

2. Sagay ya Tabbatar da Kama Tsohon Babban Janara, Adoke

Shugaban kwamitin ba da shawara ga shugaban kasa kan yaki da cin hanci da rashawa, Farfesa Itse Sagay, ya tabbatar da kama tsohon babban Janarar Tarayya da kuma Ministan Shari’a, Mohammed Adoke.

Sagay ya tabbatar da kamun ne yayin wata ziyarar girmamawa a hedikwatar Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) a jiya, 20 ga Nuwamba.

3. EFCC ta gurfanar da Maina a gaban Kotu saboda tuhumar da ake masa

A ranar Laraba da ta wuce ne aka gurfanar da Abdulrasheed Maina a gaban Mai shari’a Abubakar Kutigi na Babbar Kotun FCT da ke Gwagwalada kan tuhumar da ake masa na satar fasaha.

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa (EFCC) ta gurfanar da Maina ne akan tuhume-tuhume tara da ake zargi da badakalar cin hancin na Miliyan N738.6m.

4. Jam’iyyar APC ta tura Manyan Wakilai Zuwa Jihar Edo

Jagorancin jam’iyyar APC na kasa ta tura wata tawaga mai cikakken iko don shawo kan rikice-rikicen da ke afkuwa a jam’iyyar anan jihar Edo.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole da gwamna Godwin Obaseki na jihar Edo na munsayar yawu tun da dadewa.

5. Kogi: Dino Melaye Ya Hari Ofishin INEC Da Faifan Bidiyo 21 Don Neman Soke Zabe

Sanatan da aka kora kwanan nan mai wakiltar mazabar Kogi West Senatorial, Dino Melaye, a yau ya ziyarci hedikwatar Hukumar Zabe ta kasa (INEC) don neman a soke zaben ranar 16 ga Nuwamba a gundumar.

Dino a isarsa Ofishin ya samu marabta daga hannun Sakataren INEC, Rose Orianran-Anthony da kwamishina na kasa / Shugaban Kwamitin yada labarai da kwamitocin Ilimin masu jefa kuri’a, Festus Okoye.

6. Kudurin Dokar Shafin Sadarwa ta Yanar Gizo ya Bayyana a Majalisar Dattawa a karo Ta Biyu

Dokar kafofin watsa labaru da Sadarwa a ranar Laraba ya sake bayyana a karatu na biyu a cikin Majalisar Dattawa. Ana sa ran dokar za ta hana yin karya kan yanar gizo ga ‘yan Najeriya idan har aka sanya su cikin doka.

Sanata mai wakiltar Mazabar Gabas ta Tsakiyar Jihar Neja, Musa Mohammed Sani, shine ya gabatar da kudirin a Majalisar kasa.

7. Shugaba Buhari ya sanya hannu kan dokar zartarwa 009

A ranar Laraba da ta gabata, Shugaba Muhammadu Buhari ya sanya hannu a kan Dokar zartarwa ta 009 don kawo karshen matsalar kashi a fili a Najeriya a shekarar 2025.

Sabuwar dokar da Buhari ya sanyawa hannu ta ce, “A ganin wannan dokar, Ana hangen Najeriya da fita tsarin kasashe da ake kashi a fili daga nan har zuwa 2025.

8. Tsohon Shugaban Kasa Jonathan Ya Cika Shekaru 62, Ga Sakon Shugaba Buhari Zuwa Gareshi

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nuna wa tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan murna a cikar shekara 62 ga haihuwarsa ta.

Buhari ya taya Jonathan murna ne ta hanyar hada kai da ‘yan kasar da yin addu’o’in tsawon rai, lafiya da kuma karin karfin gwiwa don ci gaba da yiwa kasa hidima.

9. Kotu Ta Dakatar da ‘Yan Majalisar PDP Biyu a Kaduna, Ta Bada Umarnin Sake Zabe

Kotun daukaka kara wacce ke zaune a jihar Kaduna ta sallami wasu mambobi biyu a majalisar dokokin jihar Kaduna a ranar Talata.

‘Yan Majalisa biyun suna wakilci yankin Kagarko da Sanga bi ne a majalissar dokokin jihar Kaduna.

Naija News ta fahimci sunan ‘yan majalisa biyun da a kora da, Mista Morondia Tanko mai wakiltar mazabar Kagarko da Malama Confort Amwe na mazabar Sanga duka biyu a dandalin Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Ka sami kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Jumma’a, 1 ga Watan Nuwamba, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Jumma’a, 1 ga Watan Nuwamba, 2019

1. Shugaba Buhari Ya Isa Makka Don Umrah

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari wanda ya tafi kasar Saudi Arabiya ranar Litinin ya isa Makka a ranar alhamis a karshen Taron kwanaki uku na zuba jari a a kasa wanda ya gudana a Riyadh.

Shugaba Buhari ya karbi marbata ne daga hannun Yariman Sarki Bader bin Sultan bin Abdulaziz, Mataimakin Gwamna na Yankin Makka da sauran jami’an gwamnati a filin jirgin sama na Sarki Abdulaziz, Jeddah, da misalin karfe 7.05 ta maraice a lokacin gida.

2. Shugaba Buhari bai kai Obasanjo Zuwa Kasar Waje ba  – Inji Oshiomhole

Ciyaman tarayyar jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a hidimar neman zabe, Adams Oshiomhole, ya ayyana da cewa Cif Olusegun Obasanjo ya yi tafiya fiye da Shugaba Muhammadu Buhari a lokacin da yake shugabancin Najeriya.

Oshiomhole ya gabatar da wannan furcin ne a yayin da yake kokarin kare yawon shakatawa da yawa na Shugaba Buhari tun lokacin da aka zaɓe shi a matsayin shugaban Najeriya a shekarar 2015.

3. EFCC ta gayyaci ‘Yan Kasuwa na kasashen waje don su Sayi Mallakar Diezani ta Biliyan N14.4bn

Hukumar Yaki da Cin Hanci da Rashawa da kare Tattalin Arzikin Kasa (EFCC) ta tuntuɓi ‘yan kasuwa na ƙasan waje don sayan kayan ado mai tsadar dala miliyan 40 (kusan Naira biliyan 14 a kudin Najeriya), waɗanda aka karɓa daga tsohuwar Ministan Albarkatun Man Fetur, Diezani Alison-Madueke.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa mukaddashin shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa, Ibrahim Magu ne ya bayyana hakan.

4. Biafra: Nnamdi Kanu Ya Bada Sharadin Da Zai Dawo da Shi A Najeriya

Shugaban kungiyar ‘Yan asalin yankin Biafra (IPOB), Mazi Nnamdi Kanu ya ba da sharadin dawowarsa Najeriya don ci gaba da fuskantar shari’a.

Shugaban kungiyar IPOB ya ce a shirye yake ya dawo kasar ya fuskanci shari’a idan har kotu ta iya ba da tabbacin lafiyarsa.

5. Shugaban Jam’iyyar APC yayi Magana kan Tsarin Shugabanci

Ciyaman Tarayyar Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole, yayi alwashin ba zai amsa a bainar jama’a ba game da zarge-zargen da Farfesa Itse Sagay ya yi masa.

Naija News ta tuno da cewa Sagay, Shugaban Kwamitin Shugaban Kasa kan yaki da cin hanci da rashawa (PACAC), ya ce tsaurin ra’ayi da tsarin Oshiomhole zai sa jam’iyyar ta rasa iko a wasu jihohin kasar.

6. Gwamnatin Tarayya Ta Dage Kuntatawa ga Wasu Kamfanoni Masu Zaman Kansu Guda biyu a arewa maso gabas

Gwamnatin Tarayyar Najeriya a jagorancin Shugaban kasa Muhammadu Buhari ta amince da sauya dakatarwar da aka sanya kan kungiyoyi biyu na agaji na kasa da kasa (kungiyoyi masu zaman kansu) a Arewa maso Gabas.

Naija News ta tuno da cewa, rundunar ‘Operation Lafiya Dole” ta rundunar sojojin Najeriya ta dakatar da wadannan kungiyoyi masu zaman kansu guda biyu, a ranar 19 ga Satumbar da 24 ga Satumbar, a bisa zargin cewa suna wadatar da abinci da magunguna ga maharan Boko Haram.

7. Zaben Kogi: INEC ta bayyana Abin da Zai Faru da Yahaya Bello Akan Rijista Biyu

Hukumar Gudanar Da Zaben Kasa (INEC) ta bayyana matsayinta kan tuhume-tuhumen yin rijistar mutum biyu da aka yi wa Gwamna Yahaya Bello na Jihar Kogi.

Naija News ta tuno da cewa Natasha Akpoti, memba a cikin jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), ta nemi wata babbar kotun tarayya da ke Abuja da ta tsige gwamnan daga sake neman takara a jihar Kogi game da batun rajistar ninki biyu a matsayin mai jefa kuri’a.

8. Mazauna Sun Guje A Yayin da Wata Motar Tanki ta Fadi A Onitsha

Wata mummunar bala’i ta afku a ranar Alhamis bayan da wata motar tanki da ke dauke da man fetur ta rutsa cikin wata rami a kan titin Onitsha / Enugu ta tashar Chipex, da ke Onitsha.

Ko da shika a lokacin da aka wallafa wannan rahoto, ba a samu barkewar gobara ba daga faduwar motar, amma wata majiya ta ce mazauna kusa da yankin suna tserewa daga wurin saboda fargabar barkewar wutar.

Ka samu Kari da Cikakken Labaran Najeriya ta Yau a Naija News Hausa

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 22 ga Watan Yuli, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 22 ga Watan Yuli, 2019

1. Anyi karar Buhari, Tsohin shugaban kasa da wasu manya a kasar Najeriya ga Hukumar ICC

Hukumar Socio-Economic Rights and Accountability Project (SERAP) ta gabatar da wata zargi a gaban Alkalin Kotun International Criminal Court (ICC), Malama Fatou Bensouda, da bukatar ta da binciken rashin kulawa da shugabancin kasar ta nuna ga yaran da basa a makaranta a kasar Najeriya.

Hukumar SERAP a cikin karar, ta gargadi Alkali Bensouda da binciken rashin jinkirtan Manya a kasar Najeriya akan al’amarin da tsawon shekaru da suka gabata.

2. Boko Haram: Hukumomin Tsaro sun gano da inda aka katange Masu taimaka wa kiwcon lafiya da aka fyauce a baya

Hukumomin tsaro da ta kunshi hukumar rundunar Sojojin Najeriya sun gano da inda mutanen da aka bayyana da bacewa a baya suke.

Naija News ta fahimta da cewa mutanen sun bace ne tun kwanakin baya a wata hari da ‘yan ta’addan Boko Haram suka kai a shiyar da su ke.

3. Karya Buhari yayi game da katange El-Zakzaky – inji ‘Yan Shi’a

Kungiyar Cigaban Musulunci ta Najeriya (IMN) da aka fi sani da ‘Yan Shi’a sun bayyana da cewa ƙaddara da tsirar shugaban kungiyar su, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky, na a hannun shugaba Muhammadu Buhari.

Naija News ta fahimta da cewa shugaba Buhari ya fadawa ‘yan shi’a a ranar Jumma’a da ta gabata da cewa su bar kotu da gabatar da hukunci ga shugabansu.

4. Majalisar Dattijai sun gayawa shugaba Buhari lokacin da zai bayar da Jerin sunan Ministoci

Majalisar Dokoki ta Najeriya sun gargadi shugaba Muhammadu Buhari da bayar da jerin sunayan Ministoci da zasu yi wakilci a shugabanci sa ta ‘Next Level’ kamin ranar Jumm’a ta gaba.

Naija News ta fahimta da cewa Babban rukunin Majalisar Dattijai zasu shiga hutun su ta shekara da shekara kamar yadda suka saba daga ranar Jumma’a 26 ga watan Yuli har zuwa ranar 26 ga watan Satunba.

5. Oyegun ya gargadi Oshiomhole da barin kunyatar da Jam’iyyar APC

Tsohon Ciyaman Tarayyar Jam’iyyar APC, John Odigie Oyegun, ya gargadi Adams Oshiomhole da janyewa daga kunyatar da Jam’iyyar.

Naija News na da sanin cewa a halin yanzu Oshiomhole nada jayayya da Gwamnan Jihar Edo, Godwin Obaseki, akan shugabancin Jam’iyyar APC ta jihar.

6. ‘Yan Kungiyar Biafra sun aika sakon gargadi ga Miyetti Allah

Kungiyar Matasan ‘yan Biafra da ake kira ‘Biafra Nations Youth League’, BNYL ta gargadi Makiyaya Fulani da barin yankin Kudu ko kuma su fuskanci duk abin da ya biyo da baya.

Naija News ta tuna da cewa Miyetti Allah Kautal Hore ta umurci makiyaya Fulani da su kare kansu daga duk wata hari a kuducin kasar.

8. COZA: ‘Yan Sanda sun yi bayani game da bukatar Busola da Timi Dakolo da bayani a ofishinsu

A ranar Asabar da ta wuce, Hukumar ‘Yan Sandan Najeriya sun bayyana da cewa lallai sun samar da takardan bukatar bayani daga bakin Busola da Timi Dakolo.

A ganewar gidan labaran nan tamu, akwai ganewa da cewa ‘yan sandan sun bukaci hakan ne don neman bayani akan matsalar da ke tsakanin matar Timi Dakolo da Faston da ke jagorancin Ikilisiyar COZA.

Ka samu kari da cikakken Labaran Najeriya a shafin NaijaNewsHausa

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Alhamis, 18 ga Watan Yuli, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Alhamis, 18 ga Watan Yuli, 2019

1. Majalisar Dokoki ta amince da gabatar da Tanko Muhammad a matsayin CJN

A ranar Laraba da ta gabata, Majalisar Dattaija ta Najeriya sun gabatar da Tanko Muhammad a matsayin Babban shugabannan Alkalan Kotun Najeriya.

Wannan ya biyo ne bayan shugaba Muhammadu Buhari ya bayar da sunan Tanko ga Majalisar don tabbatar da shi a matsayin CJN.

2. Majalisar Wakilai sunyi barazanar daukan mataki akan Gwamna Obaseki

Majalisar Wakilai ta Najeriya sun bada tsawon kwanaki bakwai ga Gwamna Godwin Obaseki, Gwamnan Jihar Edo don gabatar da wani sabon shela don kiran taron na Majalisar Jihar Edo na 9.

Majalisar Dokokin Tarayyar ta kara da cewa idan gwamnan ya kasa aiwatar da hakan a cikin lokacin da aka tsara, za su iya daukar nauyin ayyukan jihar.

3. Buhari, Lawan, Gbajabiamila sun yi wata taron daki kulle
Shugaba Muhammadu Buhari a ranar Laraba da ta gabata, ya gana da Shugaban Majalisar Dattijai, Ahmed Lawan da Shugaban majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila, a Fadar Shugaban kasa, Abuja.

Naija News Hausa ta fahimta da cewa sun fara taron ne a misalin karfe Uku da rabi ta ranar Laraba.

4. Rukunin Gwamnatin Hukuntawa ta Najeriya ta cika da Cin Hanci da Rashawa – inji CJN Tanko

Tanko Muhammed, Babban alkalin Shari’ar Najeriya, ya bayyana da cewa gwamnatin shari’ar kasar Najeriya ta lalace da cin hanci da rashawa, kuma tana buƙatar taimakon Majalisar Dattijai.

Naija News Hausa ta gane da cewa Tanko ya bayyana wannan zancen ne a lokacin da yake amsa tambayoyin ga Sanatocin kasar lokacin da aka tabbatar da shi a matsayin Babban Alkalin Shari’ar Nijeriya a ranar Laraba.

5. Gwamnatin Jihar Edo ta bayyana sanadiyar Matsaloli da jihar ke fuskanta

Gwamnan Jihar Edo, Gwamna Godwin Obaseki ya zargi jagoran hidimar neman zaben tarayyar Jam’iyyar APC, Adams Oshiomhole tare da kwamitin kadamarwan sa da alhakin matsaloli da jihar ke fuskanta.

Obaseki ya bayyana da cewa jagorancin APC da rashin cikakken binciken ta ga al’amurran ne sanadiyar matsalar da aka samu.

6. Majalisar Dattijai ta yanke shawara game da binciken Sanata Elisha Abbo

Majalisar Dattijai ta Nijeriya a ranar Laraba ta ba da karin lokaci ga kwamiti na musamman da ke bincike kan zargin da ake ga Sanata Elisha Abbo, Sanatan da ke wakilcin Arewacin jihar Adamawa.

Ka tuna a baya da cewa an gano da wata bidiyon da ya mamaye layin yanar gizo, wanda ke dauke da Sanata Abbo inda yake cin mutuncin wata Mata.

7. Kakakin Majalisar Jihar Edo ya mayar da martani ga Majalisar Wakilan Najeriya akan wata mataki

Shugaban majalisar wakilan jihar Edo, Frank Frank Okiye, ya gargadi majalisar wakilai ta Najeriya da kawar da zancen kafa bakin su ga ayyukan Majalisar jihar Edo.

Ka tuna da cewa Majalisar Wakilan Najeriya a baya ta bayar da tsawon kwana bakwai ga Gwamna Godwin Obaseki don gabatar da wani sabon shela akan taron majalisa ta 9 a Edo.

Ka sami kari da cikkaken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com