An Bayyana Lokacin Da ‘Yan Bautan Kasa (NYSC) Zasu Fara Karbar Tallafin N30,000

An tabbatarwa membobin kungiyar ‘yan bautan kasa da aka fi sani da (NYSC), cewa za a sake nazari kan fara basu sabon mafi karancin albashi na N30,000 a kowane wata daga shekarar 2020.

Mista Sunday Dare, Ministan matasa da ci gaban wasanni ya yi wannan sanarwa ne a cikin wata sanarwa da ya fitar daga ofishinsa na watsa labarai a jiya yayin ziyarar Filin ganawa da koyaswa ta hukumar ‘National Youth Service Corps’ da ke a Iyana-Ipaja, jihar Legas.

Ya ce, “Za a sake nazari da shiri domin yadda za a fara biyan mafi karancin albashi na N30,000 na kowace wata ga ‘yan bautan kasa ta NSYC daga shekarar 2020. An riga an yi adadin wannan shirin a cikin kasafin shekara mai zuwa.” 

“A koyaushe ina bayar da shawarar cewa dole ne Najeriya ta sanya hannun jari ga matasa. Mu a ma’aikatar muna sake duba da kokarin samar da cigaban matasan mu dangane da shirye-shirye.”

“Ma’aikatar ta kirkiro wani shiri mai suna DY.NG. Muna son hakan ya kasance shiri ne na watanni biyu wanda zaku gudanar yayin hidimarku, bayan haka zaku sami wasu matakan takaddun shaida. Zai ba ku wannan damar da ta fiye digiri da kuke da ita.”