PDP: Alkawalin Atiku Abubakar a Jihar Zamfara

Alhaji Atiku Abubakar, dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP ya gabatar da cewa zai magance halin ta’addanci a kasar, musanman a Jihar Zamfara.

Muna da sani a Naija News Hausa da cewa, Atiku Abubakar da Jam’iyyar PDP sun gudanar da hidimar yakin neman zaben shugaban kasa a Jihar Zamfara, a ranar Litini 4 ga Watan Fabrairu, 2019.

Dan takaran yayi alkawali ga mutanen Zamfara da cewa zai samar da tsaro da kuma magance ta’addanci a Jihar inda an zabe shi a matsayin shugaban kasan Najeriya.

“Idan babu kwanciyar hankali a kasa ko Jiha, ba yadda manoma ko masana’anta zasu ji dadin samar da ayukan su, har ma ayukan addini ba za ta tafi daidai ba” inji Atiku

Jama’ar Zamfara sun yi murna da wannan kuma fitar su ya bayyana wannan.

Kalli yadda mutanen Jihar Zamfara suka fito ga marabtan Atiku:  

Taron mutane na ta tsuwa da kirarin sunar Alhaji Atiku Abubakar (Sai PDP, Sai Wazirin Adamawa).

Atiku ya kara da alkawarin cewa zai gyara, zai kuma tsarafa Mabulbulin ruwa na Bakolori da ke a Jihar Zamfara.

“ko da shike Noma ita ce aikin ainihin aikin mutanen Zamfara, amma ta’addanci da hare-hare daga ‘yan hari da bindiga ya hana mutane zuwa gonakin su, zamu magance wannan da yardan Allah, sa’anan mu baiwa manoma tallafin kayan aikin gona don samar da ayukan su da kyau” inji shi.

Ya karshe da shawartan jama’ar Zamfara da zaben dan takaran Gwamnan Jihar a Jam’iyyar PDP, Bello Matawalle.

Ga hotunan yadda jama’a suka fito ga hidimar ralin Atiku Abubakar.