Kwamitin Shugabanci da Manyan Sarakunan Arewacin Kasar sun yi ganawa don anfani da Miyagun Kwayoyi da kuma Almajiranci

Buba Marwa, tsohon shugaban sojoji na Jihar Legas ya jagoranci Kwamitin Shawarar Shugaban kasa kan kawar da miyagun kwayoyi, an yi wannan ganuwa ne a Jihar Kaduna, a ranar Laraba 19, ga Watan Disamba, 2018 da wasu shugabannin gargajiya na arewacin kasar da ta kumshi Jiha goma sha 19 hade da Birnin Abuja suka halarta, akan yaki da amfani da miyagun ƙwayoyi a yankin.

Marwa ya fadawa manema labaru bayan wannan ganawa cewa, saboda muhimmancin matsalar, manyan masu ruwa da tsaki kamar sarakunan gargajiya dole ne a hada gwiwa da su ga wannan harka ta yaki da miyagun ƙwayoyi.

Ya kara da cewa an tattauna batun  almajiranci, watau (yaran da suka bar iyayensu don neman ilimi Qur’ani) a  wajen taron.

A fadinsa, kwamitin ta yi kira ga manyan sarakunar don taimaka wa gwamnati a ganin ta magance wannan matsalar.

“Almajirinci hakika wata abu ne da komitin zata kulawa a wannan lokacin, yayin da muke kira ga sarakunan gargajiya don taimakawa a wannan bangaren,” in ji shi.

Tsohon Janar ya ce kwamiti zata ci gaba da saduwa da sarakunan gargajiya na kasar har sai an kawar da miyagun ƙwayoyi ko kuma ganin an rage ta Najeriya.

Marwa ya yi kira ga karfafa Ƙungiyar Harkokin Kiwon Lafiyar Jama’a ta kasa (NDLEA) da Hukumar Kula da Abinci da Kwayoyi ta Duniya don magance miyagun ƙwayoyi a kasar.

A halin yanzu, Matar Mataimakin Shugaban kasa, Dolapo, ta yi kira ga ‘yan Najeriya su dakatar da yin amfani da mugayen kwayoyi saboda mummunan illa da magunan ke da shi ga jikin mu. ta fadi wannan ne a bayanin ta a yayin da suka yi wata ganawa da Ministan Kulawa da Lafiyar Jiki, Frofesa Isaac Adewole a ofishinsa a birnin Abuja a ranar Laraba.

Bincike ya nuna cewa daga cikin mugayen kwayoyi da ake amfani da ita a kasar sune kamar taba, sigari, kaffin,  tramadol da codeine. kwamitin zata yi iyakar kokarin ta don taimakawa wadanda suka bar wannan halin. in ji Dolapo.

Karanta kuma: Abin kaito, Sojojin sama ta Najeriya sun sanar da mutuwar tsohon babban hafsan hafsoshin tsaron kasar, mai suna, Air Chief Marshal, Alex Badeh (retd.).