‘Yan Ta’adda sun kaiwa Oshiomhole da wasu ‘yan Majalisa 14 hari a Jihar Edo

Wasu ‘yan ta’adda masu tada zama tsaye a Jihar Edo a ranar Talata da ta wuce sun hari Mista Seidu Oshiomhole, kani ga Ciyaman na Jam’iyyar APC na Tarayya, Adams Oshiomhole, anan cikin Benin, babban birnin Jihar.

Naija News ta fahimta da cewa ‘yan ta’addan sun kaiwa Mista Seidu hari ne tare da wasu ‘yan majalisa 14 da ke wakilci a Jihar a yayin da suke wata zaman tattaunawa a wata shiyya da ba a bayyana ba.

Bisa ga rahoton manema labaran NAN, sun bayya cewa an fara zaman tattaunawar ne tun tsakar daren ranar Litini da ta wuce, a inda suka gudanar da rantsar da sabbin ‘yan majalisa 9 da kuma nadin Frank Okiye a matsayin kakakin yada yawun majalisar Jihar.

An gabatar da cewa ganawar ‘yan majalisai 9 cikin ‘yan majalisa 24 da jihar ke da ita shine mafarin tanzomar da ‘yan ta’adda suka tayar.

Ko da shike masu bayani sun kara da cewa ba mamaki farmaki da harin ya kunshi matsalar da ke tsakanin gwamnan Jihar Mista Godwin Obaseki da tsohon gwamnan jihar, Adams Oshiomhole.

Mun ruwaito a Naija News Hausa cewa Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje ya gabatar da karatun kyauta a Jihar Kano ga ‘yan Firamare da Sakandare don magance halin roko da yawace-yawace a Jihar.