Kalli kyakyawan hotunan yaran mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo

Naija News ta gano da waddanan kyakyawan hotun diyan mataimakin shugaban kasar Najeriya, Yemi Osinbajo a layin yanar gizo, a yayin da hirar kyakyawan hotunan yaran ya mamaye layin yanar gizon nishadi.

Inda ka diba da kyau kaga namiji daga cikin su mai suna Damilola, ya ci kamannin baban su Osinbajo, ‘yan matan kuma guda da suna Kiki, dayan kuma da suna Fiyin.

Ka tuna mun rabas a layin labarai a baya yadda Osinbajo ya yabawa matarsa Dolapo da godiya don goyon bayan da ta bashi a zaman mataimakin shugaban kasa da kuma zama macce mai adalci da hali na gari.

Kalli hotunan yaran a kasa; 

Kalli Sakon Mataimakin shugaban kasa, Osinbajo ga Matarsa Dolapo

Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo ya aika wa matar sa, Dola wata kyakyawar sakon so da nuna godiya.

Ka tuna cewa a ranar jiya Laraba, 30 ga watan Mayu 2019, An rantsar da Shugaba Muhammadu Buhari da mataimakin sa Yemi Osinbajo ga shugabancin kasar Najeriya a karo ta biyu ga mulkin farar fula.

Ko da shike bayan hidimar rantsarwan, Buhari da wasu manya da tsohin shugbanan Najeriya ta da sun kaurace ga bayyana a hidimar Liyafa da aka shirya don murna da nasarar Buhari da kuma Gwamnonin kasar da suka ci nasara ga zaben 2019.

A hakan ne Mataimakin shugaba Buhari, Osinbajo ya aika wa matarsa sako, inda ya nuna mata godiya da irin goyon bayan ta a shekaru hudu da suka shige da suke jagoranci kasar Najeriya.

Ko da shike Naija News Hausa na da sanin cewa aika sakon soyaya daga miji zuwa matarsa a fili yafi yaduwa ne tsakanin matasan zamani, amma abin da armashi a yayin da aka ga Osinbajo da bayyana yin hakan da matarsa.

Yemi Osinbajo ya rabar a yau da wata kyakyawar hoto da ke dauke da shi da Dolapo matarsa, a layin yanar gizo.

“Masoyiya na Dolapo, Na gode maki da shekarun baya da suka shige. Na kuma gode maki da goyon baya musanman ga shekaru hudu da suka gabata, ke ce dutsen jingina ta. Tare da ke kusa da ni, Ina a shirye don wakilci a shekaru hudu ta gaba a cikin wannan sabon shugabanci tamu” inji Osinbajo.

Kalli sakon a kasa kamar yadda ya aika a layin yanar gizon nishadarwa;

KARANTA WANNAN KUMA; Kalli Tsohin Hotunan Buhari da Matarsa Aisha da baka taba gani ba