Majalisar Dattijai Ba za ta Zartar da Dokar Kalaman Kiyayya Ba – Shugaban Majalisa

Shugaban majalisar dattijai ta Najeriya, Ahmed Lawan ya ce zauren majalisun dokokin kasar ba za su zartar da dokar yada kalaman kiyayya ba.

Wannan zancen ya biyo bayan koke-koke da zanga-zangar da aka yi kan kudirin kalaman kiyayya wadda Sanata Aliyu Sabi Abdullahi, mai wakilcin APC a jihar Neja ya gabatar.

Ku tuna, kamar yadda Naija News Hausa ta ruwaito a baya cewa Sanata Enyinnaya Abaribe ya ce, ‘Da Lai Mohammed ya mutu ko idan da a ce an kafa dokar kisa kan kalamun kiyayya tun wa’adin Jonathan’.

Abaribe ya mayar da martani game da dokar mutuwa ta hanyar ratayewa wanda ke a kunshe cikin wata sabuwar tsarin da Majalisar Dattawa ke kokarin kafawa.

Abaribe a cikin yada yawunsa ya haɗu da wasu ‘yan Najeriyar don ƙin amincewa da dokar.

Yace; “Idan da an riga an zartar da irin wannan dokar a lokacin mulkin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, da Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed a yanzu ya mutu ko.”

Da Lai Mohammed Ya Mutu ko Idan Da A Ce an Kafa Dokar Kisa kan Kalamun Kiyayya tun Wa’adin Jonathan – Abaribe Ya Gayawa Lai Mohammed

Sanata Enyinnaya Abaribe ya mayar da martani game da dokar mutuwa ta hanyar rataye wanda ke a kunshe cikin wata sabuwar tsarin da Majalisar Dattawa ke kokarin kafawa.

Ka tuna kamar yadda Naija News Hausa ta ruwaito a baya cewa Jam’iyyar PDP Sun Yi Allah Wadai da Dokar Kisa ga Masu Yada kalaman Kiyayya da Majalisar ta Shirya da kafawa.

Abaribe a cikin yada yawunsa ya haɗu da wasu ‘yan Najeriyar don ƙin amincewa da dokar.

Yace; Idan da an riga an zartar da irin wannan dokar a lokacin mulkin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, da Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed a yanzu ya mutu ko.

Abaribe ya ce Lai Mohammed ya furta kalamai masu yawa da ba za a iya bayyanawa ba kan Jonathan a lokacin wa’adinsa, ya kara da cewa ba a hanna shi hakkinsa na bayyana ra’ayin nasa ba a lokacin.

A lokacin da aka nemi Abaribe da bayani game da batun dokar a gidan talabijin na TV Channels, Sanatan ya amsa da cewa:

“Ku bari in tunar da ku da karanta muku wasu zance domin bada karin haske a wannan zancen.”

“Bai kamata a yi dauriya da gwamnatin da ba ta shirye don daukar nauyin al’ummar ta ba. Gwamnati kasa ke da hakin kare ‘yan kasarta amma ba kafa baki ba ga neman zargi. Yanzu, wannan Shugaban yariga ya bayyana a fili a tsarin sa ga duniya da cewa ya kasa ga shugabanci. A cikin tarihin shugabanci, ba a taba samun gwamnati marasa manufa da hanayar ci gaba ba kamar irin wannan gwamnatin. Wannan gwamnatin tana tafiyar da ƙasar gabaɗaya tare da hadin shugabannai marasa himma da kuma cikke da cin hanci da rashawa. Hakikan wannan gwamnatin bata da wata alaka da kabilanci, amma kawai cikke da shugabannai da basu cancanta ba ga tsarin mulki.”

Waɗannan sune kalmomin Lai Mohammed, Ministan Labarai tsakanin shekarar 2012 da 2014.

Ina tabbatar maku da cewa a yau duk wanda ya faɗi irin wannan kalamai da an riga an dakile shi da zargin kalamun kiyayya da bacin shugabancin kasa.

Zasu ce ka baci shugaban kasa da kuma raina shi, a hakan kuma a daure ka da jefa ka a kurkuku. Idan da ace an riga an kafa dokar kisa ta hanyar ratayewa ga masu kalaman kiyayya tun a wa’adin jonathan, shin da Lai Mohammed da wadannan kalaman da ya furta, kuna ganin da zai saura da rai a yau?

Wannan shirin ba komai bane illa rashin juriya da kuma neman tsananta wa rayuwa al’umar kasa. Mutumin da ya furta irin wadannan kalamu a baya sai ga shi a yau da kafa dokar da zai hana wasu da yin hakan.

“Ya dace kowane dan Najeriya ya farka daga barci, ya kuma gane da cewa wannan gwamnatin bata da kirki ko wata manufa ta kwarai ga al’ummarta” inji Abaribe.