Wani Matashi ya ci karo da Gidan Jaru bayan da yayi wa ‘Yar Shekara 12 Ciki

Kotun Kara ta Jihar Katsina ta saka wani mutumi mai shekaru 25 ga Kurku da zargin yiwa diyar Makwabcin sa
mai shekaru goma shabiyu ciki.
Naija News Hausa ta samu rahoto da cewa Hussaini Muntari, mutumin da yayi wa yarinyar ciki, mazauni ne na
kauyan Inwala Jangele da ke a karamar hukumar Batagarawa ta Jihar Katsina.

An bayyana da saka matashin a gidan jaru zar sai ga ranar 30 ga watan Afrilu ta shekarar 2019 kamin a ci
gaba da karar a jagorancin babban alkalin Kotun kara ta Jihar Katsina, Hajiya Fadila Dikko.

Naija News Hausa ta gane bisa bayanin ‘Yan Sanda da cewa Muntari, mutumin da ya aiwatar da halin banzan
makwabci ne ga Uban Yarinyar, Mohammed Sani.

Bayan da Malam Sani ya gane da abin da Muntari ya aikata, sai yayi gaugawa da kai karar ga Hedkwatan
jami’an tsaron da ke a yankin Batagarawa.
‘Yan Sanda sun bayyana da cewa Malam Sani bai gane da abin da ke gudana tsakanin Muntari da diyar shi ba
sai har ranar 22 ga watan Janairu 2019 da ya gane da cewa diyar nasa na dauke da juna biyu sakamakon jima’i
da Muntari ke yi da ita.

An kara bayar da cewa Yarinyar da aka yi wa cikin ta bada tabbaci da cewa lallai Muntari ne yayi mata
cikin. “Cikin da ni ke dauke da shi na Muntari ne. Yayi Jima’i da ni sau da dama a cikin dakin shi” inji
Yarinyar.

Insfekta Sani Ado, shugaban Jami’an ‘Yan Sandan yankin, da ke jagorancin karar ya bayyana ga Kotun kara a
ranar Talata da cewa suna kan bincike game da karar.
Ko da shike a halin yanzu, an saka Muntari a gidan jaru har sai ranar da Alkali Dikko ta gabatar ya kai ga
isowa.
Mun ruwaito a baya a Naija News Hausa da cewa Hakilu Saidu, wani manomi mai shekaru 30 ya kashe diyar agolan makwabcin sa da ke da shekaru hudu 4 a Jihar Katsina.

Tau ga wata: Maganin Bindiga ya karye a yayin da wani ya rasa ransa garin gwada karfin magani

Abubakar Hamisu, wani mai shekaru 40 a Jihar Katsina ya mutu sakamakon gwada karfin maganin bindiga.

Kamar yadda aka bayar bisa labari, abin ya faru ne a ranar 16 ga watan Maris ta shekarar 2019 a karamar hukumar Jibia ta Jihar Katsina.

An bayyana ne da cewa Hamisu da abokannan sa na gwajin karfin wata maganin bindiga ne da suka samu, a yayin gwajin ne aka harbi Abubakar Hamisu har ga mutuwa.

Bincike ta nuna da cewa Rabe Salisu, abokin Hamisu, shi ma ya samu raunukan harsasun bindiga a yayin da suke gwada kyan maganin da harsasu.

Hamisu da Salisu na daga kauyen Kwari ne a karamar hukumar Jibia, Jihar Katsina.

‘Yan Sandan yankin sun gabatar da cewa an kame Mani Mohammed, mutumin da ya harbe Hamisu. Ko da shike an bayyana da cewa a fadin sa, ba wai ya so hakan bane, da cewa bindigar ta tashi ne a yayin da yake kokarin anshe bindigar daga hannun Hamisu da Salisu a lokacin da suke kokarin gwada maganin bindigar a jikin su.

Mohammed na da shekaru 43, kuma aboki ne da kuma mazaunin kauye guda da Hamisu da ya mutu da kuma Salisu abokin su da ya samu raunukar bindiga.

“Bindigar ta tashi ne a yayin da nike kokarin karban bindigar daga hanun Marigayi Hamisu da kuma hannun Salisu”

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa wata Macc a Jihar Bauchi, ta tsage cikin ta da reza don zafin na’uda

Ko da shike an kai Hamisu da Salisu a Asibitin Janara ta Jibia, amma abin takaici, Hamisu ya mutu a yayin da ake basu kulawa.

A halin yanzu, an bayar da cewa an riga anyi karar Mani a gaban Babban Kotun kara ta Jihar Katsina a ranar Talata da ta gabata don kadamar da kisan kai.

Alkalin da ke karar, Hajiya Fadila Dikko, ta daga karar zuwa ranar 7 ga watan Mayu ta shekarar 2019, sa’anan a ci gaba da karar daga inda aka tsaya.

Ofisan Jami’an ‘Yan Sanda da ke jagorancin karar, Sajan Lawal Bello, ya bayyana ga kotu da cewa zasu ci gaba da bincike akan karar.