An tare Mataimakin Shugaban Kasa, Yemi Osinbajo da Zanga-Zanga

Da safiyar yau Talata, 7 ga Watan Mayu 2019, wasu Masu zanga-zanga sun katange mataimakin shugaban kasar Najeriya, Farfesa Yemi Osinbajo a babban hanyar Umaru Musa Yar’Adua ta birnin Abuja.

Wannan ya faru ne a kauyan Goza a yayin da Mataimakin shugaban kasa ke kokarin bin hanyar garin zuwa filin jirgin sama don wata tafiya.

Naija News Hausa ta gane da cewa mazaunan kauyan, watau Gwarawa (Gbagyi) sun keta manyan hanyoyin ne da ta bi zuwa filin jirgin sama ta birnin Abuja don nuna rashin amincewar su akan tawaye da muzuntasu da Sojoji suka yi na maye Filayen su da suka gada.

Duk da haka, jami’an tsaron mataimakin shugaban kasa sun kasa cimma nasarar da dakatar da mutanen kauyan daga tare hanyar, har sai da suka tilasta Osinbajo ya sauka daga motarsa.