Kalli hotunan Auren Matan Tsohon Gwamnan Taraba da ya Mutu da wani Matashi

Bayan shekaru biyu da mutuwar Danbaba Suntai, tsohon Gwamnan Jihar Taraba, matarsa Hauwa Suntai ta sake shiga dankon soyaya da Auren wani kyakyawan mutumi.

Bisa rahotannai da Naija News Hausa ta gana da shi, an bayyana da cewa Hauwa ta sake kula dankon so ne da wani kyakyawan Saurayi mai suna Haliru Saad Malami, da aka fi sani da suna, San Turakin Malumfashi, mai jagoran kamfanin ITBAN Global Resources LTD.

Ka tuna mun sanar a Naija News Hausa a baya da cewa sabon Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni ya auri diyar Ibrahim Gaidam, tsohon Gwamnan Jihar.

Bisa bincike da sanarwa, Malama Hauwa da aka sani da fiye da shekaru 50 ta auri dan saurayin ne mai kankani shekaru 30.

Rahoto ya bayyana da cewa Haliru dan uwa ne ga Turai Yar’Adua, matan marigayi, tsohon shugaban kasar Najeriya, Umaru Yar’Adua.

Kalli Hotuna a kasa;

Ka tuna da cewa a watan Aktoba na shekara ta 2012 da ya gabata, marigayi Gwamna Suntai yayi wata hadarin jirgin sama a Yola, aka kuma tafi da shi a gurguje zuwa kasar Turai, watau kasar Jameni don bashi kulawa.

A baya dai ya mutu ranar 28 ga watan Yuni, a shekara ta 2017, a kasar Turai, nan birnin Houston, Texas, ta hadaddiyar kasar Amurka (United States).