Sabuwar Labari: Kotu ta Kori dan takarar gwamnan jihar Bayelsa na APC

Rahoto da ke isa ga Naija News Hausa a wannan lokaci ya bayyana da cewa babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, a yau Talata, 12 ga Watan Nuwamba ta hana mataimakin dan takarar gwamna a jihar Bayelsa daga jam’iyyar All Progressives Congress, Biobarakuma Degi, shiga tseren takara a ranar Asabar mai zuwa, 16 ga Nuwamba, 2019, a zaben gwamna a jihar.

Hakan ya bayyana ne daga bakin Mai shari’a Inyang Ekwo, a yayin da yake gabatar da hukunci a karar wacce aka yi da lambar shaida FHC / ABJ / CS / 1101/2019, wadda jam’iyyar Peoples Democratic Party da sauran ‘yan jam’iyu suka kafa gabatar.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa an kona sakatariyar Jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), da ke Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

A cewar rahoton da wakilinmu ya tattara, mutane da ba a san ko su wanene ba amma da ake zargi da zaman ‘yan tada zama tsaye wajen hidimar siyasa, sun kutsa cikin sakatariyar jam’iyyar SDP da sanyin safiyar ranar Litinin da ta wuce, suka kuwa kone ofishin kurmus da wuta.

Al’amarin ya faru ne ‘yan kwanaki kadan ga hidimar zaben kujerar gwamnan jihar, wadda hukumar INEC ta sanar da gudana a ranar 16 ga Nuwamba a jihar.

2019: Kada ku gabatar da sakamakon zaben Jihar Bauchi, Kotu ta gayawa INEC

Kotun koli ta Abuja, babban birnin Tarayya ta hana Hukumar gudanar da hidimar zaben kasa (INEC) da gabatar da sakamakon zaben Jihar Bauchi.

Kotun ta umurci hukumar INEC da dakatar da hidimar zaben Jihar Bauchi, musanman gabatar da rahoton zaben da aka yi a ranar  9 ga watan Maris da ya gabata a Jihar.

An gabatar ne da hakan ga hukumar INEC a jagorancin Alkali, Inyang Ekwo, a ranar Talata (yau) akan wata kara da ake akan Jam’iyyar APC da Gwamnan Jihar, Mohammed Abubakar wadda ya bukaci hukumar INEC da dakatar da sanar da sakamakon kuri’un zaben Jihar, musanman, zaben karamar hukumar Tafawa Balewa.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa hukumar INEC ta yi barazanar cewa Kotu ba ta isa ta hana su kadamar da zabe ba a Jihar Adamawa.

Alkali Inyang ya fada da cewa wanda ke kan shugabanci zai dakata daga shugabancin sa daidai bayan da aka gama karar da ke gaban kotun.