Boko Haram: ISWAP sun Kashe Sojojin Najeriya Biyar a Borno

Naija News Hausa ta karbi rahoton cewa ‘Yan kungiyar Islamic State West Africa County (ISWAP) sun kashe a kalla sojojin Najeriya hudu da wani mayaki a cikin jihar Borno.

A cewar majiyoyin tsaro da suka yi magana da kamfanin dillancin labarai na AFP ranar Lahadi, ya bayyana da cewa fadar ya barke ne a yammacin Asabar a yayin da sojoji suka yi wa wani ayarin ‘yan kungiyar ISWAP – wanda suka tashi daga kungiyar Boko Haram – kusa da kauyen Jakana, mai nisan kilomita 42 daga Maiduguri babban birnin jihar.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa rundunar Sojojin Sama ta Najeriya (NAF) sun rushe wata rukunin ‘yan Boko Haram da ke a Boboshe, a karkarar da Dajin Sambisa ta ke a nan Borno.

An bayyana da cewa wannan wajen da Sojojin suka rusa da Bam wajen hadin taro ne ga ‘yan ta’addan Boko Haram.

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 21 ga Watan Oktoba, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 21 ga Watan Oktoba, 2019

1. Shugaba Buhari Ya Bar Najeriya Zuwa kasar Rasha

Shugaban kasa Muhammadu Buhari a yau Litini zai bar Najeriya don halartar taron kwanaki uku a Rasha da Afirka a nan Sochi, Rasha.

Naija News ta fahimta da cewa taron kolin za a fara shi ne a ranar 23 ga Oktoba zuwa 25 ga Oktoba 2019.

2. Boko Haram: Mutane Biyar sun Mutu a Munsayar wuta tsakanin ISWAP da Sojojin Najeriya a Borno

Wakilan kungiyar Islamic State West Africa County (ISWAP) sun kashe a kalla sojojin Najeriya hudu da wani mayaki a cikin jihar Borno.

A cewar majiyoyin tsaro da suka yi magana da kamfanin dillancin labarai na AFP ranar Lahadi, ya bayyana da cewa fadar ya barke ne a yammacin Asabar a yayin da sojoji suka yi wa wani ayarin ‘yan kungiyar ISWAP – wanda suka tashi daga kungiyar Boko Haram – kusa da kauyen Jakana, mai nisan kilomita 42 daga Maiduguri babban birnin jihar.

3. An samu Kama Zakin da ya Tsere a Kano

Daraktan kula da gidan namun dajin na Kano, Alhaji Usman Gwadabe ya sanar da cewa wata kungiyar kwararru sun ci nasara da kama wani zakin da ya tsere daga gidan dabbobi a jihar Kano.

Naija News ya gane da cewa mazauna yankin Kano sun kwana ne cikin fargaba bayan da aka sami labarin tseretarwar zakin daga Gidan Namun Dajin a daren jiya, kamin aka sake kama.

4. Biafra: Maman Nnamdi Kanu ta rasu

Malama Ugoeze Sally Nnenne Okwu-Kanu, mahaifiyar shugaban kungiyar ‘yan asalin Biafra (IPOB), Nnamdi Kanu ta mutu.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa mahaifiyar Kanu ta mutu a ranar 30 ga Agusta a Jamus, shugaban IPOB din ya ba da sanarwar a wani faifan bidiyo da Naija News ta ci karo da ita.

5. Dino Melaye ya mayarda martani ga Tsige Mataimakin Gwamnan Kogi

Sanata Dino Melaye, Sanatan da ke wakilcin APC Yammacin Kogi yayi Allah wadai da tsige mataimakin gwamnan jihar Kogi, Simon Achuba.

Naija News ta ruwaito cewa a ranar Jumma’a da ta gabata ne majalisar dokokin jihar Kogi ta tsige Achuba

6. Dalilin da Yasa Ba za a Raba Buhari da Mamman Daura Ba

Dangin Daura sun dage da cewa ba zai yiwuwa ba a raba Shugaba Muhammadu Buhari da dangin ​​sa, Mamman Daura ba.

Ka tuna da cewa matar Buhari, Aisha da kuma dangin Mamman Daura a kwanan nan sun shiga fada ga rigingimun da jama’a suka gana da shi a layin yanar gizo, anan Fadar Shugaban kasa.

7. Osinbajo Bai Amfani da Sa na Mataimakin Shugaban Kasa ba a hanyar da bai dace ba – Junaid Moh’d

Dan majalisa na jamhuriya ta biyu, Junaid Mohammed, ya ce mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo a kan matsayin sa bai yi furuci ko dauki matakin da zai sanya Najeriya a cikin rikici ba a lokacin da yake rike da mukamin Shugaban kasa.

Naija News ta ruwaito a baya da cewa Osinbajo ya maye gurbin matsayin mukaddashin shugaban kasa a lokacin Shugaba Muhammadu Buhari ya tafi kasar Ingila don hutu da kuka da lafiyar jikinsa.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 11 ga Watan Yuni, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 11 ga Watan Yuni, 2019

1. APC, Gwamnoni da ‘yan Majalisa sun bada goyon baya ga Lawan da Gbajabiamila

Manyan jigo da shugabannan Jam’iyyar APC, Gwamnonin Jiha da ‘yan Majalisar Dattijai da ke wakilci a Jam’iyyar APC sun bada goyon baya ga Ahmed Lawan da Femi Gbajabiamila a zaman shugaban Sanatocin Najeriya da kakakin gidan Majalisa.

Haka kazalika aka bayyana goyon baya ga Sanata Ovie Omo-Agege da Idris Wase a matsayin mataimakin shugaban sanatoci da mataimakin kakakin yada yawun majalisa.

2. Shugaba Buhari ya rattaba hannu ga bil na hidimar ranar Dimokradiyya, 12 ga Yuni

Shugaba Muhammadu Buhari ya rattaba hannu ga bada hutu ranar 12 ga watan Yuni 2019 don hidimar ranar Dimokradiyya.

Naija News Hausa ta gane da rahoton ne bisa sanarwa da aka bayar daga bakin Sanata Ita Enang, mai wakilcin shugaba Buhari a al’amarin gidan Majalisar Dattijai.

3. Kotu ta kafa baki ga hidimar karar Atiku da Buhari

Kotun Neman Yanci da ke tafiyar da karar Atiku Abubakar da Shugaba Muhammadu Buhari ga zancen zaben 2019, a birnin Tarayya, Abuja, a ranar Litini da ta gabata, sun tada zancen karar.

A yayin da ake kan zancen, kotun ta janye kara ta Uku da Jam’iyyar Coalition for Change suka gabatar a baya akan hidimar zaben watan Fabrairu 2019.

4. INEC ta gabatar da lokacin da zata dauki mataki akan Okorocha

Hukumar Gudanar da Hidimar Zaben kasar Najeriya (INEC) sun bayyana da cewa a yau Talata, zata kara bincike da binbini akan ko watakila zata iya bayar da takardan yancin wakilci ga Rochas Okorocha.

Naija News ta fahimta da cewa za a gabatar da sabin ‘yan Majalisar Dattijai a yau, wanda ya nuna da cewa Okorocha ba zai samu damu kasancewa a ciki ba, don ba a bayar da takardan shiga Majalisar ba a gareshi.

5. Gwamna Sanwo-Olu ya nada Alogba a matsayin babban Alkali a Legas

Gwamnan Jihar Legas, Mista Babajide Sanwo-Olu ya gabatar da Alkali Kazeem Alogba a matsayin babban alkali da zai wakilci Kotun Koli ta Jihar Legas.

Naija News ta samu ganewa da hakan ne bisa wata sanarwa da aka bayar bayan da Gwamna Sanwo-Olu ya sanya Alkalin a ranar Litini da ta wuce.

6. Adebo Ogundoyin ya lashe kujerar kakakin yada yawun Majalisa a Jihar Oyo

Dan shekara 32 ga haifuwa, Mista Adebo Ogundoyin ya ci nasara da lashe zaben zama kakakin yada yawun gidan Majalisar Jihar Oyo.

A fahimtar gidan labaran nan tamu, Ogundoyin ya karshe karatun sa ne daga makarantar Jami’a babba ta Babcock University, haka kuwa ya dace da zama kakakin yada yawun Majalisar Jihar ba tare da jayayya ba.

7. Garba ya maye gurbin Bulkachuwa ga karar neman yanaci tsakanin Buhari da Atiku

Alkali Mohammed L. Garba ya maye gurbin tsohon jagoran Kotun neman yanci, Zainab Bulkachuwa, a hidimar karar jayayya da neman yanci tsakannin shugaba Muhammadu Buhari da Alhaji Atiku Abubakar akan zaben watan Fabrairu.

Naija News na da sanin cewa a da, Mista Garba ne ke jagorancin kotun kara da ke a wata yankin Jihar Legas.

8. Rundunar Sojoji sun kashe ‘yan Boko Haram 9

Rundunar Sojojin Najeriya sun gabatar da cewa sun kashe mutane tara da aka gane da kasancewa cikin rukunin ‘yan ta’addan (ISWAP).

Bisa wata bayani da aka bayar daga bakin Col. Sagir Musa, Daraktan Rundunar Sojoji a lamarin sadar da labarai, ya bayyana da cewa sojoji sun ci nasara ga kashe mutane 9 da ke da hakin ta’addanci a kasar.

Ka samu kari da cikkaken Labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com

Boko Haram sun kashe Sojoji 5, Talatin kuma sun bata a Jihar Borno

Kimanin Sojojin Najeriya biyar suka rasa rayukan su a wata sabuwar ganawar wuta da ‘yan Boko Haram a Jihar Borno.

Naija News Hausa ta karbi rahoto a yau Litini da cewa Rundunar Sojojin kasa ta Najeriya sun yi wata ganawar wuta da ‘yan ta’adda a ranar Jumma’a da ta gabata, inda ‘yan ta’addan Boko Haram suka samu cin nasara da kashe sojoji biyar daga cikin sojojin Najeriya a nan take.

Bisa bayanin wani da bai bayar da sunan sa ba ga manema labarai, ya gabatar da cewa Rundunar Sojojin kasar sun samu gano da gawakin sojoji biyar da aka kashe. “An gano gawakin Sojoji biyar da suka mutu amma har yanzu ba a samu ganin kimanin sojoji Talatin ba da suka halarci ganawar wutan”

Ya kara da cewa har wa yau Rundunar sojojin na cikin bincike da neman sojoji kimanin 30 da suka bata a harin wanda ba wanda ya san inda suke, inji shi.

Naija News Hausa ta samu sanin cewa ‘yan ta’addan da aka fi sanin sunar kungiyan su da ‘ISWAP’ ne suka hari rukunin Rundunar Sojojin kasa ta Najeriya a ranar Jumma’a da ta wuce a rukunin su da ke a shiyar Mararrabar Kimba, mai Kilomita 135 daga garin Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Mun ruwaito a baya a shafin Labaran Hausa ta gidan yada labaran mu, da cewa Gwamnatin Jihar Kaduna ta kafa Dokar ƙuntatawa na tsawon awowi 24 a Jihar.

An gabatar ne da dokar ƙuntatawa a ranar 26 ga watan Afrilu ta shekarar 2019 a layin yanar gizon nishadarwa ta Facebook, kamar yadda Samuel Aruwan, Kakakin yada yawun Gwamnan Kaduna Nasir El-Rufai, ya rabar.