Farmaki: An kashe mutane Uku, wasu kuma sun yi raunuka a yankin Jema, Jihar Kaduna

An sami rahoto da cewa wasu ‘yan hari da ba a san dasu ba, sun fada wa yankin Jema dake Jihar Kaduna

Wannan harin ya faru ne kamar yadda muka sami rahoto a ranar Asabar da ta gabata, a misalin karfe 7:30 na yamma.

Farmakin ya faru ne tsakankanin gadan Asso da Tanda a wani kauyen Gwong da ke yankin Jema’a, Jihar Kaduna.

Ciyaman na yankin, Mista Peter Averik ya tabbatas da farmakin ga manema labarai a yau, Mista Peter ya ce “Harin ya abku ne daidai misalin karfe 7:30 na maraice a yayin da maharan suka fado wa mazaunan kauyen da ke akan tafiyarsu tsakanin gadan Asso da gadan Tanda.

“An gaya mani ne cewa maharan sun harbi mutanen ne da tsoron kada su tona su a yayin da suka hange su” in ji Mista Peter.

“Mutum guda ya mutu a nan wajen, biyun kuma an kai su a asibitin da ke Fadan Kagoma inda ake nuna masu kulawa, a nan kuwa asibitin ne guda kuma ya mutu sanadiyar raunuka da ya samu” in ji shi.

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa Wasu yan hari sun kai farmaki har sun kashe mutane 14, sun kuma yiwa mutane 17 rauni a wata kauye mai suna Ungwan Paa-Gwandara a yankin Jema’a na Jihar Kaduna.

Mista Peter Averik ya kara da cewa na ukun ya mutu ne da safiyar Litini, watau a yau in da aka same shi bakin daji kwance ba rai a wata kauyen Wazo, kamin a kai kauyen Aso.

A halin yanzu an rigaya an yi shiri don kai wadanda suka sami raunuka a asibitin musanman ta Barau Diko, Jihar Kaduna, kamin dada akai su babban asibin Patrick da ke Kanfanchan.

Mista Peter ya karshe da cewa an riga an zuba jami’an tsaro a wajen da wannan farmakin ya abku don tabbatar da tsaro da kuma zaman lafiyar mutanen yankin da tattalin arzikin su.

 

Karanta kuma: ‘Yan Sandan Jihar Neja sun kame Habiba Usman da zargin cewa tana da sani kuma itace sanadiyar sace ta da barayi suka yi – in ji Yan Sanda.

 

 

Mutane 14 sun Mutu, 17 da rauni a wata hari a Jihar Kaduna

Yan Hari sun kai farmaki a garin Ungwan Paa-Gwandara

Wasu yan hari sun kai farmaki da har sun kashe mutane 14, sun kuma yiwa mutane 17 rauni a daren Lahadi da ta gabata, a wata kauye, mai suna Ungwan Paa-Gwandara a yankin Jema’a na Jihar Kaduna.

Mista Joshua Paul, wani mazaunin yankin ya bayyana ga manema labarai a Kafanchan a yau cewa wadanda aka kashe a same su a wata bikin aure daidai karfe takwas (8) na yamma.

“Mutane tara (9) suka rasa rayukan su a lokacin harin, sa annan mutum biyar (5) suka mutu a wannan safiya a Kafanchan General Hospital.

“da sauran wasu sha bakwai (17) hade da yan yara guda shida da suka ji mummunar ciwo da raunuka. har yanzu suna cikin mummunan yanayin,” in ji shi.

Har ila yau, Malama Victoria Martins, da ita ma ta fada ga wannan mugum hari, bayan an kula da ita a asibitin a garin Kafanchan, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Najeriya cewa, Mata da yara ne suka fi samun rauni a wannan harin.

Ciyaman yankin Jema’a, Mr Peter Averik, ya bayyana akan wayar salula da cewa har yanzu bai sami cikakken bayani game da wannan lamarin ba, amma an riga an tsara ‘yan sanda zuwa ga yankin da wannan mugum harin ya faru.

The police was yet to react to the incident at the time of filing this report. However a source said the command would issue a statement later.

Har yanzu ‘yan sanda ba su amsa ga abin da ya faru ba a lokacin bada rahoton nan. Duk da haka wata majiya ta ce za a ba da sanarwa daga nan baya.