Kannywood: Jama’a ga Naku! Sabuwar Fim ta Fito mai liki ‘Garba Mai Walda’ a NorthFlix

Kamfanin Yada Fina-finan Hausa na sanar da fitar da sabuwar shiri mai liki ‘GARBA MAI WALDA’

Takaitacen Fim din:

Garba Mai Walda labarin wani Magidanci ne mai tsananci hali, wanda ta zan mai da wuya ga iya gamsar da kowa, harma Iyalinsa. Ba wanda ya taba jin dadin alaka dashi. Matarsa kullum sai kuka, Uwarsa kuma kullum sai kaito, mazauna unguwa kuma sai baƙin ciki da shi kullum.

Yadda zaka sami kallon Fim din Garba Mai Walda:

Idan kana da muradin kallon ‘Garba Mai Walda’ abu mai sauki ne, kawai ka nemi Manhajar Northflix a shafin Google PlayStore da ke a wayar ka, sai ka saukar da Manhajar a wayan ka, anan sai ka nemi ‘Garba Mai Walda,‘ saura sai labari.

KARANTA WANNAN KUMA; Anyiwa ‘yan wasan Kwallon Niger Tonadoes alkawarin naira dubu N500,000 a kowane Gwal da suka ci Kano Pillars a gasar cin kofin Aiteo ta shekarar 2019.

Kannywood: Northflix ta sanar da mayar da Fim din SAREENA kan Manhajar

Kanfanin da ke yada fina-finan Hausa akan Manhajar, Northflix na sanar da mayar da fim din SAREENA da a baya aka cire daga jerin fina-finan da ke kan Manhajar don wasu dalilai.

Karanta sanarwan a kasa;

A madadin hukumar gudanarwar Northflix da kuma furodusa Bashir Maishadda, muna farin cikin sanar sa ku cewa yanzu haka mun mayar da fim din SAREENA kan Manhajar Northflix kamar yadda muka yi muku alkawari.

KARANTA WANNAN KUMA; Dalilin da yasa wata Mata ta zuba wa Mijinta Ruwan Zafi ga Azakarin sa

Kannywood: Anyaka wa fitacen jarumi dan Shirin Fim kafa don Tsanancin Ciwon Daji

Abin takaici, Naija News Hausa ta samu sanin cewa anyankewa fitatcen Jarumin kannywood, Sani Idris MODA kafa sanadiyyar matsanacin ciwon daji da yake fama dashi na tsawon lokatai.

Sanarwan ya bayyana ne a layin yanar gizon nishadi ta Twitter wadda Musa Kutama [@kutamamuhammad] ya bayar.

Ga sakon a kasa karmar haka;

Innalillahi Wainna ilaihiraju’un anyankewa fitatcen Jarumin kannywood Sani Idris MODA kafa sanadiyyar matsanacin ciwon daji da yake Fama dashi.
Majiyar mu ta bayyana mana cewa anyi aikin cikin nasara yanzu haka yana kara samun sauki.
Muna rokon Allah ya kara masa lafiya #Ameen

Kalli Bidiyon lokacin da Ali Nuhu ya ziyarceshi a kan gadon asibiti;

https://www.youtube.com/watch?v=OUSDMdqej7I

Ka tuna da cewa Naija News Hausa ta ruwaito a baya cewa Ali ArtWork da aka fi sani da ‘Madagwal,’ Na cikin Mawuyacin yanayin rashin lafiya.

Ko da shike dai a baya an iya gane da cewa sauki ya samu ga shahararran.

Kannywood: Kalli Jerin sabbin Fina-Finan Hausa da za a Fitar ba da dadewa ba

Kamfanin Haskar da fim na Arewa, NorthFlix na batun haska da fitar da sabbin Fina-finai da dama ba da jimawa ba.

Ka riga abokannai da ‘yan uwa saurin samun wadanan Fim ta saukar da Manhajar NorthFlix daga GooglePlay don samun sabbin Fina-Finan Hausa a koyaushe.

KALLI WANNAN SABON SHIRIN;

 

Kannywood: Kalli wannan Sabon Fim mai liki (Fitila)

Masoya kallon fina-finan Hausa tau yau ga taku! Naija News Hausa ta gano maku da sabon shiri mai liki ‘FITILA’

Fim din ya kasance da Shahararrun ‘yan shirin fina-finai a #Kannywood kamar su #AliNuhu, #RahamaSadau, #AishaTsamiya dadai sauransu.

Ka sha kallo a kasa;

https://www.youtube.com/watch?v=sFHeE_5zPsM

Kannywood: Kalli ranar da za a fara yada Fina-Finan Hausa a shafin NorthFlix

Naija News Hausa ta samu tabbaci da sanar da cewa za a fara haska sabbin Fina-Finan Hausa a shafin Northflix.

Ka tuna da cewa akwai shafin da ake cewa Netflix, inda ake haska sabbin fina-finai da basu shiga kasuwa ba tukuna. Gannin hakan ne Shahararrun Tsarafa Fim tare da hadin kan masu fita shirin fim a layin Kannywood, sun hada kai da fitar da sabon tsari inda za a yita nuna sabbin Fim ga masoya a dukan duniya.

Bisa ga sanarwan da aka bayar akan Northflix, za a fara yada fina-finai ne a shafin daga ranar 8 ga watan Yuni ta shekarar 2019.

Wannan shine karo na farko da yin hakan a gidan Cinema.

Kalli sakon a kasa;

https://twitter.com/northflixng/status/1135045899057598464/photo/1

An kara bayyana da cewa za a fara haska Fina-Finan ne a Gidan Cinema a garuruwa Hudu a rana daya a kasar.

Kalli Tsari da Jihohi Hudu da za a fara haska wa a Najeriya;

KARANTA WANNAN KUMA; Maza ku yi Hatara! Kalli yadda Mata ke Rudar da Maza da Kwalliyan Zamani

Sabon Fim: Rigiman Gida [Shafi 1 da 2)

Ga sabuwa ta fito, Ka sha kallo a wannan sabon shirin fim na Hausa mai liki ‘Rigiman Gida’

A fim din, zaka ga irin matsalolin da rashin fahimta da ke aukuwa a gidaje da dama a yau, musanman akan rashin hakuri, jimiri, tsoro, ban girma, da dai sauran su.

Ka Sha Kallo;

KARANTA WANNAN KUMA; Gwamnan Zamfara ya bada Naira Miliyan N83m don sayan Shanayan Sallar Eid El-Fitr

Kannywood: Salisu Mu’azu da wasu mutane biyu sun samu Yanci daga ‘yan Mahara

Shahararran Mai Hadin Fim a Kannywood, Salisu Muazu, tare da wasu mutane biyu sun samu yancin ransu daga hannun ‘yan hari da makami bayan rana biyu da aka sace su a babban hanyar da ta bi Kaduna zuwa Jos, a ranar Alhamis da ta gabata.

Naija News Hausa ta fahimta da hakan ne bisa bayanin da dan uwan Salisu, Alhaji Sani Muazu ya bayar ga kungiyar manema labaran Najeriya (NAN) a ranar Lahadin da ta wuce a birnin Kano, cewa lallai Mahara da Bindigar sun saki dan uwansa Salisu Mu’azu.

Sani ya bayyana da cewa ‘yan harin sun saki su ukun ne bayan da suka biya kudin yanci na naira Miliyan Goma (N10m), kamar yadda aka bukace su da biya.

“Mun biya su Miliyan Goma, suka kuma tura mu a wani wuri daban da inda ‘yan uwanmu suke. A yayin da muke cikin rudu, wani direban babban mota da ya biyo hanyar da ya kuma gana da su ya gwada mana inda suke, muka kuma gana da su” inji Sani.

Bisa bayanin manema labarai, an bayyana cewa an sace Salisu ne da sauran mutane biyun a yayin da suke kan dawo wa a Jos daga wata taro da suka tafi a Jihar Kaduna, anan ne Mahara da Bindiga suka tare su, suka kuma sace mutum uku daga cikin su.

Ko da shike su hudu ne ke a cikin motar kamin aka tare su, amma shi Sani ya samu tserewa da barin kanin sa Salisu da sauran mutane biyun.

Sani da Salisu dan uwansa shahararru ne a shafin hadin fim a Kannywood tun da dadewa.

KARANTA WANNAN KUMA; Kalli yada wani ya biya wa kansa kudin makarantan Babban Jami’a har ya kamala da Turin Baro.

Kannywood: An gabatar da Takardan Sulhu Tsakanin Naburaska da Hadiza Gabon

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa Babban kotun majistare ta Jihar Kano ta bada umarnin kame ‘yar shirin fim a Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon.

Kotun ta bada umarnin gaugawa ne ga kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano, Mohammed Wakili da kame Hadiza akan zargin cewa ta kaurace wa kirar da kotun tayi gareta.

An gabatar a yau a shafin yanar gizon Twitter na Kannywood da Takardan sulhu tsakanin Mustapha Naburaska da Hadiza Gabon.

Kalli sanarwan a kasa;

Ni Ba ‘Yar Kano Bace, Saboda Haka Ba Ku Da Iko A Kaina – Sadau Ta Gayawa Kannywood.

Jaruma Rahama Sadau ta bayyana da cewa shugabancin kungiyar masu shirya fina-finan Hausa a Kano wace aka fi sani da Kannywood, cewa basu da ikon daukan matakan hukunci a kanta, don ita ba ‘yar Kano ba ce.

Wannan zancen ya fito ne a wata sanarwa da shugaban kungiyar masu shirya fina-finai ta Arewa reshen jihar Kano, Jamilu Ahmed Yakasai ya bayar a wajen bikin rantsar da sababbin shugabannin kungiyar reshen jihar Kano, wanda ya gudana a ranar Lahadi, 15 ga watan Disamba 2019.

A bayan hakan ne aka gano wasu hotuna da faifan bidiyo da ke yawo a kafafen sada zumunta na Facebook da Instagram, inda jarumar ke cikin wani yanayi da shiga marar kyan gani na rashin da’a, tana ta taka rawa, inda wani sassa na jikinta musamman ta kafarta duk a waje yake.

Shugaban ya ce kungiyar na fuskantar matsala game da daukar mataki kan jarumar, Rahama Sadau. A yanayin da ya bayyana da mara kyan gani da kuma abin kyama wacce yake zargin jarumar ta yi akan ikirarin cewa ita fa ba ‘yar Kano bace saboda haka ba su da iko akanta.

Sai dai ya ce kungiyar za ta ci gaba da sa ido kan jarumar domin gano gaskiyar ikirarin da ta yi.

“Matukar muka gano cewa tana karkashin ikon mu ba zamu bata lokaci ba wajen daukar matakin ladaftarwa akanta. Ba zamu saurara mata ba, Ina tabbatar muku matukar ta yi kokarin shirya film a yankin da muke iko wato nan jihar Kano,” inji Yakasai.

“Amma a yanzu bamu da iko saboda bazan iya yin hukunci a wata jiha ba saboda suma da nasu shugaban cin” Inji Shi.