Kannywood: Kotun Majistare ta bada Umarnin kame Hadiza Gabon

Babban kotun majistare ta Jihar Kano ta bada umarnin kame ‘yar shirin fim a Kannywood, Hadiza Aliyu Gabon.

Ka tuna cewa Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Shahararriyar ‘yar shirin fim a Kannywood, Amina Amal ta wallafa kara ga Kotu Koli ta Jihar Kano, a kan fadan ta da Hadiza Aliyu Gabon.

Amal ta gabatar da cewa Hadiza ta ci mutuncin ta da kuma muzurta ta, a hakan ne ta wallafa kara da bukatar Kotun Koli ta Jihar Kano da tsananta da kuma sa Hadiza ta roke ta da kuma biyar ta kudi kimanin naira Miliyan Hamsin (N50m) hade da manyan shaidu biyu a gaban kotun.

Naija News Hausa ta samu fahimtar cewa Kotun Koli ta bada umarnin gaugawa ne ga kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kano, Mohammed Wakili da kame Hadiza.

Kotun ta gabatar da hakan ne don kauracewar da Hadiza ta yi ga kirar da Kotu ta yi a gareta. An bayyana da cewa Kotun ta gayyaci Hadiza Gabon a baya da halarta a gaban kotun don bayani bisa wata zargi da Mustapha Badamasi Naburaska ya gabatar ga kotun.

https://www.instagram.com/p/Bv7QwzahlDo/?utm_source=ig_embed

https://www.instagram.com/p/BuZ7zJ5gBeD/?utm_source=ig_embed

Babban alkalin kotun, Muntari Dandago ya bada umarnin kame Hadiza ne a ranar Alhamis, 16 ga watan Mayu.

Alkalin ya kuma bukaci ‘yan sanda da kara kadamar da bincike don samun tabbacin ko gaskiya ne zargin da aka yi ga Hadiza.

KARANTA WANNAN; Takaitaccen Labarin Umar M. Sharif, Shahararren Mawaki a Kannywood

Kannywood: Takaitaccen Labarin Umar M. Sharif, Shahararren Mawaki

Umar Muhammadu Sharif yana daya daga cikin Shahararrun mawaƙan hausa masu mahimmancin kwarari da gaske.

Sharif ba Mawaki ne kawai ba, Dan kasuwanci a fagen wasa, yana kuma da kyautannai lambar yabo mai yawa da ya karba a fagen shiri.

An haifi Sharif ne a shekarar 1987, ya kuma yi karatun Makarantar Firamare da Sakandiri ne a garin su, Rigasa ta Jihar Kaduna.

Umar ya bayyana da cewa shi ya kasance ne dalibi mai mahimmanci kuma tun lokacin yarantakarsa, abin da ya sa shi cikin raira waƙa shi ne wani abin da ya faru tsakanin shi da ƙaunarsa na farko, kamar yadda ya fada wa BBCHausa.

“A da ni dalibi ne na kwaran gaske, kuma tun a baya lokacin da nake makarantar sakandiri, ni Musulmi ne na gaske.”

YADDA M. SHARIF YA SHIGA FAGEN WAKA

Umar M. Sharif ya bayyana a wata ganawa da manema labaran BBC Hausa da cewa lallai ya shiga fagen Waka ne sakamakon wata abun da ya gudana tsakanin shi da yarinyar da yake soyayya da ita a da.

Ya Bayyana a haka;

A wata ranar haka a lokacin da nake dan matashi na, akwai wata kyakyawar yarinya da nake so kwarai da gaske a kauyan mu, amma don rashin kwarewa na da soyayya da kuma zamancewar fadawa ga soyayya a karo ta farko, kunya ya cika ni kwarai da gaske har na kasa bayyana a gaban ta in gabatar da so na.

Bayan da na gayawa abokan arziki, sai suka shawarce ni da isa har ga kofar gidan su da kuma kiran ta, ni ko sai na kokarta da yin hakan.

Amma abin takaici, duk lokacin da na aika da kiranta, idan na ji motsin ta da fitowa sai in labe ina leken ta daga nesa don tsoron fuskantar ta ido-da-ido. Ita kuma idan ta fito, sai ta juya hagu da dama, idan kuma bata gan mai kiran ta ba sai ta koma cikin gida, a lokacin ni kuma ina boye da leken ta, Na yi hakan ne har kusan sau Uku.

A rana guda kwaram sai na kudurta cewa ba zani kara boyewa ba idan ta fito. Na kakkabe takalma na sai na hari gidan su, Ina isa a gaban gidan sai na aika mata, amma abin takaici a gareni, yarinyar taki fitowa a ranar.

Wannan ya zafeni kwarai da gaske, da bari na da mammakin dalilin da ya sa ta ki fitowa. Ganin hakan sai na kafa baki ga wakewake don lafar da zafin zuciya na, na kuma kama hanyar gidan mu. 

A duk lokacin da na tuna da al’amarin, sai in kafa baki ga wakewake. Na ci gaba da yin hakan har sai da wani Yaya na da ke zaman Mawaki ya ji ni. 

Da kuma ya gane da zakin murya na da kwarewa na, sai ya dinga bani shawarwari akan yadda zan kara kwarewa ga wakewake. Bayan ‘yan lokatai kuma, sai ya tallafa mani ga yin rikodi na ta farko a lokacin.

Wannan ita ce bayanin M. Sharif a ganawar shi da manema labaran BBC a kwanakin baya.

KARANTA WANNAN KUMA; Ba ni aka wa Duka ba, Bata mani suna kawai ake kokarin yi – Inji Bilkisi Shema

A halin yanzu, bisa ganewar Naija News Hausa, Umar M Sharif na da rikodin wakoki kimanin 500 da ya rigaya buga. A cikin hakan aka samu su; Duniya Ce, Nadiya, Madubi, Jinin jikina, Mai atamfa, Bakandamiya, Babbar yarinya da dai sauran su.

Sharif na da kwarewa kuma a shafin fita shirin fim, zaman Furoduza a fagen Kannywood, Ya kuma fito ga Fina-Finai kamar su; Mahaifiyata, Nas, Jinin jikina, Ba zan barki ba, ka so a so ka, dadai sauran su.

Ba ni aka wa Duka ba, Bata mani suna kawai ake kokarin yi – Inji Bilkisi Shema

Daya daga cikin Kyakyawan ‘yan Matan Kannywood, Bilkisu Shema ta fito da yin bayani game da wata bidiyon da ya mamaye ko ta ina a layin yanar gizo, wanda ke dauke da wata da ake zargin cewa Shema ce.

Naija News Hausa ta gane da cewa a cikin bidyon, an nino inda wani ke Dukan wata yarinya da ake zancen cewa ai Bilkisu Shema ce. Shararrar ‘yar shirin fim din, Shema ta gabatar da yin watsi da wannan, tace “wannan bidiyon ba ni bace ke a ciki, kawai mahassada ne suke kokarin bata mani suna.” inji Shema.

Kalli bayanin Bilkisu Shema a YouTube din Kannywood;

KALLA: SABON FIM DAGA KANNYWOOD | “JINI SARAUTA” 

https://www.youtube.com/watch?v=7zv9HX6QRWk

Rawa ta dauki sabon Sallo! An daura Auren Adam A. Zango da Softy

Mun sanar a baya a Naija News Hausa da cewa an daga ranar Auren Shahararre da Jarumi a Kannywood, Adam A. Zango.

Ko da shike ba a bayyana dalilin da ya sa aka daga auren ba, amma dai ba a samu daura auren ba kamar yadda aka so a baya.

A yau Naija News ta gano da bidiyo da ya bada tabbacin cewa lallai an daura Auren Adam da Softy ‘yan kwanaki da suka gabata.

Kaiya! Aure da dadi, kaga yadda Jarumin ke walwashi da Murmushi da sanin cewa lallai makiya sun sha kunya.

Kalli bidiyon a kasa kamar yadda aka rabar a layin nishadarwa ta Youtube da Kannywood ke amfani da ita.

https://www.youtube.com/watch?v=LQM8hS17uTM&feature=youtu.be

____________________________________________________________________________________________________________________________

Kalli Wannan sabon shiri mai liki ‘CIWON SO’ Shafi na 1 da shafi na 2

Kannywood: Muna da kudurin Fita takaran zabe nan gaba – inji Ali Nuhu

Daya daga cikin ‘yan shirin fina-finai a Kannywood, Kwararre da Fitacce, Jarumi Ali Nuhu ya rattaba baki ga zancen hidimar takaran zabe a kasar Najeriya.

Naija News Hausa ta samu wannan rahoton ne bisa wata ganawa da Jarumin yayi na tattaunawa da gidan labaran BBC.

“Wasu jaruman fina-finan Hausa na da kudurin fita da tsayawa takaran zabe a kasar Najeriya nan gaba.” inji Ali.

Wannan itace bayanin Ali Nuhu a ganawar shi da manema labaran BBC a wata zaman tattaunawa ta musamman da suka yi da shi.

Jarumin ya ci gaba da bayyana da cewa a halin yanzun ma, fita takara da daya daga cikin gurin ‘yan shirin fina-finai a kannywood. “A gaba ma yanzu, yana daga cikin irin kudurin da muke da shi, na ganin cewa wasu daga cikinmu sun fito a 2023 don tsayawa ga takara,”

“Ai jarumai irinsu Abba El-Mustapha da Nura Hussaini duk sun taba tsayawa takara a zabukan Najeriya” inji Ali Nuhu.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Rikici ta barke tsakanin ‘yan shirin Fina-fina a kannywood akan wata kudi da ‘yan siyasa suka bayar a garesu.

Da aka yi tugumar Ali Nuhu da tambaya, shi cikin raha ko wata rana za a ga fasta dauke da hoton Ali Nuhu yana takaran shugaban kasar Najeriya? kawai jarumin sai ya kyalkyale da dariya da cewa, “Ah haba! Gaba daya?”

An kara bukatar shi da bayyana sunayen wadanda ke da muradin fita zabe a Kannywood, sai ya ce “Lallai ba zan iya fadar sunayen su ba a halin yanzu, dalili kuwa itace, ana kan tattaunawa da shiri akan hakan”.

Kannywood: Ana wata ga Wata, Rikici ya barke tsakanin Naburaska da Hadiza Gabon

Mun ruwaito a Naija News Hausa a shafin Nishadarwa da cewa Amina Amal tayi karar Hadiza Gabon da bukatar ta da biyan kudi naira Miliyan Biyar da kuna rokonta da shaidun cewa ba zata kara ba.

Sai gashi kuma a yau mun gano da rahoton cewa sabuwar rikice ya tashi tsakanin Gabon da Naburaska.

Kalli bidiyon sanarwan a kasa kamar yadda aka rabar a layin nishadarwa ta Kannywood.

Karanta wannan kuma: Mai Martaba, Sarki Muhammad Sanusi II, Sarkin Kano ya nada wani dan Chana a matsayin wakilin ‘yan Chana da ke a Jihar.

Kash! An yanka ta tashi, An daga ranar Auren Adam A. Zango da Softy

Adam A. Zango, Shahararren dan shirin fim a Kannywood ya gabatar da daga ranar Auren sa bisa wasu dalilai.

Naija News Hausa ta gane bisa wata sanarwa da cewa ya kama ayi hidimar Auren Adam ne a wannan karshen Makon, amma sai abin ta kasance ‘An yanka ta tashi’.

Adam da kansa ya wallafa wata sabuwar sakon sanarwa ga dukan masoya da cewa lallai an daga ranar Auren na sa da Softy har sai zuwa bayan Sallah.

“Salam ‘Yan Uwa da Abokannan Arziki. An daga Aure na zuwa bayan Salla. Zan sanar maku da sabon lokacin da aka tsayar” inji Adam a cikin sakon sa.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Adam A. Zango ya nemi Sulhu da Ali Nuhu

Kannywood na cikin Rudu: Amina Amal tayi karar Hadiza Gabon a Kotu da bukatan Miliyan N50m

Naija News Hausa ta gano da wata rahoto da cewa Shahararriyar ‘yar shirin fim na Hausa, Amina Amal ta wallafa kara ga Kotu Koli ta Jihar Kano, a kan fadan ta da Hadiza Aliyu Gabon.

Mun ruwaito a baya da cewa Shahararrun Manya daga cikin ‘yan fim na Kannywood biyu sun shiga kafar wando guda. Watau Ali Nuhu da Adam A. Zango.

Ko da shike mun sanar kuma da baya da yadda aka shirya Shahararun, musanman wata bidiyon da ke dauke da Adam A. Zango inda ya nuno kansa da neman sulhu da Ali Nuhu. Ko da shike bai gabatar da sunan Ali Nuhu ba amma kalaman sa a cikin bidiyon ya bayyana hakan.

Yace “Lokaci yayi da ya kamata a yafe wa juna. Wanda aka yi wa laifi ya yafe, wanda kuma yayi wa wani laifi ya nemi gafartawa” inji Adam.

Shararrar ginbiya da kuma Haifafar kasar Kamarun, da aka sani a baya a matsayin kawar Hadiza Gabon, Amal ta gabatar da cewa Hadiza ta ci mutuncin ta da kuma muzurta ta, a hakan ne ta wallafa kara da bukatar Kotun Koli ta Jihar Kano da  tsananta da kuma sa Hadiza ta roke ta da kuma biyar ta kudi kimanin naira Miliyan Hamsin (N50m) hade da manyan shaidu biyu a gaban kotun.

Kalli karar a kasa;

Kalli Bidiyon Karar a nan; 

Kannywood: Wanda yayi laifi ya kamata a yafe masa – Adam A. Zango ya roki Ali Nuhu

Mun Ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa mun gano da wata takardan karan Kotu da Ali Nuhu ya gabatar a kotun kara game da fadan sa da Adam A. Zango

Ko da shike ba mu iya gane ainihin dalilin fadan su ba, amma bisa ga bayanin da ke cikin takardan Kotun, an bayyana ne da cewa Adam A. Zango na kokarin bata wa Ali Nuhu suna ne.

A yau kuma mun gano da sabuwar bidiyo inda Shahararan dan shirin fim din, Adam ya shirya wata bidiyo da ya gabatar da cewa lallai lokaci yayi da za a gafarta wa juna.

A cikin bidiyon, An bayan da Adam yayi sallama, ya yi Ikirarin kansa a matsayin Sabon Shugaban tsare-tsare na kasa a shekara ta 2020.

Ya kuma ci gaba da cewa “Lallai lokaci ya kusanto da Watan Ramadan, ya kamata kuma duk wandan yayi laifi ya nemi gafara, wanda kuma aka yi wa laifi ya gafarta”

Kalli sakon Adam a kasa kamar yadda ya bayar a cikin bidiyon;

Kalli yadda aka shirya su a cikin wata bidiyo;

 

Ga sabuwa a Kannywood: Ali Nuhu yayi karar Adam A. Zango a Kotu

Shahararrun Manya daga cikin ‘yan fim na Kannywood biyu sun shiga kafar wando guda

Naija News Hausa ta gano da wata bidiyon da ya bayyana da cewa Ali Nuhu da Adam A. Zango na fada da junar su.

Mun sanar a baya da cewa Hadiza Gabon tayi fada da Amina Awal a fagen shirin fim. An bayyana da cewa tayi fada da jayayya da Kyakyawa da kuma Shahararar ‘yar shirin fim, Nafisa Abdullahi a kwanakin baya a fagen shirin fim.

Ali da Adam abokai ne a da a fagen shiri. amma mun gane kwanakin baya da cewa wata abu ta shiga tsakanin su, har ga rabuwa da magana da juna.

Ko da shike an bayyana da cewa Adam ya gabatar da cewa fadan ya kare, amma abin mamaki sai gashi an gano wata takardan Kotu da Ali Nuhu ya wallafa na zargin cewa Adam A. Zango na bada masa suna.

Kalli bidiyon a kasa;

https://www.youtube.com/watch?v=XcKcAa5lGtQ&feature=youtu.be

Karanta wannan kuma: Karanta Takaitaccen Labarin rayuwar Sani Danja