Kannywood: Hadiza Gabon ta sake fada da wata a fagen Kannywood

Naija News Hausa ta gano wata sabuwar rahoto da cewa daya daga cikin Shahararun ‘yan shirin wasa fim a Kannywood, Hadiza Gabon tayi fada da wata a Kannywood.

Ko da shike ba a gabatar da sanadiyar fadan ba, amma mun samu gane da cewa ba wannan ne farkon Hadiza da yin fada ba a Kannywood. An bayyana da cewa tayi fada da jayayya da Kyakyawa da kuma Shahararar ‘yar shirin fim, Nafisa Abdullahi a kwanakin baya a fagen shirin fim.

Mun gano da wannan labarin ne a gidan yada labarai tamu a wata sakon da kamfanin ‘Kannywood Empire’ ta aika a layin nishadarwa ta Twitter na su, inda suka nemi ra’ayin mutane akan halin Hadiza Gabon.

Kalli sakon a kasa;

Kalli ra’ayi da bayanin mutane game da halin Gabon;

https://twitter.com/Mohamed71723719/status/1115938896376995841

https://twitter.com/hafizdrahmed/status/1115934807966593024

Kannywood: Karanta Takaitaccen Labarin Sani Danja

Ga Takaitaccen labarin Shahararran dan shirin wasan fim na Kannywood, Sani Danja

Sani Danja, kamar yadda aka fi sanin sa da suna, daya ne daga cikin shaharrarun ‘yan shirin fim ba Kannywood da ake ji da su.

Ainihin sunansa Danja ita ce; Sani Musa Abdullahi, ko kuma Sani Musa Danja.

An haifi Sani Danja ne a ranar 20 ga watan Afrilu ta shekarar 1973 a nan garin Fagge, ta Jihar Kano, a kasar Najeriya. Bincike ya bayyana da cewa Sani Musa Abdullahi ya samu likin Danja ne a lokacin da yake karami, dalilin suna kuwa itace irin halin da Sani ke da shi na rashin ji a lokacin. Kawai abokanan wasa suka laka masa sunan ‘Danja’ wanda a yau ko ina ka kira Sani Danja an riga an gane ko da wa kake.

Alhaji Musa Abdullahi, Baban Sani Danja na da diya bakwai ne. Maza biyar da Mata biyu. Sunan Maman Danja kuma ita ce, Hajiya Risikat.

Sani Danja kuma na da Aure da Mansura Isah tun shekarar 2007.

Karanta wannan kuma: Ba na son Auren mai Kudi – inji Jaruma Jamila Nagudu

Tarihin Karatun Sani Danja

Sani Danja ya fara karatun sa na farko ne a Makarantar Firamare da ake ce da ita `Yan Sanda Special Primary School, anan Jihar Kano daga shekarar 1979 zuwa shekarar 1980, bai karshe karatun Firamaren sa a nan ba sai da ya kara gaba zuwa ‘Kano Capital Primary School’, inda ya fara daga farko kuma daga shekarar 1980 zuwa 1985.

Bayan hakan, Danja ya shiga karatun Sakandiri ta farko a ‘Government Junior Secondary School Kawaji’ inda yayi karatun sa na shekaru ukku, daga shekarar 1985 zuwa 1989, kamin dada ya kara gaba zuwa Babban Makarantar Sakandari ta Rumfa, ya kuma kamala shekarar sa ukku anan, daga shekarar 1989 zuwa 1991.

Danja yayi karaun sa ta Jami’ar farko ne a Makarantar Jami’a ta Kano inda ya karbi takardan karutun sa ta NCE a nan ‘FCE Kano’ a shekarar 2004.

Sani Danja ya fara tashen rawa da raye-raye ne tun yana dan shekara 12. Abokansa da ‘yan anguwa kuma kan yaba masa kwarai da gaske tun lokacin, saboda irin murya da kuma taken rawa da yake da ita.

Danja na daya daga cikin wata kungiyar rawa da ake ce da ita YKK a lokacin, kamin dada a baya suka rabu akan wata dalili. daga nan kuma Danja ya shiga shirin nasa waka shi kadai. Wakan sa ta farko a lokacin ita ce `Yaki-taho-yaki’.

Shirin Fim

Sani Danja ya shiga shirin fim na Hausa ne a shekarar 1999. Ya kuma samu fita a shirin sa na farko da aka sanya wa liki `Students’, a Hausance ‘Dalibai’. 

Daga wannan shirin sai Danja ya zama jigo a kamfanin shirin fim na Hausa, ya kuma fito daga fim kamar `Adon kishiya’ a shekarar 2000, `Kwarya tabi Kwarya’ dadai sauran su.

Ga Shirye-Shirye da Sani Danja ya samu fita a Kannywood;

  • ‘Yan Uwa
  • ‘Yar Agadez
  • A Cuci Maza
  • Adali
  • Albashi (The Salary)
  • Nijeriya Da Nijar
  • Sa’ah
  • Sabon Shafi
  • Sai Na Dawo
  • Sameeha
  • Sani Nake So
  • Shelah
  • So Sanadi
  • The Other Side
  • Ango Da Amarya
  • Ban Ga Masoyi Ba
  • Bani Adam
  • Binta Suga
  • Fitattu
  • Gani Gaka
  • Gabar Cikin Gida
  • Gambiza
  • Garin Dadi
  • Gurnani
  • Gwanaye
  • Ijaabaah
  • Kukan Zaki (the Lion’s Cry)
  • Makauniya
  • Matakin Aure
  • Mijina Sani
  • Na’imatu
  • Nageria
  • Ummi
  • Wata Shariar
  • Wata Tafi Wata
  • Ya Humaira
  • Yammaci
  • Zazzabi
  • Buri Uku A Duniya (My Three Wish in the world), Da dai Sauran su.

Kalli yadda masoyan Ali Nuhu suka taya shi murnan ranar haifuwa

Mun ruwaito a baya a nan Naija News Hausa da cewa Ali Nuhu, shahararren dan shirin wasan fim na Hausa ya kai ga karin shekaru.

Bayan sakonnai ta gaisuwar fatan alkhairi, kalli yadda abokannan shirin Kannywood, masoya da Iyali suka taya Ali Nuhu murna da hada bikin nishadi don murna.

Kalli Hotuna da Bidiyo a kasa;

Kalli bidiyo a kasa;

Kannywood: Barka da Ranar Haifuwar, Ali Nuhu

Shahararran dan shirin fim na Kannywood, Ambassador Ali Nuhu, ya kai ga kara hawar shekaru.

Naija News Hausa ta gane da cewa Ali Nuhu ya daya daga cikin manyan shahararrun ‘yan shirin wasan fim na Hausa a kasar Najeriya. Ba a Kannywood kawai ba amma har ma ga Nollywood.

Naija News Hausa a Yau ta taya Ambassada na @GloNG, Jigon Kannywood murna da kai ga ganin ranar haifuwa cikin kuzari da isasshan lafiyar jiki. Alla ya kara hikima da tsawon shekaru.

Kalli yadda masoya ke ta aika ta su gaisuwar a shafin twitter;

Kannywood: Kalli yada Adam A. Zango ya hada casu don zaben Jihar Kano

Muna da sani a Naija News Hausa da cewa hukumar INEC da ke jagorancin zaben Jihar Kano ta bayar da cewa basu kai ga aminta da zaben Jihar ba tukunna. Saboda hakan ba a sanar da wanda ya lashe tseren takaran kujerar gwamnan Jihar ba.

Amma sai ga shi mun gano wata bidiyo kamar yadda muka samu a shafin twitter na Kannywood, inda Adam A. Zango, sharararren dan shirin wasan fim na kannywood tare da mabiyan sa ke ta casu akan sakamakon zaben Jihar Kano.

Kalli bidiyon a kasa;

https://www.youtube.com/watch?v=qbHzyUfQ3pw&feature=youtu.be

Kannywood: Takaitaccen Tarihin Rahama Sadau

Wannan shine takaitaccen Labarin Shararriyar ‘yar shirin fim na Kannywood, Rahama Sadau

A yau 6 ga Watan Maris, shekara ta 2019, Naija News Hausa na murnan gabatar maku da taikaitaccen bayani game da rayuwar Rahama Ibrahim Sadau. Daya daga cikin shahararrun ‘yan wasan kwaikwayon Hausa da aka fi sani da Kannywood.

Labarin Haifuwa:

An haifi Rahama Ibrahim Sadau ne a ranar 7 ga watan Disamba, a shekarar 1993 kamar yadda ‘Wikipedia’ ta bayar. Ta kuma yi zaman rayuwarta ne da iyayen a Jihar Kaduna tun daga haifuwa.

Labarin Karatun Rahama Sadau:

Rahama Sadau tayi karatun jami’a na farko ne a Makarantan Fasaha ta Jihar Kaduna da aka fi sani da (Kaduna Polytechnic), inda ta karanta ‘Business Administration’ a matsayin kwas na ta.

Sadau, ta kara da karatun ta na karanta kwas din ‘Human Resource Management‘ a wata babban Makarantar Jami’ar Eastern Mediterranean University in Northern Cyprus a shashin bincike akan sana’a da tattalin arziki.

Shigar Rahama Sadau a shirin Fim:

A wata sanarwa, Rahama ta bayyana da cewa ta shiga ra’ayin shirin fim ne tun lokacin da take karamar yarinya, watau tun lokacin da ta ke makarantar Firamare har zuwa Sakandari.

“Shirin Fim ya shiga rayuwa na ne tun lokacin da ni ke karamar yarinya. Na yi shigar ajin rawa a karama, amma kullum ina da hangen nesa da ganin cewa wata rana zan zama babba fiye da hakan” inji ta.

Kannywood:

Rahama Ibrahim Sadau ta samu shigar shirin fim na Kannywood ne a shekara ta 2013, bayan da ta hadu da kwararren dan shiri, darakta da ambasada, Ali Nuhu. Haduwar Rahama da Ali Nuhu ya sa tauraron ta ya haska kwarai dagaske, musanman bayan da ta fito cikin shirin fim na farko da taken Gani Ga Wane.

Rahama Sadau ta fito daga cikin shiri kamar;

Da Kai Zan Gana, Mai Farin Jini, Sabuwar Sangaya, Sirrin Da Ke Raina, So Aljannar Duniya, Suma Mata Ne, Farin Dare,
Gani Ga Wane, Aljannar Duniya, Adam, Ba Tabbas, MTV Shuga Naija 2017, Rariya, Rumana, Sons of the Caliphate 2016, The Other Side 2016, Jinin Jiki Na, Hujja, Garbati, Kaddara Ko Fansa, Kisan Gilla, Mati da Lado, da sauran su.

Kyautannai:

Rahama,  a cikin dan kanancin lokacin da ta shiga shiri da kannywood; ta sami kyautuna da daman da ya kara haska ta.

Rahama na da Kyautunai kamar; Fitacciyar ‘yar wasa a City People Awards – 2014, Bidbits – 2014, Arewa Films Awards hade da Afro Hollywood Awards a shekara ta 2015, Fitacciyar ‘yar wasan Afrika – 2015, Fuskar Kannywood – 2016, da dai sauran su.

 

Kalla: Bello Mohammed Bello ya hada wa shugaba Buhari wata bidiyo

Kalli wannan bidiyo da aka tsarafa wa shugaba Muhammadu Buhari don nuna masa goyon baya ga zaben 2019.

Mun ruwaito a baya da cewa mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osibanjo, ya shawarci ‘yan Najeriya da su sake zaben shugaba Muhammadu Buhari ga zaben 2019 don samar da ayuka kyakyawan ayuka a kasar kamar yadda ya ke yi.

“Shugaba Muhammadu Buhari zai samar da aiki da daman idan har an sake zaben sa ga shugabancin kasar Najeriya” inji Osinbajo.

Kalli bidiyon, kamar yadda aka aika a yanar gizon nishadarwa ta twitter;

So kan sa mutum ya Kara Aure – Saddiq Sani Saddik

Ko da kana cikin zaman lafiya ne da iyalin ka, so kan sa ka ji marmarin kara aure.

Wannan shine fadin shahararen Jigo a Kannywood, Saddik Sani a yau.

Kalli yadda ya wallafa kalmomin a cikin wannan bidiyon;

Wata kyakyawa mai suna Halima, ta mayar da martani a kan hakan;

Karanta wannan kuma; Dakta Zainab Shinkafi, Matan Gwamnan Jihar Kebbi ta bayar da Miliyan 2 don magance ciwon Kanser