Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 12 ga Watan Fabrairun, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 13 ga Watan Fabrairun, 2019

 

1. Hukumar EFCC tayi karar Babachir Lawal, a kotu Tarayya

Hukumar Yaki da Bincike akan Tattallin Arzikin Kasa (EFCC) ta kai Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal, a gaban Kotun Babban Birnin Tarayya, Abuja akan wata zargi na makirci da kuma zamba da ya aikata.

Mun ruwaito a Naija News da cewa Hukumar EFCC ta kame Babachir Lawal ne a ranar Litinin da ta gabata.

2. Wuta ya ƙone kayan aikin zabe a ofishin INEC dake a jihar Anambra

Motocin Kwantena biyu da ke cike da kayan zaben kasa a yankin Awka, na Jihar Anambra sun kone da wuta.

Wannan lamarin ya faru ne a ranar Talata da ta gabata, a yayin da wuta ya kame ofishin hukumar INEC da ke kusa da Fillin Dokta Alex Ekwueme a nan  Awka, tare da ma’aikatan hukumar da suka guje daga ofisoshin su.

3. Shugaba Buhari ya yi barazanar binciken tsohon shugaban kasa, Obasanjo

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya yi alwashin cewa zai ribato kudi dala biliyan 16 da ake zargin gwamnatin da da sacewa a jagorancin tsohnon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo na Jam’iyyar PDP a shekarun baya.

Shugaba Buhari ya gabatar da wannan ne a yayin da yake jawabi a hidimar ralin Jam’iyyar APC a Yenagoa, babban birnin Jihar Bayelsa a yau.

“Za mu kame duk wadanda suka sace tattalin arzikin kasar Najeriya” inji Buhair.

4. Zamu dauki mataki ta musanman akan abin da ya faru a Jihar Ogun – Jam’iyyar APC

Jam’iyyar APC sun yanke shawarar cewa zasu dauki mataki ta musanman akan wadanda ke da alhakin tallafawa tashin hankali da ya auku a hidimar ralin shugaban kasa da aka yi a Jihar Ogun a ranar Litinin.

Duk da haka, jam’iyyar sun ce, duk wata mataki akan hakan zai biyo baya ne a karshen zaben tarayya.

5. Kungiyar ASUP ta Umurci mambobin kungiyar da su dakatar da yajin aiki a makarantun su

Mallaman Makarantar kimiyya na kasa, a jagorancin Hukumar Mallaman Makarantan Jami’a sun dakatar da yajin aikin da suka soma watannai da suka gabata.

Ganin hakan, Hukumar ASUP ta umarci mambobinta da su koma ga Ofishin su da aiki a gaggauce.

6. Rikici ya barke a wajen hidimar ralin Jam’iyyar PDP a Jihar Legas

Wasu ‘yan ta’adda sun tayar da farmaki tsakanin junar su a wajen ralin shugaban kasa da Jam’iyyar PDP ta yi a a ranar Talata da ta gabata a Jihar Legas.

Ko da shike ba a bada tabbacin mafarin rikicin ba, amma dai abin ya faru ne misalin 1:150 na rana, inda aka hango ‘yan tada zama tsayen suna damne da junar su.

7. Osinbajo ya mayar da kanshi matsayin makiyin Yarbawa – inji Afenifere

Kungiyar Halaka da Zamantakewa ta Yarbawa, da aka fi sani da suna ‘Afenifere’, sun bayyana da cewa Farfesa Yemi Osinbajo, mataimakin shugaban kasan Najeriya, ya sanya kanshi a matsayin makiyin kasar yarbawa. Ganin irin yada Osinbajo ya mara wa yankin Hausawa da Fulani, da barin nashi ‘yan uwa.

Kungiyar sun gabatar da zabin su ga dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ga zaben shugaban kasa ta shekarar 2019.

8. Mahaifin Rabilu Musa (Dan Ibro) ya Rasu

Alhaji Musa, Mahaifin Rabilu Musa da aka fi sani da suna ‘Dan Ibro’, ya rasu a ranar Lahadi 10 ga Watan Fabrairu da ta gabata, a misalin karfe 2:30 na rana.

Alhaji Musa ya rasu ne sanadiyar wata rashin lafiyar da ta kama shi da tsawon kwanaki. Allah ya Jikan sa, ya kuma yi masa rahama.

Ka sami cikakkun labaran kasar Najeriya a shafin Naija News Hausa

Mahaifin Rabilu Musa (Dan Ibro) ya Rasu

Allah ya jikan rai!

Alhaji Musa, Mahaifin Rabilu Musa da aka fi sani da suna ‘Dan Ibro’, ya rasu a ranar Lahadi 10 ga Watan Fabrairu da ta gabata, a misalin karfe 2:30 na rana.

Alhaji Musa ya rasu ne sanadiyar wata rashin lafiyar da ta kama shi da tsawon kwanaki. Allah ya Jikan sa, ya kuma yi masa rahama.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da tunawa da rayuwar Rabilu Musa ‘Dan Ibro’, Sai ga shi a yau kuma muna samu labarin rasuwar tsohon sa.

Allah kadai ya san ranar karshen kowa, addu’ar mu itace kowa ya kare lafiya.

Mu sami tabbacin mutuwar Alhaji Musa ne daga yanar gizon nishadarwa ta twitter da ‘yan Kannywood ke amfani da ita.

Ga sanarwar a kasa;

Wasu daga cikin masoyan Rabilu Musa ‘Dan Ibro’ sun yi juyayi da wannan, kuma sun aika sakon ta’aziya ta su.

APC/Kannywood: ‘Yan wasa Fim na Hausa sun marawa shugaba Buhari baya a Jihar Kano

Kamar yadda muka sanar a Naija News Hausa a ranar jiya da cewa shugaba Muhammadu Buhari ya sauka daga jirgin sama a Jihar Kano don kadamar da hidiman yakin neman sake zaben sa.

Rahoto ta bayar da cewa ‘yan wasan fim din sun mamaye wajen hidimar don marawa shugaba Muhammadu Buhari baya da Jam’iyyar APC ga zaben tarayya da ta gabato.

Hidimar ta samu halartar wasu kwararun yan wasan Kannywoord kamar, Ali Nuhu, Zainab Booth, Sadik Sani, Rukayya Dawayya, Baba Ari da Rabiu Daushe.

Hidimar da aka gudanar a filin wasan kwallon Sani Abacha da ke a Jihar Kano a ranar Alhamis da ta gabata don hidimar yakin neman zabe ga shugaba Muhammadu Buhari da Jam’iyyar APC gaba daya.

An kuma iya gano shahararun mawakan Kannywood kamar su Ado Gwanja, Ibrahim Yala da kuma Rarara Kahutu a wajen hidimar.

Baba Ari da Rabiu Daushe sun taka irin nasu rawar gani kuma a yayin da suka fada wa rawa a filin taron da bawa jama’ar da ke wajen dariya.

Mun ruwaito a Naija News Hausa da cewa Rikici ya barke tsakanin ‘yan shirin Fim na Kannywood, a yayin da Ummi Ibrahim (ZeeZee) da Zaharaddeen Sani suka yi barazanar kai karar junan su akan kudi da Jam’iyyar PDP ta ba su a wata ganuwa da suka yi a Jihar Kaduna, a jagorancin Sanata Bukola Saraki.

Karanta kuma: Ban damu ba ko da na fadi ga zabe na gaba – inji El-Rufai, Gwamnan Jihar Kaduna

Kannywood: Anyi Wuf da Kudin da Sanata Saraki ya bayar – Ummi Zee Zee

Naija News Hausa ta ruwaito da cewa dan takaran shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar kwanakin baya ya fada wa ‘yan shirin fim da cewa idan har aka nuna masa so, kuma aka zabe shi a matsayin shugaban kasar Najeriya ga zaben shekara 2019 da ke gaba, zai tabbatar da ganin cewa bai manta da bangaren nishadi ba a Najeriya .

Atiku yayi nuni ga matsaloli da ake samu a bangaren nishadantarwa, kuma yace zai magance su. Wasu daga cikin matsalolin da Atiku ya ambato na kamar haka;

  • Matsalar samun isassun kudade wajen gudanar da aikace aikacen shiri
  • Satar fasahar ‘yan shiri
  • Sayar da ayyukansu ba tare da izinini ba
  • Rashin sanin hanyoyin watsa shirye-shirye a kasuwannin duniya
  • Da kuma rashin samun tallafi da sassaucin kudin wajen biyan haraji.

A yau mun sami sani a Naija News Hausa da cewa Ummi Ibrahim da aka fi sani da ‘Zee-Zee’ ta zargin wadansu sanannu da kwararrun ‘yan shirin fim a Kannywood da cewa sun yi wuf da Miliyoyin kudi da Sanata Bukola Saraki ya bayar garesu don rabawa masu shirin fim na Kannywood.

Mun sami tabbacin wannan ne a yanar gizon nishadi ta twitter da Kannywood Empire ke amfani da ita.

Sanarwan na kamar haka: 

Kalla bidiyo a kasa inda aka bayyana yadda aka yi da kudaden:

Kannywood: A Yau Mun tuna da Marigayi Rabilu Musa ‘Dan Ibro’

Yau a Naija News Hausa muna tunawa da shahararen dan wasan fim na Kannywood, marigayi Rabilu Musa da aka fi sani da suna ‘Dan Ibro’.

Yau Shekaru Hudu da Wata Daya da ‘yan kwanaki da ‘Dan Ibro’ ya rabu da wannan duniyar, Allah ya jikan rai.

Rabilu Musa na daya daga cikin ‘yan wasan fim na kannywood da ba za a taba manta da gurbin su ba. Mutum ne da ake ji da shi, kuma mutun ne mai bada dariya kuwa. Mutuwar ‘Dan Ibro’ ya bawa mutane da yawa mamaki da kuma tausayi, har ma wasu sun ce ko mafarki suke yi da jin labarin mutuwarsa, amma ga shi a yau abin ya kai har shekara hudu da kwanaki.

Takaitacen Rayuwar Rabilu Musa ‘Dan Ibro’

  • An haifi Rabilu Musa ne a ranar 12 ga Watan Disamba, Shekara ta 1971 kamar yadda tarihi ta bayar.
  • Rabilu Musa kuwa ya mutu ne a ranar 9 ga Watan Disamba, shekara ta 2014 a Jihar Kano

Maimacin da aka haifa a Jihar Kano ya yi rayuwar shekaru 41 a duniya kamin Allah ya sa ya kai ga hutawa.

Karatun ‘Dan Ibro’

  • Dan Ibro ya yi karatun Firamari ne a Danlasan Primary School da ke a Wudil, Jihar Kano
  • Ya kara gaba da karutunsa a makarantar Government Teachers College a nan Wudil.
  • Rabilu Musa ya shiga aikin Jami’an Kula da Kurkuku (NPS) a shekara ta 1991 ya kuma bar hukumar bayan ‘yan lokatai kadan ya koma wa shirin fim da wasan kwaikwayo na ban dariya.

Shirin Fim. 

Bayan da Rabilu Musa ya janye ga aiki da Jami”an tsaron Kurkuku a shekara ta 1991, ‘Dan Ibro ya fada wa shirin fim. Wasan farko da ‘Dan Ibro yayi itace; ‘Yar Mai Ganye’ wannan shirin ya daukaka Rabilu Musa da gaske har sunan shi ya bi ko ta ina.

Ya kuma fito cikin wasannai kamar; Andamali, Bita Zai Zai, Ibro Aloko, Ibro Angon Hajiya da sauran su dai.

Waka;

Bayan fita shirin fim da jagoran wasannai, ‘Dan Ibro na da baiwar waka kuma. Sau da yawa a fim ya kan watsa muryan sa ga waka, ko ga shirin da aka bukace shi da hakan ko kuma nasa shirin.

Rabilu Musa yayi wakoki kamara: Bayanin Naira, Idi Wanzami, Dureba Makaho, da sauran su dai.

Muna isar da gaisuwar mu ga Iyalan Rabilu Musa da ‘yan uwan sa duka don hakkuri da abin da Allah kawai ya isa yi. kuma muna mai cewa “Harwa yau muna ji da Rabilu, ko da shike bai saura da rai ba”. 

“Allah ya sa ya huta Lafiya” Amin.

Naija News Hausa

Kalla: Kadan daga cikin Shirin da ‘Dan Ibro’ ya fito ciki kamin rabuwarsa da mu

Ku sami karin cikakkun labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa

Kannywood: Ba na son Auren mai Kudi – inji Jaruma Jamila Nagudu

A fadin Jarumar, “Ba na son Auren mai kudi ko kadan, kuma kazalika ba na son auren talaka”

Jamila Umar Nagudu, shaharariyar ‘yar wasan fim na Kannywood ta bayyana wannan ne a wata zaman ganawa da ta yi da gidan telebijin ‘Kannyflix Programme’ a wajen shirin su na ‘Mujallar Tauraruwa’ 

An haifi Jamila ne a ranar 10 ga Watan Agusta, ko da shike babu tabbacin shekarar da aka haife ta, amma Jamila ta kasance jaruma ce da kuma masoyanta ke murna da ita sosai ga irin kwarewanta a fagen wasan kwaikwayo.

Ganin Jarumar ta isa ta yi aure, kuma kamar yadda ta ke da kyan ganin, za ka iya ransuwa da cewa wata mai girman kai ce ko kuma watakila macce ce mai son kudi sosai.

Amma abin mamaki shine Jamila ta ce “Ba na son auren mai kudi, kuma kazala ba na iya auren talaka, saboda shi mai kudi ba zai ba ni kulawa ta gaske ba ganin irin yada zai yita tafiye-tafiye da fita iri-iri, kuma ba zai iya zuba ma ni soyayya iri da na ke so ba. lokaci zai zama masa kadan wajen kulawa da ni” in ji Jamila.

“Ina son ne in auri mutum wanda zai nuna mani kulawa ta gaske kuma wanda zai biya bukata ta, kuma ya bani lokacin sa” in ji ta.

Jin hakan zaka iya bayyana irin macce da Jamila Nagudu ta ke.

A baya, shekara da ta wuce Jamila a bayanin ta da gidan labaran BBC ta ce “Ibada ne da Shirin fim ne abu mafi muhimanci a waje na” in ji ta.

 

Kara samun labarai akan nishadi a Naija News Hausa

Kalla kuma: Sabon Shiri na Shekarar 2019: “Mubarak” Shafi na daya da shafi nabiyu

 

Kannywood: Fatima Alihu Nuhu na murnar ranar haifuwanta

Shahararen dan wasan fim na Kannywood/Nollywood, Akta Ali Nuhu na taya diyar shi na farko murnan kai ganin ranan haifuwarta.

Shahararen, da ake kira da shi ‘Sarki Ali’ wajen fagen shirin fim ya aika sakon gaisuwa da nuna farin cikin sa na ganin cewa diyar ta kai ga kara shekara daya da haifuwa.

Fatima Ali Nuhu itace diyar Ali Nuhu na farko sai Ahmed, sunan mamar tasu kuma Maimuna.

Fatima kyakyawar yarinya ce kuma da hali na dacewa.

Uban na ta kuma kwararre ne a fagen shirin ko hadin fim, kuma sanan ne ne har ma ga shirin fim na Nollywood. Ali Nuhu ya fito cikin shirin fim da dama fiye da fim 200 tun shigar sa a shirin fim na Hausa a shekarar 1999.

Dibi hoton kyakyawar diyar na sa Fatima Ali Nuhu

Fatima Ali Nuhu
Sakon Nafisa Abdullahi zuwa ga – Fatima: A turance: Happiest Birthday to you Beautiful @fatimaalinuhu You’re so Special and not everyone will understand it✨🥰 Shine on Love and keep being happy,not only on your day but always

Ali Nuhu, Matarsa da Diyansa Fatima da Ahmad

 

Sami Karin labarai daga Naija News Hausa

Kannywood: Takaitaccen labarin Ummi Ibrahim Zee Zee

Takaitaccen labarin shararriyar ‘yar wasan film na Kannywood da kuma mawaka mai suna Ummi Ibrahim da aka fi sani da wata sunan shiri watau ‘Zee Zee’.

An haifi Ummi ne a Jihar Borno a shekara ta 1989. Tsohon ta Ba’Fullace ne, uwar kuwa ‘yar Arab ce.

Ummi ta bayyana shahararun ‘yan wasa da ta ke ji d su da kuma take koyi da su sosai wajen shiri.

“Wadanda na ke ji da su kuma na ke koyi da su a filin wasan Kannywood sune kamar haka; Marigayi’a Aisha Dan-Kano da Marigayi Rabilu Musa Dan-Ibro. muna ba wa juna girma sosai da gaske, Allah ya gafarta masu” in ji ta a wata ganawa da ta yi da manema labaran (Information Nigeria) shekara da ta gabata.

Tana da kyautannai da dama da ta samu wajen shiri, musanman a wata shiri da ta yi mai suna ‘Jinsi’ a inda ta sami sunan ‘Zee-Zee’, daga cikin wasan ne aka sami mai suna Fati Washa wadda ta jagoranci shirin na ‘Jinsi’. 

Naija News ta ruwaito Dan takarar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ce ba zai manta da yan Shirin Fim, Mawaka da Yan Nanaye ba

A halin yanzun, Ummi Ibrahim ba ta saura da shirin fim ba a Kannywood amma shaharariyar ‘yar wasan da kuma mawakar ta samu fita daga shirin fim da dama a Kannywood haka kuma ta na da rakad din wakoki da tayi da dama kamin ta bar Kannywood. Ma soyan ta na yaba mata kwarai da gaske ganin irin hikima da ke gareta a lokacin da take shirin fim.

Kyakkyawar na da kudi sosai kuma har ila yau ba ta da aure. Ta ce “Ina duban nufin Allah ya cika ga me da yin aure na” a ganawan ta da manema labarai shekara da ta gabata.

 

Karanta kuma: Jaruma Nafisa Abdullahi ta bayyana matsayin Ali Nuhu a wurin ta

Kalla; Ruwan Dare Shafi na Daya da na Biyu

 

Sabuwa: Jaruma Nafisa Abdullahi ta bayyana matsayin Ali Nuhu a wurin ta

Daya daga cikin fitattun fuskoki a masana’antar shirya fina-finan Hausa da aka fi sani da Kannywood watau mai Nafisa Abdullahi ta bada karin haske game da matsayin Ali Nuhu a wajenta musamman ma dai a harkokin masana’antar.

Jarumar ta kara da cewa ta fito a fina-finai da dama da ta kiyasta da ‘sama da 50’, ta shaida wa majiyar BBC a lokacin da ta zanta da ita kai tsaye a dandalin sadarwar zamani na Facebook cewa, fitattcen jarumin Kannywood Ali Nuhu ya wuce matsayin aboki a wajenta.

Karanta Kuma: Ba zan Manta da Yan Fim, Mawaka da Yana Nanaye ba – Alhaji Abubakar Atiku

“Yadda zan zauna na yi magana da sauran jarumai, ba zan iya yi da Ali Nuhu ba,” in ji Nafisa.

Ta ce Ali Nuhu ne sanadiyar zuwanta a Kannywwod.

Nafisa Abdullahi dake zaman daya daga cikin jaruman da ke da farin jini sosai a fina-finan Kannywood ta kuma bayyana yadda ta soma shiga harkar fim bayan ta hadu da jarumi Ali Nuhu a shekarun baya a jihar Bauchi.

Naija News ta ruwaito Takaitaccen Bayani game da Fati Washa