Zaben2019: Atiku zai ci Nasara da Buhari a Kotu – PDP

Jam’iyyar PDP a ranar Litinin, 20 ga Mayu, sun sake buga gaba da bada gaskiya da cewa dan takarar shugaban kasa na shekarar 2019 a Jam’iyyar PDP, Atiku Abubabar zai ci nasara ga karar shugabanci kasar Najeriya da ake a Kotun Zabe.

Jam’iyyar adawan sun yi kira ga kwamitin karar da tabbatar da cewa an gudanar da karar a yadda ta dace da kuma adalci.

Naija News Hausa ta fahimta a bayanin Kakakin yada yawun Jam’iyyar PDP na Tarayya, Mista Kola Ologbondiyan cewa Shugaban kasar, Buhari ya kasa a sassa uku da kasar ke begen shi da ita tun daga shekarar 2015.

A cikin jawabinsa, PDP ta kara da cewa Jam’iyyar APC ta ci gaba da raunana shugabannin PDP da kuma gabatar da zarge-zarge kan dan takarar su, Alhaji Atiku Abubakar, don jan hankalinsu daga karar da ke gaban Kotu.

“Al’ummar Najeriya sun gane da cewa zamantakewar su a kasar shekarun baya da PDP ke shugabanci yafi dacewa da ta shugabancin Jam’iyyar APC da ake ciki yanzu. Ganin hakan ne muka tunawa al’ummar kasar da hakan, da kuma yin alkawarin tabbatar da cin nasara da halin Talauci, Rashin Tsaro, Cin Hanci da Rashawa da Ta’addanci a kasar” inji Kola.

“Muna da tabbataciyar shaidodi da ya bayyana dan takaran mu da nasara ga zaben shugaban kasa ta shekarar 2019″

A hakan ne Jam’iyyar PDP suka bukaci Alkali Zainab Bulkachuwa da janyewa daga zancen karar don dangantakar ta da shugaba Muhammadu Buhari da kuma Jam’iyyar APC.

Tafiyar Buhari zuwa Turai ba tare da barin Osinbajo ya maye gurbin sa, ba daidai bane – PDP

Jam’iyyar Dimokradiyya (PDP) na kalubalantar shugaba Muhammadu Buhari da yin tafiya zuwa kasar Turai ba tare da bada daman ci gaba da shugabanci ga mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo ba.

Naija News Hausa ta ruwaito a wata labarai a baya da cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya kai ziyarar kai tsaye a kasar Turai, inda aka bayyana da cewa shugaban ba zai dawo kasar Najeriya ba sai har zuwa ranar 5 ga watan Mayu ta 2019.

Ko da shike ba a bayyana dalilin tafiyar shugaban ba, amma an gabatar da cewa ziyarar na kai tsaye ne kuma zai dauki tsawon kwanaki goma kamin ya dawo.

Ko da shike dai bisa jita-jitan mutane, Naija News Hausa na tsanmanin cewa wata kila shugaban ya ziyarci kasar Turai ne don binciken lafiyar jikin sa.

Amma abin kula shine da cewa shugaba Muhammadu Buhari bai bada dama ga mataimakin sa Farfesa Osinbajo ba, kamar yadda ya saba, kuma kamar yadda doka ta bayar.

“Matakin da shugaba Muhammadu Buhari ya dauka na rashin bada gurbin sa ga mataimakin sa a yayin da baya a kasar Najeriya, ba daidai bane. Dokar kasa ta bukaci shugaba ya bada dama ga mataimakin sa da daukan matakai a yayin da shugaba zai fita kasar, amma rashin yin hakan ga shugaba Buhari ya nuna da cewa da shi da Jam’iyyar APC basu damu da bin dokar kasa ba, kuma basu da ra’ayin al’ummar kasar a zuciyar su” inji bayanin Mista Kola Ologbondiyan, kakakin yada yawun Jam’iyyar PDP na Tarayya.

KARANTA WANNAN KUMA: Ba da gangan na ki bayyana ga Ziyarar Buhari ba a Legas – inji Tinubu

Jam’iyyar Adawa, PDP sun bayyana da cewa irin wannan tafiya na shugaba Muhammadu Buhari da bai da wata kwakwarar dalili ko manufa ba daidai bane, musanman irin hali da yanayin da ake ciki a kasar a wannan lokacin.

“Bai dace ba ga shugaba Buhari da yin watsi da lamarin kasar Najeriya ba da shiga tafiya mara dalili, musanman a halin matsalar tsaro da mawuyacin yanayi da ake a ciki a kasar. Wannan ya bayyana irin yanayin da kasar Najeriya zata kasance nan gaba idan har aka bada dama ga Buhari da Gwamnatin sa da ci gaba da mulkin kasar.” inji PDP.

Ko da shike a yayin da Jam’iyyar PDP ke gabatar da zargin ziyarar Buhari a UK ba tare da mayar da gurbin sa ga mataimakin sa ba, an rufe bakin su da fadin cewa ai ba Buhari kawai ba, har ma tsohin shugabannan kasar da suka yi mulki a baya sun yi hakan, musanman daga jam’iyyar PDP.

An gabatar da cewa tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo da Marigayi Umar Yar’Adua da suka yi shugabancin kasar Najeriya a karkashin Jam’iyyar PDP a baya sun yi hakan. Sun fita daga kasar Najeriya zuwa wata kasa ba tare da bada dama ga mataimakan su da ci gaba da mulki ba kamin su dawo.

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Talata, 30 ga Watan Afrilu, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Talata, 30 ga Watan Afrilu, 2019

1. Zaben 2019: PDP na zargin Hukumar INEC da musanya sakamakon zaben 2019 da ke a Kwanfutan su

Jam’iyyar PDP ta Tarayya na gabatar da sabon zargi ga Hukumar Gudanar da Hidimar Zaben kasar Najeriya. PDP na fadin cewa INEC ta musanya sakamakon zaben da ke a kwanfutocin su a kowace jihar kasar.

PDP sun gabatar da zargin ne a wata gabatarwa da kakakin yada yawun Jam’iyyar, Mista Kola Ologbondiyan, yayi a ranar Litini da ta gabata.

2. Manyan Jam’iyyar APC sun dage da cewa Yahaya Bello bai dace da komawa shugabancin Jihar Kogi ba

Masu ruwa da tsaki ta Jihar Kogi daga Jam’iyyar shugabancin kasa (APC), sun dage da gayawa shugaba Muhammadu Buhari da cewa kada a bayar da dama ga Gwamnan Jihar Kogi, Yahaya Bello, da komawa kujerar Gwamnan Jihar. ta karo biyu.

A bayanin ‘yan Jam’iyyar APC na Jihar, sun bayyana da cewa Gwamna Bello ya karbi kudi kimanin naira biliyan (N344billion) tsakanin watannai 38 da yayi jagoranci, amma ba wata abin nuni ga yadda Bello yayi amfani da kudaden ga ci gaban Jihar.

3. Hukumar NIS ta fara bayar da sabon Fasfot na Tafiye-Tafiyen kasa ga ‘yan Najeriya

Hukumar Sabis na Shiga da Fita na Najeriya, NIS sun fara bada sabon katin fasfot mai amfanin tsawon shekara goma da aka gabatar a baya ga ‘yan Najeriya.

Naija News Hausa ta gane da wannan ne a wata gabatarwa da  shugaban hukumar NIS, Mista Muhammad Babandede ya bayar a Hedikwatan Hukumar da ke a birnin Tarayya, Abuja.

4. Gwamnan Jihar Zamfara yayi gargadin kasa akan Sanin koma bayan tattalin arziki

Abdulaziz Yari, Gwamnan Jihar Zamfara ya gabatar da sabon hange da cewa ya gane da alamun cewa kasar Najeriya zata fuskanci koma bayan tattalin arziki a shekarar 2020.

Gwamna Yari ya bayyana hakan ne a wata gabatarwa da yayi a ranar Litini da ta gabata a wata taron tattaunawa da Gwamnonin Jihohin kasar Najeriya da aka yi a birnin Abuja.

5. A karshe, Akpabio da Amaechi sun amince da hada hannu don ci gaban APC

A karshe, Jigon Jam’iyyar APC biyu daga Kudu maso Kudu ta kasar Najeriya, Rotimi Amaechi da Godswill Akpabio sun zo ga arjejeniya don tabbatar da zumunci da cigaban Jam’iyyar APC a yankin su.

Naija News Hausa ta gane da hakan ne bayan wata ganawa da Jigo biyun suka yi na amincewa da juna a birnin Abuja ranar Lahadin da ta gabata.

6. Yawar Al’ummar Najeriya ya karu da shiga kimanin mutane Miliyan 201m – inji UN

Hadaddiyar Kungiyar Tallafin Kasashe (UNFPA) sun bayyana da cewa kasar Najeriya na da kimanin yawar mutane Miliyan 201 a halin da ake ciki.

Naija News ta gane da wannan ne a wata Rahoto da ke a cikin takardan yawar Al’ummar kasa na hukumar UNFPA ta shekarar 2019.

7. Sabi da Tsohin Gwamnonin Jihohin kasar Najeriya sun gana a Abuja

Kungiyar Gwamnonin Jihohin kasar Najeriya (NGF) sun yi wata ganawa da kadamarwa a birnin Tarayya, Abuja.

Naija News Hausa ta samu sanin cewa zaman da Gwamnonin suka yi a fadar shugaban kasa ya samu halartan tsohi da sabbin Gwamnonin kasar.

8. APC da Shugabancin kasa na kokarin kauracewa dokar kasa ta  shekarar 1999 –  inji PDP

Jam’iyyar Dimokradiyya, PDP na zargin Jam’iyyar APC da Shugabancin kasar Najeriya da kokarin kaurace wa dokar kasar Najeriya da aka bayar a shekarar 1999 da ta gabata.

A wata bayani da kakakin yada yawun PDP, Kola Ologbondiyan, ya bayar ranar Litini da ta wuce, ya ce “Tafiyar shugaba Muhammadu Buhari na tsawon kwanaki goma a London ba tare da bayar da dama ga mataimakin shi da ci gaba da maye gurbin sa kamar yadda doka ta bayar ba, bai dace ba” Wannan karya dokar kasa ne, inji Mista Kola.

9. Dalilin da ya sa Buhari bai bayar da gurbin sa ga Osinbajo ba – Garba Shehu

Babban mataimaki ga shugaba Muhammadu Buhari ta hanyar sadarwa, Garba Shehu, ya gabatar da cewa shugaban na iya gudanar da kadamar da shugabancin sa a ko ina a duniya.

Naija News ta gane da cewa Garba ya fadi hakan ne don mayar da martani ga zargin da Jam’iyyar PDP ke yi na cewa shugaba Buhari ya karya dokar kasa akan rashin bada daman maye gurbi ga mataimakin sa Farfesa Yemi Osinbajo.

Ka samu kari da cikakken labaran Najeriya a shafin Hausa.NaijaNews.Com

An sace kakakin jagoran hidimar siyasar shugaban kasa na Jam’iyyar PDP a Jihar Kogi

Muna ‘yan lokatai kadan da fara jefa kuri’a ga zaben shugaban kasa da gidan majalisai ta shekarar 2019, don zaban sabbin shugabannana da za su jagoranci kasar Najeriya a tsawon shekaru hudu da nan, sai gashi an sace Mista Austin Okai, kakakin hidimar zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP ta jihar Kogi.

Jam’iyyar PDP a jihar na zargin cewa ‘yan adawan su, jam’iyyar APC ne suka aiko da ‘yan ta’adda a daren ranar jumma’a da ta gabata don sace Mista Austin kamin gari ya waye.

Mista Kola Ologbondiyan, kakakin jam’iyyar PDP na tarayya, ya bukaci IGP Adamu Mohammed, shugaban jami’an tsaron ‘yan sandan kasar Najeriya da cewa ya watsar da jami’an tsaro a hanyar da ta bi Banda, Lokoja har zuwa Abuja don bincike da ganin cewa an ribato Mista Austin daga wannan harin.

“Idan ba a ribato ko kubuto da Mista Austin Okai daga hannun wadanan ‘yan ta’addan ba, abin zai tada farmaki kwarai da gaske, musanman ga matasa da daman suna jiran ta baci ne su dauki mataki da kansu” inji Kola.

Mun iya ganewa a Naija News Hausa da  cewa cikin makonnai biyu zuwa ukku da suka gabata, mun ruwaito da rahoton sace-sacen ciyamomin jam’iyya da dama a kasar, har ma akwai wadanda aka kashe daga cikin su.

Wannan abi takaici ne ganin ga zaben kasar ta gabato cikin ‘yan kalilan awowi.

Jam’iyyar PDP sun kara bayyana da cewa an sace ciyamomin kananan yankuna a Jihar Rivers, da zargin cewa sojoji ne suka aiwatar da hakan a jagorancin shugaba Muhammadu Buhari.

“Haka kuma aka kame mana shugabannan jam’iyyar a Jihar Kano, kamar dan takaran Sanata, Ahmed Haruna Bichi dan takaran Gidan Majalisar Jiha, Hon. Ahmed Garba Bichi” inji PDP.

“Mun kira ga al’ummar Najeriya da su kula da yadda shugabancin Muhammadu Buhari ke tsananta wa ‘yan kasa, musanman mambobin jam’iyyar adawa” inji su.

Karanta wannan kuma: Yan Sandan sun kame Sanata Rafiu Ibrahim a Jihar Kwara

Ka koma Daura ka huta – PDP sun gayawa Buhari

Jam’iyyar PDP sun ce wa Shugaba Muhammadu Buhari ya koma gidansa a Daura

Jam’iyyar PDP sun shawarci Buhari ya koma gidan sa a Daura yaje ya huta. sun fadi wannan ne wurin amsa wa rokon Shugaba Muhammadu Buhari inda yace  yan Najeriya su bashi lokaci kadan. sun ce ba za a ba da shugabancin kasar nan ba ga mutumin da kullum a na neman ya huta, ya kuma yi barci dakyau.

Sakataren Harkokin Jakadanci, Mista Kola Ologbondiyan, ya gaya wa wakilinmu cewa shugaban ya koma gidansa a Daura, Jihar Katsina, inda ya ce ya, ya kamata Shugaba Buhari ya je ya huta.

Ya ce, bamu da wani lokaci da zamu watsar kuma. Kasar ba za ta bada dama ga Shugaba mai barci ba. Shugaba Buhari ya rigaya ya yi iyakar kokarin sa, amma kokarin na sa ya zam da kasawa ga bukatar kasar.

“Ya fada wa ‘yan Najeriya shekaru hudu da suka wuce cewa tsufa zai raunana kuzarin sa. kuma tabbas yana karuwa da tsufa a ko yaushe. Haka kuma Shugaban ya bayyana cewa likitocinsa sun ce ma sa ya huta, ya ci abinci, kuma ya yi barci sosai.

Ganin wadanan bukatu duka, ya kamata mu gaya masa gaskiya cewa kasar bata da bukatan jagoranci ga mutumin da ke da wadanan illa a wannan hali da kasar ke ciki.

“Muna da yawancin matasa zube da ba su da wata aikin yi, ‘yan ƙasa da sojoji na rasa rayukan su kullum ga yan ta’ada, hanyoyi basu da kyau ko kadan, tattalin arziki bai daidaita ba kuma duk da haka shugaban da aka ce ya huta na rokon a kara masa lokaci. shin, a kara masa lokaci na me?” Ologbondiyan ya ce a matsayin uba, shugaban ya bukaci ya koma gida ya huta.

Naija News ta ruwaito Wakilin wakilai na wakilcin Kazaure/Geisel/Yankwashi a Jihar Jigawa, Mohammed Kazaure, ya lura cewa Buhari Tsoho ne, amma ba wanda zai Rinjaye shi a shekarar 2019