An saka ‘Yan Mata biyu Jarun wata biyu don Sanya Rigunan da ke nuna Tsirancin Jiki

Wata Kotun Shari’a II da ke a Magajin Gari, a Jihar Kaduna, ta saka wasu ‘yan Mata biyu a Jarun wata biyu akan nuna tsirancin jiki.

Naija News Hausa ta gane da rahoton cewa Kotun a ranar Talata da ta gabata ta saka Farida Taofiq, ‘yar shekara 20 da abokiyar ta Raihana Abbas, a kurkuku da zargin cewa sun fita gari kusan a tsirara da irin kayan da suka sanya a jikunan su.

Farida da Rahaina mazauna ne na shiyar Argungu ta Jihar Kaduna. Sun kuma amince da zargin da aka yi da su na fita kusan a tsirance.

“Ayi mana hankuri, ba zamu sake hakan ba.” inji ‘yan Farida da Rahaina bayan da aka kama su.

Mallam Musa Sa’ad-Goma, Alkalin Kotun ya ba su dama ga kowanen su da biyan naira dubu Ukku (N3,000) kamin a sake su, Ya kuma umarce su da komawa ga Iyalan su.

Bisa bayanin Aliyu Ibrahim, Alkalin da ya karbi karar Rahaina da Farida, ya bayyana ga manema labarai da cewa an kame ‘yan matan biyu ne tun ranar 16 ga watan Afrilu 2019 da ta gabata a hanyar Sabon Gari da kayan da ke nuna tsirancin jiki.

Da aka tambayi ‘yan Matan inda zasu sanye da irin wannan kayan, sun bayyana da cewa lallai zasu je gayar da wata kawar su ne da ta haifu.

Ka tuna mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Hukumar Jami’an Tsaron ‘Yan Sandan Jihar Jigawa sun sanar da gane wani dan Jariri da Maman tayi watsi da shi bayan haifuwa.

Bisa bayanin Jami’an tsaro, an ajiye jaririn ne a cikin wata rijiya da ba a amfani da shi, da ke a wata shiyya na karamar hukumar Kaugama.