Sarauta: ‘Yan Nadin Sarautan Jihar Kano sun sanya Lauyoyi 17 don Kalubalantar Ganduje

Masu Nadin Sarauta ta Jihar Kano sun yi kira da kalubalantar Gwamnan Jihar Kano da Majalisar Wakilan Jihar, akan matakin da suka dauka na kara kujerar sarauta hudu a Jihar Kano.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya cewa Gwamna Abdullahi Ganduje, Gwamnan Jihar Kano ya kara kujerar Sarauta hudu bisa ta da a Jihar.

‘Yan nadin Sarautan Jihar sun nemi Manyan Masu Bada Shawarwari ga Kasar Najeriya 7 hade da Lauyoyi 17 don kalubalantar Ganduje da Majalisar Wakilan Jihar akan matakin da suka dauka na rabar da Kujerar Sarauta a Kano.

Wadannan ne Sunayan Masu Nadin Sarauta da suka Kalubalanci Ganduje: Madakin Kano, Yusuf Nabahani; Makaman Kano, Sarki Ibrahim; Sarkin Dawaki Maituta, Bello Abubakar da kuma Sarkin Bai, Mukhtar Adnan.

Ga sunayan Lauyoyin da zasu kadamar da kalubalantar Gwamnan;

1- Prince Lateef Fegbemi, SAN, FCIArb,(UK)

2- AB Mahmoud, OON, SAN, FCIArb, (UK)

3- Adeniyi Akintola, SAN

4- Suraj Sa’eda, SAN

5- Hakeem O. Afolabi, SAN

6- Paul Usoro SAN

7- Nassir Abdu Dangiri, SAN

8- Maliki Kuliya Umar Esq

9- Nureini S. Jimoh Esq

10- Dr. Nasiru Aliyu Esq

11- Sagir Gezawa Esq

12- Muritala O. Abdulrasheq Esq

13- Aminu S. Gadanya Esq

14- Ismail Abdulaziz Esq

15- Rashidi Isamotu Esq

16- Oseni Sefullahi Esq

17- Ibrahim Abdullahi Esq

18- Haruna Saleh Zakariyya Esq

19- Auwal A. Dabo Esq

20- Badamasi Sulaiman Esq

21- O. O. Samuel Esq

22- Fariha Sani Abdullahi

23- Yahaya Isah Abdulrasheed, ACIArb, (UK)

24- Amira Hamisu

Kalli Tsarin Sabbin Sarakai Biyar da zasu Wakilci Kananan Hukumomin Jihar Kano

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya gabatar da kara Kujerar Sarauta Biyar (5) a Jihar Kano.

Kamar yadda muka sanar a wannan gidan labarai ta Naija News Hausa cewa Gidan Majalisar Dokokin Jihar Kano da Kwamitin Sauratan Jihar sun amince da karin kujerar Sarauta a Jihar Kano ne don ganin cewa hakan zai taimaka wajen samar da ayuka, rage jayayya, da kuma magance wasu rikice-rikicen dake tasowa a Jihar tsakanin al’umma.

Ga Yadda Aka Rabar da Kananan Hukumomin Kano

1- Kano Emirate:

Kano Emirate a karkashin jagorancin mai Martaba, Muhammadu Sanusi, Sarkin Tarayyar Kano zai wakilci kananan hukumomi Goma (10). Gasu nan a kasa;

 • Kano Municipal
 • Tarauni
 • Dala
 • Nassarawa
 • Fagge
 • Gwale
 • Kumbotso
 • Ungogo
 • Dawakin Kudu, da
 • Minjibir

2- Rano Emirates:

Mai Sarautan Rano zai yi sauratan kananan hukumomi goma shima.

 • Rano
 • Bunkure
 • Kibiya
 • Takai
 • Sumaila
 • Kura
 • Doguwa
 • Tudun Wada
 • Kiru
 • Bebeji.

3- Gaya Emirate

Mai Sarautan Gaya Emirate zai shugabanci kananan hukumomi Takwas (8)

 • Gaya
 • Ajingi
 • Albasu
 • Wudil
 • Garko
 • Warawa
 • Gezawa
 • Gabasawa

4- Karaye Emirate:

Mai Sauratan Karaye Emirate shima na da hakin jagorancin kananan hukumomi Shidda (6)

 • Karaye
 • Rogo
 • Gwarzo
 • Kabo Rimin Gado
 • Madobi
 • Garun Malam

5- Bichi Emirate:

Sarkin Bichi Emirate shima zai wakilci kananan hukumomi Tara (9)

 • Bichi
 • Bagwai
 • Shanono
 • Tsanyawa
 • Kunchi
 • Makoda
 • Danbatta
 • Dawakin Tofa
 • Tofa

Naija News Hausa na da sanin cewa Jihar Kano na da kananan hukumomi 44 a karkashin ta, an kuwa rabar da dukan su a karkashin jagorancin Sarakai Biyar hade da Mai Martaba, Muhammadu Sanusi.