Bai Yiwuwa Najeriya ta Zama kasa mai Jam’iyya Guda Kacal – CUPP

Kungiyar Hadin gwiwar Jam’iyyun siyasa ta Najeriya (CUPP) ta mayar da martani ga ikirarin da Jam’iyyun All Progressives Congress suka yi cewa Najeriya ta zama kasa mai jam’iyya daya.

Kungiyar hadin gwiwar a cikin wata sanarwa da ta saki a bakin kakakinta, Imo Ugochinyere, ta ce abin dariya ne cewa Sakataren yada labarai na jam’iyyar APC na kasa, Lanre Issa-Onilu, yana zancen cewa jam’iyyun adawa sun kare a kasar Najeriya.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Ofishin Hukumar Yaki da Cin Hanci da rashawa da kare tattalin arzikin kasa (EFCC), da ke a Yankin Jihar Sakkwato ta aiwatar da wata zagayen bincike a ofishin Hukumar gudanar da Zabe ta jihar Zamfara, inda suka ci karo da dunbun kudi miliyan N65.548.

Wannan zagayar binciken ya fito ne bayan da wani ma’aikacin hidimar zabe a jihar ya tayar da zargin cewa jami’an hukumar sun cire wani bangare na kudin tallafin da ya kamata a bayar ga malaman zabe a babban zaben da ya gabata.