2023: Kalli Yankin Da Matasan Arewa Suka Ba wa Goyon baya Ga Shugaban Kasa

Wata gamayyar kungiyoyin matasan Arewa ta yi kiran da a sauya shugabancin kasar daga arewa zuwa yankin Kudu maso Kudu kafin zaben shugaban kasa a shekarar 2023.

Hadin gwiwar, a karkashin kungiyar ‘Arewa Youths Assembly’, ta ce ba zai zama da adalci ba ga Arewa ta fito da shugaban Najeriya na gaba tare da lura cewa yankin ta mamaye matsayin fiye da sauran yankuna tun bayan da kasar ta samu ‘yancin kanta a 1960.

Saboda haka, kungiyar sun bayyana cewa sun fara neman dan takara daga Kudu maso Kudu mai shekarun haifuwa tsakanin shekara 40 zuwa 50 da zai karbi shugabanci daga Shugaba Muhammadu Buhari a 2023.

Shugaban kungiyar, Mohammed Salihu Danlam ne ya bayyana wannan matsayin kungiyar a gaban wani taron manema labarai a jiya.

Yayin da Danlam ke jawabinsa, ya bayyana cewa dan takarar “dole ne ya kasance yana da cudanya na kwarai da kasashen duniya, dole ne ya shiga cikin tsarin mulki na lokaci mai tsawo, ya kasance da kwarewar sadarwa, dole ne ya zama iya ba da fifikon tabbatar da adalci na zamantakewa da kyautatawa kan ci gaban tattalin arziki.”

“Arewa ta mamaye matsayin shugabancin kasar nan tun lokacin da ta sami ‘yancin kai, fiye da kowane yanki; lokaci ya yi da matasan Kudu maso Kudu za su fitar da shugaban kasa shekarar 2023,” in ji Danlam.

“Najeriya kasa ce da ke baya a tsakar cin gaba da alkawurai da kuma zama cikin duhun rashin adalci. Muna rayuwa da rashin tabbas. A yadda abubuwa suke a yanzu, bamu da masaniyar al’ummar da za su faru idan Arewa ta ci gaba da mulki a 2023. inji shugaban Kungiyar Matasan Arewa.

 

Wata Kungiya a Arewa Ta Bada Goyon Baya Ga Tinubu Da Ya Maye Gurbin Buhari a 2023

Jagoran jam’iyyar APC na kasa baki daya, Asiwaju Bola Tinubu ya samu goyon bayan shugabancin Najeriya a lokacin da wa’adin shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kare a shekarar 2023.

Wata kungiyar siyasa, North Eastern Youth Mobilization Congress, Kungiyar Matasan Arewa da ke Yankin Arewa Maso Gabas, ta bayyana goyon bayansu a wata sanarwa da ta fitar a karshen mako a Bauchi.

Shugaban kungiyar, Aliyu Balewa ne ya ba da sanarwar a karshen bikin rantsar da shugabannin zartarwa na kungiyar.

Balewa ya ce ya kamata shugabancin kasar ta sauya zuwa Kudu a 2023 tunda Arewa a lokacin ko ta riga tayi wa’adi biyu a jere.

Ya kara da cewa Tinubu fitaccen dan siyasa ne wanda ya ba da gudummawa sosai ga tsarin siyasar kasar, kuma ya cancanci a ba shi tikitin takarar shugaban kasa a jam’iyyar APC.

“Bisa kan adalci, ya kamata mulki ya sauya zuwa yankin kudancin kasar nan a 2023 tunda Arewa ta yi aiki wa’adi biyu a jere.” inji Balewa.

“Mun yi imanin cewa mutumin da ya fi dacewa da shugabancin kasar bayan Buhari shine jigon jam’iyyar APC na kasa, Bola Tinubu, saboda ya taka rawar gani ga nasarar Buhari a zabukan 2015 da 2019. Ya kuma ba da gudummawa sosai ga nasarar APC a cikin dukkanin ofisoshin zabe.”

Balewa ya kara da cewa “Saboda haka, ya kamata shekarar 2023 ta zama lokacin biya. Bari mu mutunta yarjejeniyar mutumin ta hanyar tallafawa Kudu don samar da shugaban kasa na gaba. Kuma Bola Tinubu shine mutumin da ya fi dacewa da wannan matsayin saboda kwarewarsa ta siyasa, cancanta, bayyanar da kishin kasa.”

Buhari: Matasan Arewa Sun Nemi Osinbajo da Ya Yaki Shugabancin Kasar Ko kuma ya yi Murabus da Matsayinsa

Kungiyar Arewa Youth Consultative Forum ta tuhumi Mataimakin Shugaban kasa, Yemi Osinbajo, da mayar da harin tsanancin da fadar shugaban kasar ke yi masa.

Babban Shugaban Kungiyar Matasan Arewa (AYCF), Yerima Shettima, a wata hira da jaridar Daily Post, ya lura cewa za a kori Osinbajo idan ya ki mayar da harin tsanantawa da wulakanci da ake masa, ko kuma ya yi murabus cikin mutunci da matsayinsa.

Shettima ya fadi hakan ne a yayin mayar da martani kan wasu sabin harin tsanantawa da kunyatarwa da mataimakin shugaban kasar ke fuskanta a fadar shugabancin kasa.

Shugana AYCF din ya nace a bayaninsa da cewa gwamnatin kasar a jagorancin Muhammadu Buhari tana tsanantawa Osinbajo, ya na kuwa mamakin abin da ya sa Mataimakin Shugaban kasar ya yi shuru game da rikicin da ke gudana da shi a Shugabancin.

“Mun gane da cewa wasu mutane a ofisoshin shugabancin kasar suna yin amfani da tsarin jagorancin ne don biyan bukatun kansu, Ko kun yarda ko kuma ku ki amincewa, akwai wani ko wasu da ke neman tabbatar da cewa an cire Mataimakin Shugaban kasa a tsarin mulkin don neman hanyarsa ta zuwa shugabancin kasar a 2023.” Inji Shettima.

“Abu daya nike bukatan ku gane a wannan gwamnatin, ko ta yaya suka ki amince da wannan zargin, tabbas akwai abin da ke gudana a boye. A daidai lokacin da suka ce Shugaban kasar da Mataimakinsa suna cikin kyakkyawan yanayi Na san wani abu da ba daidai ba na gudana, saboda ba a taba hayaki ba ba tare da wuta ba.”

“Maimakon a kori mataimakan Mataimakin Shugaban kasar, me zai hana a dubi Majalisar Dokoki ta kasa, idan da da gaske ake da son a rage kashe-kashen kudi a shugabanci a Najeriya me zai hana a nemi tsige wasu ma’aikata da ke a majalisar da basu da wata aiki na fari ko baka da suke yi, amma sai karban albashin da bai da ma’ana. Ko kuma a rage adadin yawar ‘yan majalisar, maimakon duba ofishin Mataimakin Shugaban.”

“Wasu daga cikin mu sun san cewa an zazzage fagen fama. Tabbas ana matukar raunana Osinbajo, wannan ya nuna a fili cewa ana hari da kuma neman a tsige shi ne daga tsarin mulkin. Na yi mamakin yadda bai fito ba da karfin gwiwa don neman tausayi da goyon bayan ‘yan Najeriya ya kuma bayyana zuciyarsa. Yana zaune kawai a cikin nutsuwa saboda yana son tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa shi mutumin Allah ne. Batun siyasa ba batun Allah bane, ya shafi batutuwa da yawa, tilas ne a nuna kwaraewa da iya taka rawa. Na san shi Farfesa ne na shari’a amma akwai bukatar ya fito ya fadawa ‘yan Najeriya abin da ke faruwa, idan ya ci gaba da yin shiru, kawai zai farka ne a wata safiya ya ga cewa an cire shi. “

Ka tuna a baya kamar yadda Naija News Hausa ta sanar, da cewa Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani-Kayode ya yi zargin Shugaba Muhammadu Buhari da wulakantar da Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo a hanyoyi goma.

2023: Yadda Za a Hana Wa’adin Buhari na Uku – Matasan Arewa

Shugaban kungiyar Arewa Youths Consultative Forum (AYCF), Yerima Shettima, ya yi kakkausar suka kan duk wani yunƙuri na tsawaita wa’adin Shugaba Muhammadu Buhari zuwa 2023.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta ruwaito a baya da rahoton cewa, wasu gungun jama’a sun yi kira ga Shugaba Buhari da ya tsawaita wa’adin shugabancinsa zuwa shekara hudu bayan wannan wa’adin.

Haka kazalika, lauyan kundin tsarin mulki da yaki da yancin bil adama, Femi Falana (SAN) ya zargi Shugaba Buhari da shirya makircin wa’adi na uku a 2023.

Femi Falana ya bayyana matakin da Buhari da mutanensa ke yi na kara tsawon jagorancin shugaban a kasar bayan wannan wa’adi da ake a ciki.

A wata hirar da Shettima ya yi da manema labaran kamfanin dilancin labarai ta Daily Post, ya yi gargadin cewa za a watsar da matasan Arewa don tabbatar da dakatar da wannan yunkuri da gwamnatin a yanzu ke kokarin gabatarwa na wa’adi na uku.

“duk wani yunkuri na ci gaba da mulkin Buhari, zai sha kaye ne kamar irin ta tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo,” inji Shettima.

“Muna sane da cewa wasu abubuwa na gudana a cikin wannan gwamnatin. Muna sane da cewa batun shirin wa’adi na uku na ci gaba a kasa amma gwamnati ba ta fito fili ta bayyana wannan shiri ba, ko kuma su yi rashin amincewa da zargin haka,”

“Jita-jita game da wa’adi na uku na yaduwa a ko’ina kuma zai mutu kurmus kamar shirin wa’adi na uku da Obasanjo ya nema, domin mun ƙuduri aniyar mu da kuma tabbatar da cewa batun wa’adi na uku bai ga hasken ranar ba a kasar.” inji Shettima.