Kogi: Hukumar INEC Ta Baiwa Gwamna Bello Takardar Shaidar Nasara da Jagoranci

Hukumar da ke gudanar da hidimar zaben kasa (INEC) ta bayarwa dan takarar gwamna a jam’iyyar All Progressives Congress a jihar Kogi, Yahaya Bello da abokin karawarsa Edward Onoja Takaddun shaida na Komawa kan mulki a ranar Alhamis.

Hukumar zaben a yau Alhamis ta bayar da takardar shaidar komawa kan kujerar gwamnan jihar Kogi ga Yahaya Bello, a nan dakkin bikin Farfesa Mahmoud Yakubu, a hedikwatar hukumar zaben da ke a Lokoja, babban birnin jihar.

Naija News Hausa ta ruwaito a baya da cewa Dan takarar jam’iyyar APC, Yahaya Bello ya samu yawar kuri’u 406,222 don kayar da dan takarar jam’iyyar Peoples Democratic Party, Musa Wada, wanda ya samu kuri’u 189,704.

Kwamishinan hukumar na kasa wanda ke lura da yankin Arewa ta Tsakiya, Mohammed Kudu Haruna, wanda ya gabatar da takardun shaidar ga zababben gwamnan ya ce, “Yau ne sabon wa’adi ya fara bayan kamala zaben da kuma kira zuwa ga jagoranci ga zababban gwamna da mataimakin nasa.”

Abin da Ya Dace ‘Yan Sanda Suyi da Wadanda suka Kashe Shugaban Matan PDP a Kogi

Dan takarar kujerar Gwamna a zaben Jihar Kogi, karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), Musa Wada ya yi kira ga ‘yan sandan Najeriya da su tabbatar da kamo wadanda suka kashe Acheju Abu.

Ka tuna cewa a yayin wata arangama ta jini da magoya bayan jam’iyyu suka yi ranar Litinin a Ochadamu, karamar hukumar Ofu na jihar Kogi, ya yi sanadiyar mutuwar mutane biyu.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar, DSP Willam Aya, wanda ya tabbatar da lamarin a ranar Talata, ya ce wata tsohon Kansila a karamar hukumar, Malama Salome Abu da Mista Awalu Zekeri sun mutu a rikicin.

Ofisan ya kara da cewa rikicin ya fara ne sakamakon rashin fahimta da ya afku tsakanin Zekeri na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da Mista Goodwin Simeon, memba a jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

“Don yin ramuwar gayya, wasu matasa da suka fusata a cikin Ochadamu sun tafi gidan Mista Simeon Abuh, wanda yana zaman kawu ne ga wanda ake zargin kuma suka haska wa gidan wuta. ‘Yar shekara 60, Malama Salome Abuh ta mutu ne a cikin gidan sanadiyar ƙone ta har lahira” inji Aye.

Dan takaran, Wada a lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya ga iyalan mamacin a ranar Talata ya yi kira ga ‘yan sanda Najeriya su bincika tare da kama wadanda suka kashe Abu.

KARANTA WANNAN KUMA: Yaron Shehu na Borno, Kashim Ya Nakasa Jami’in Civil Defence da Mota

Kogi: Hukumar INEC ta Gabatar da Mai Nasara Ga Zaben Jihar Kogi (Kalli Yawar Kuri’u a Kasa)

Hukumar gudanar da hidimar Zaben Kasa (INEC) a ranar Litinin, ta bayyana sakamakon karshe da kuma wanda ya yi nasara a zaben gwamna na Kogi na shekarar 2019.

Jami’in hukumar INEC da ya jagoranci hidimar zaben gwamnan da ta majalisa, Farfesa Ibrahim Umar Garba, ya bayyana sakamakon, a ranar Litinin, 18 ga Nuwamba a cibiyar tattara kuri’u da ke a Lokoja, babban birnin jihar bayan an samu sakamako daga dukkan kananan hukumomin.

Dangane da sakamakon, Gwamna Yahaya Bello na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya samu yawar kuri’u 406,222 don kayar da sauran ‘yan takara, musanman Engr. Musa Wada na Jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 189,704.

Zaben gwamnan da aka gudanar a ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba a jihar Kogi ya kumshi yawarn ‘yan takara 24 da suka fafata a zaben.

Dubi cikakken sakamako bisa ga kuri’un da aka tattara daga kananan hukumomi na manyan jam’iyyun siyasa biyu a zaben.

1. Olamaboro
APC – 16,876
PDP – 8,155

2. Idah
APC – 4,602
PDP – 13,962

3. Yagba West
APC – 7,868
PDP – 8,860

4. Ajaokuta
APC – 17,952
PDP – 5,565

5. Mopa-muro
APC- 4,953
PDP – 3,581

6. Okehi
APC – 36,954
PDP- 478

7. Yagba East
APC – 6,735
PDP – 7,546

8. Koton Karfe
APC – 14,097
PDP – 9,404

9. Kabba/Bunu
APC – 15,364
PDP – 8,084

10. Okene
APC – 112,762
PDP – 139

11. Igala Mela/Odolu
APC- 8,075
PDP – 11,195

12. Adavi
APC – 64,657
PDP – 366

13. Omala
APC- 8,473
PDP – 14,403

14. Ijumu
APC – 11,425
PDP – 7,585

15. Ogori-Magongo
APC – 3,679
PDP – 2,145

16. Bassa
APC – 8,386
PDP – 9,724

17. Ankpa
APC – 11,269
PDP – 28,108

18. Ofu
APC – 11,006
PDP – 12,264

19. Dekina
APC – 8,948
PDP – 16,575

20. Ibaji
APC – 12,682
PDP – 10,504

21. Lokoja
APC – 19,457
PDP – 11059

Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Litini, 18 ga Watan Nuwamba, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Litini, 18 ga Watan Nuwamba, 2019

1. INEC ta Dakatar Da Sanar da Sakamakon Zaben Gwamnonin Kogi

Hukumar gudanar da hidimar Zaben Kasa (INEC) a ranar Lahadi ta sanar da cewa ta dakatar da sanarwar sakamakon zaben gwamnoni na ranar 16 ga Nuwamba a jihar Kogi.

Wannan sanarwan an bayar da ita ne a bakin Babban Ofisan da Shugaban Hukumar INEC ta Jihar, wanda ke jagorancin hidimar zaben.

2. Tsoracewa A Yayin da INEC ta Fara Bayyana Sakamakon zaben Bayelsa

Hukumar gudanar da hidimar Zaben Kasa (INEC) ta fara tattara sakamakon zaben gwamnan jihar Bayelsa da aka gudanar ranar Asabar.

Naija News ta fahimci cewa an jinkirta ne da sanar da sakamakon wanda ada aka shirya da farawa a karfe 10 na safiyar ranar Lahadi a cibiyar Farfesa Mahmood Yakubu.

3. Fayose ya Kalubalanci zaben Jihar Kogi da Bayelsa

Tsohon gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, ya koka da sakamakon zaben gwamnonin jihar Kogi da na jihar Bayelsa.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta bayar da rahoton cewa duka zabukan da suka gudana a ranar Asabar sun kasance da rikice-rikice da kuma magudi.

4. Dalilin da yasa Membobin Edo na APC ke son Obaseki ya fita – Airhavbere

Wani jigo a jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a jihar Edo, Charles Airhavbere, ya ba da dalilan da suka sa membobin jam’iyyar ke son tsige Gwamna Godwin Obaseki.

A yayin da yake zartawa da manema labaran NAN a ranar Lahadi, tsohon mai neman takarar gwamna a Edo ya zargi Godwin Obaseki da kin sauraren muryar dalilai.

5. Abinda aka ga Yahaya Bello na yi yayin da INEC ke sanar da sakamakon zaben Kogi

A ranar Lahadin da ta gabata ne aka hango Gwamna Yahaya Bello na jihar Kogi a hotuna tare da mukarraban sa a Lokoja, babban birnin jihar, yayin da suke shan shayi da nishadewa.

Ka tuna kamar yadda Naija News ta sanar, ranar Asabar 16 ga watan Nuwamba ne Hukumar Zabe ta gudanar da zaben Gwamnonin jihar Kogi.

6.  Ban Amince da Sakamakon Zabe ba – Musa Wada ya Kalubalanci Hukumar INEC

Dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamna ta ranar 16 ga Nuwamba a jihar Kogi, Engr. Musa Wada, ya yi watsi da sakamakon zaben da hukumar INEC ke sanarwa.

Wada da abokin karawarsa sun bayyana da cewa akwai makirci a cikin sakamakon zaben da INEC ta riga ta sanar don taimakawa wa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da dan takarar ta, Yahaya Bello.

7. Zaben Kogi: INEC ta ayyana ma’aikata 30 da suka Bata

Hukumar gudanar da hidimar Zaben Kasa (INEC), ta bayyana jami’anta 30 da suka bace a zaben gwamnoni da aka yi a Kogi.

Kamfanin dillancin labarai na Naija News ta fahimta da cewa mutane 30 din da suka bata suna cikin malaman zabe da aka dauka don hidimar zaben zaben gwamnoni na ranar Asabar a jihar Kogi, arewa maso-tsakiyar Najeriya.

8. Kotun daukaka kara ta Soke Dan Jam’iyyar PDP a Majalisa

Kotun daukaka kara da ke zaune a Owerri ta tsige dan majalisa mai wakiltar mazabar Isiala Mbano / Onuimo / Okigwe da ke jihar Imo a majalisar wakilai, Obinna Onwubuariri.

Da yake yanke hukuncin a ranar Asabar, shugaban kwamitin, Mai shari’a R.N Pemu, ya bayyana da cewa nasarar Onwubuariri na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a watan Fabrairu ya kasance ne da sabawa dokar zaben kasa kamar yadda aka ayyana tun shekarar 2010.

Ka samu kari da Cikakken Labaran Najeriya a shafin Naija News Hausa

Kogi: Ban Amince da Sakamakon Zabe ba – Musa Wada ya Kalubalanci Hukumar INEC

Dan takarar gwamna na jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) a zaben gwamna ta ranar 16 ga Nuwamba a jihar Kogi, Engr. Musa Wada, ya yi watsi da sakamakon zaben da hukumar INEC ke sanarwa.

Wada da abokin karawarsa sun bayyana da cewa akwai makirci a cikin sakamakon zaben da INEC ta riga ta sanar don taimakawa wa Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da dan takarar ta, Yahaya Bello.

Naija News ta fahimci cewa a cikin sakamakon zaben da aka riga aka sanar, gwamna Bello na gaban sauran ‘yan takara da yawar kuri’u.

Rahoton sakamakon ya nuna da cewa Gwamna Bello yana kan gaban sauran ‘yan takara 23 da yawar ƙuri’u sama da dubu 200, 000 a cikin kananan hukumoi 15 daga kananan hukumomi 21 da ke a Jihar, kamar yadda aka sanar.

Wada wanda ya yi magana da manema labarai a Lokoja a ranar Lahadi, ya yi watsi da sakamakon, yana zargin cewa mataimakin gwamnan jihar, Cif Edward Onoja tare da hukumomin tsaro suna tafiya ba tare da izini ba kuma suna ziyartar cibiyoyin tattara kuri’u inda suke sauya sakamakon don fifita jam’iyyarsu.

“Lallai PDP zata kalubalancin wannan sakamakon a kotu.” inji Wada.

“Sakamakon ba tabbacin gaskiyar abin da ya faru ba ne a runfar zabe. Mutanen jihar sun zabi PDP amma APC ta canza sakamakon da ya gamshe su.

Sakamakon da hukumar INEC ta bayyana har zuwa yanzu sakamakon ba zamu yarda da hakan ba. An riga an canza duk sakamakon da aka samu a kowace runfar zabe kuma za mu kalubalanci wannan zaben. Ba gaskiyar abinda ya gudana aka sanar ba.”  inji shi.

“Ni ne dan takarar Jam’iyyar PDP kuma ba lallai ne in jira har sai sun kashe ni ba. Dole ne in yi kira ga jama’ar Najeriya su sani cewa APC ta yi magudi a zaben,” in ji Wada.

INEC: Sakamakon Zaben Jihar Kogi kamin INEC ta Dakatar da Kirga ranar Lahadi

Hukumar INEC ta Dakatar da Kirgan Sakamakon Zaben Jihar Kogi

Hukumar Gudanar da Hidimar Zabeb Kasa (INEC) ta Jihar Kogi a ranar Lahadi ta sanar da cewa ta dakatar da sanarwar sakamakon zaben ranar Asabar, 16 ga Nuwamba na zaben gwamna a jihar Kogi.

Wannan sanarwan an bayar da ita ne a bakin Babban Ofisan da Shugaban Hukumar INEC ta Jihar, wanda ke jagorancin hidimar zaben.

Jami’in, yayin da yake ba da dalilai game da dakatarwar da kuma jinkirtawa ya lura cewa yayi hakan ne saboda sakamakon kananan hukumomi biyu da suka saura basu rigaya sun iso dakin kirga ba.

Ko da shike dai ya sanar da cewa zasu ci gaba da kiirgan a ranar Litini, 18 ga watan Nuwamba, watau a Yau.

Naija News Hausa ta kula da cewa a daidai lokacin da aka dakatar da kirgan, Dan takara daga Jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Yahaya Bello na gaban Musa Wada, Dan takaran Peoples Democratic Party (PDP) da yawar kuri’u a tseren gwamnan Jihar Kogi.

Kamar yadda INEC ta sanar a rahotannai, Gwamna Bello na APC na da kimilar kuri’u 184,430 yayin shi Wada da PDP ke da yawar kuri’u 176,803.

INEC ta Bayyana Damuwarta kan Rikici gabadin Zaben Jihar Kogi

Hukumar gudanar da Zaben Kasa, INEC ta jihar Kogi ta nuna damuwar ta game da yiwuwar tashin hankali yayin da zaben gwamnoni na ranar 16 ga Nuwamba na gabatowa.

Naija News ta fahimci cewa Kwamishinan Zabe na mazaba (REC) a Kogi, Farfesa James Apam, a ranar Talata ya bayyana wannan ne a wurin bayyana “fita da jefa kuri’a (GOTV), Ilimin masu jefa ƙuri’a da kuma dakatar da cin zarafin mata a siyasa (STOP VAWIP)” da aka yi a Lokoja, babban birnin jihar Kogi.

Ka tuna da cewa babban dan takaran kujerar Gwamnan Jihar Kogi a karkashin Jam’iyyar Dimokradiyya (PDP), Sanata Dino Melaye ya fadi ga zaben Firamare da Jam’iyyar ta yi a kwanan baya.

Naija News Hausa ta kuma gane da cewa dan takaran ya yi barazana a baya da cewa ya fice Yahaya Bello, Gwamnan Jihar Kogi da ke kan mulki, “a kowace hanya da matsayi” inji Dino Melaye.

Ko da shike bayan da Dino ya fadi ga zaben Firamaren Jam’iyyarsa, PDP ta bashi mukamin jagoran neman takara ga abokin adawan shi ga kujerarshi gwamnan, Musa Wada, wanda ya kasance da nasara ga zaben firamare ta jam’iyyar PDP a Jihar.

KARANTA WANNAN KUMA; Wata Yarinya ta Haska wa Kanta Wuta don Saurayinta ya gaza Biyan Sadakin da aka Yanka Masa