Jami’an Tsaro sun Cafke wasu Mutane biyu a Kano da zargin Kashe ‘yan Shekara Takwas

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana da cafke wasu mutane biyu da ake zargi da hannu a sace wata yarinya mai shekaru takwas, Aisha Umar.

Hukumar tsaron sun bayyana hakan ne a wata sanarwa da Jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan jihar, DSP Abdullahi Haruna ya sanar a ranar Talata da ta gabata a Kano.

A sanarwan, Abdullahi ya bayyana da cewa “Rundunar tsaron ‘Operation Puff Adder’ ta kama wadanda ake zargi da aikata laifin, bayan sun karbi sami rahoton wasu gawawwakin wadanda aka gano a cikin wani rijiya a unguwar Gandun Albasa a cikin Kano.”

Ya ce an kwashe gawar da dauke ta zuwa Asibitin kwararru na Murtala Muhammad da ke a Kano.

Jami’in tsaraon ya kara da cewa daga baya aka gane da cewa gawar yarinyar ne, watau yar shekaru takwas da aka sace a Tudun Wada, karamar hukumar Nassarawa ta jihar.

Haruna yayi kira ga jama’a da su samar da duk wata rahoton abin da ya faru, ko suka gane da batun faruwa ko kuwa wata motsi cikin hanzari zuwa ofishin ‘yan sanda da ke kusa.

“Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Mista Ahmed Iliyasu, ya bada umarnin a ci gaba da neman kame sauran wadanda suka aiwatar da laifin kisan yarinyar, da cewa kuma za a caji su zuwa gaban kotu bayan haka” inji shi.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa diyar sanane da babban Masanin Qur’ani da karatun Islam, Sheikh Gumi, Maryam Ahmad Gumi ta mutu.