Manyan Labarai daga Jaridun Najeriya ta ranar Laraba, 20 ga Watan Maris, Shekara ta 2019

Wadannan ne Manyan Labarai ta Jaridun Najeriya a yau Laraba, 20 ga Watan Maris, 2019

1. ‘Yan Hari sun sace Malamin da ke yi wa shugaba Buhari du’a’i

Mahara da bindiga sun sace Sheikh Ahmad Sulaiman, babban Malami da kuma masoyin shugaba Muhammadu Buhari.

‘Yan harin sun sace Sheikh Ahmad ne a yayin da yake kan komawa gidan sa a Kano bayan da kamala wata hidimar wa’azi a Jihar Kebbi. ‘yan hari da makamin sun kuma bukaci biyar kudi naira Miliyan N300m kamin su sake shi.

2. Atiku da Jam’iyyar PDP sun wallafa karar Buhari ga kotu

An gabatar da takaitaccen karar da dan takaran shugaban kasa daga Jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar da jam’iyyar suka yi ga Shugaba Muhammadu Buhari da jam’iyyar APC a gaban kotun kara ranar Talata da ta gabata.

Daya daga cikin karar ya bayyana da cewa shugaba Muhammadu Buhari bai dace da fita takara ba, da zargin cewa shugaban bai da isasshen takardun takara da ake bukata da dan takaran shugaban kasa.

3. Obasanjo ya kafa baki ga zancen nasarar Buhari

Tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo ya kafa baki ga sakamakon zaben shugaban kasa da aka yi ranar 23 ga watan Fabrairu da ta gabata.

Naija News Hausa ta gane da cewa Obasanjo bai yi kala ba da zancen zaben tun ranar da aka gabatar da Muhammadu Buhari a matsayin mai nasara ga zaben.

4. Karya ne, bamu da shirin sayar da Gidan Kasuwancin Legas – inji Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin tarayya ta karyace zance da zargin da ake na cewa tana kadamar da shirin sayar da babban Gidan Kasuwancin da ke a Jihar Legas.

“Karya ce wannan jita-jita, bamu da wata shiri na sayar da gidan kasuwancin Jihar Legas” inji Gwamnatin tarayya a yayin da take mayar da martani game da zancen da ya mamaye yanar gizo da cewa gwamnatin na da shirin hakan.

5. Gwamnatin Tarayya na shirin kara kudin Haraji – Sanata Udoma

Ministan kasafin kudin kasa, Sanata Udo Udoma ya bayyana da cewa Gwamnatin Tarayya na shirin kara kudin haraji ga ‘yan kasa don samun isasshen kudi da za a iya biyar sabon tsarin albashi na ma’aikatan kasa ta naira dubu talatin N30,000.

Udoma bayyana hakan ne a ranar Talata da ta gabata a yayin da bayani ga gidan majalisa akan lamarin kudi.

6. Shugaba Buhari yayi zaman tattaunawa da Manyan shugaban Jami’an tsaron Kasa

A ranar Talata da ta gabata, Shugaba Muhammadu Buhari yayi zaman tattaunawa da Manyan shugabannan Jami’an tsaron kasar Najeriya a nan fadar sa da ke Aso Rock, Abuja.

Naija News ta gane da cewa shugaban ya soma tattaunawar ne da jami’an tsaron a fadar sa missalin karfe 11 na safiya.

7. Gidan Majalisar Dattijai sun amince da naira dubu 30,000 ga ma’aikatan kasa

Gidan Majalisa,  a ranar Talata da ta gabata sun gabatar da amince da kanancin kudin ma’aikatan kasa na naira dubu talatin da aka tayar a baya.

Mun ruwaito a Naija News Hausa a baya da cewa kungiyar ma’aikatan kasa sun bukaci gwamnatin tarayya da biyar kankanin albashi na naira dubu 30,000 ga ma’aikatan kasa.

8. Alhaji Ibrahim Chatta Umar, Sarkin Patigi ya mutu a birnin Abuja

Alhaji Chatta ya mutu ne daren ranar Talata, 19 ga watan Maris da ta gabata a garin Abuja, babban birnin Tarayyar Najeriya. Za a kuma yi hidimar zana’izar sa a yau Laraba, 20 ga watan Maris 2019 missalin karfe 2 tsakar ranar yau, kamar yadda al’adar Islam ta bayar.

“Mutuwar Chatta abin takaici ne kuma da bakin ciki a garemu, gurbin sa kuma zai zama a sake a  wannan lokacin” inji Alhaji Sulu.

 

Ka samu cikakken labaran kasar Najeriya a shafin Naija News Hausa a koyaushe